Rufewa
Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafi da muke kawo muku labaran kai-tsaye. Da fatan kun ji daɗin kasancewa da mu.
Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/12/2024
Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Muktar
Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafi da muke kawo muku labaran kai-tsaye. Da fatan kun ji daɗin kasancewa da mu.
Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.
Asalin hoton, Getty Images
Babban bankin Najeriya CBN, ya ce ba za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 1000 da 500 da 200 ba.
A wata sanarwa da babban bankin ya fitar, wanda muƙaddashin daraktan hulɗa da jama'a na bankin Sidi Ali Hakama ta fitar, bankin ya ce labarin da ake yaɗawa kan wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin ba haka ba ne, inda ta ƙara da cewa babu ranar da za a daina.
Bankin ya kuma yi kira ga jama'a su yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa daga ranar 31 ga watan Disamban 2024, za a daina amfani da tsofaffin kuɗin.
"Hukuncin da Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke a ranar 29 ga Nuwamban 2023, ta amince a ci gaba da amfani da sababbi da tsofaffin takardun kuɗaɗen naira," kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Asalin hoton, Rivers state government
Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta jingine hukuncin da wata kotun ta bayar a baya, inda ta umarci babban bankin Najeriya da babban akanta na ƙasat su daina ba jihar Rivers kasonta na tarayya.
Alƙalan kotun uku, ƙarƙashin mai shari'a Hamman Barka ne suka yanke hukuncin, inda suka ce kotun da ta yanke hukuncin na farko ba ta da hurumin sauraron ƙarar.
A watan Oktoba ne mai shari'a Abdulmalik ta babbar kotun tarayya a Abuja ta ce kason da gwamnatin jihar Rivers ke samu daga asusun tarayya tun daga watan Janairu ya saɓa dokar kundin tsarin mulkin ƙasar, kuma dole a dakatar.
Kotun ta ce gwamna Siminalayi Fubara na Rivers ya gabatar da kasafin kuɗin ne a gaban ƴanmajalisar jihar guda huɗu, wanda a cewarta yi wa doka karan-tsaye ne.
Asalin hoton, CDS
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya buƙaci sojojin Najeriya su fatattaki Lakurawa daga jihohin Sokoto da Kebbi da ke arewacin ƙasar.
Wata sanarwa ta ce babban hafsan ya bayyana haka ne a cikin saƙon da ya aike wa runduna ta musamman da ya tura domin aikin fatattakar Lakurawa mai suna "Chase Lakuwaras Out".
Da yake jawabi a madadin babban hafsan, babban kwamandan runduna ta 8 ta sojin ƙasa na Najeriya, Birgediya Janar Oluyinka Soyele, ya buƙaci sojojin su tabbatar sun kawo ƙarshen ƴan ƙungiyar.
Sai dai ya buƙaci sojojin su kiyaye rayuka da dukiyar al'umma na waɗanda babu ruwansu.
A cewarsa: "An zaɓi sojojin ne sannan aka horar da su, don haka ƴan Najeriya suna fata za su fatattaki Lakurawan nan baki ɗaya," kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya nuna.
Mr Soyele ya ce tun kafin aika sojojin na musamman, dakarun rundunar sun kutsa dazukan Sokoto da Kebbi, inda suka gwabza da ƴanbindigar, inda suka ƙwato bindigu da alburusai da dama.
Asalin hoton, Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya tafi Dubai domin wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu wajen ƙaddamar da matatar samarwa da adana albrkatun man fetur da darajarta ta kai dala miliyan 315.
Matatar mallakin kamfanin Oriental Energy Limited ce kuma ta wani attajiri ɗan Najeriya, wadda za a ƙaddamar ranar 14 ga watan Disamba.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shettima ya ce daga Dubai zai kuma tafi Saudiyya domin gudanar da ibadar Umara.
"A Saudiyya zan gana da shugaban bankin Musulunci (IsDb) domin tattaunawa hanyoyin inganta harkokin noma da wasu ayyukan bankin a Najeriya," in ji shi.
Asalin hoton, Senator Kashim Shettima/X
Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ya ce Najeriya ba za ta samu cigaban tattalin arzikin da ake buƙata ba sai an inganta ɓangaren makamashinta.
Sai ya yi kira ga shugabanni a ƙasar da su ajiye bambancin siyasa, domin yaƙi da matsalar da ɓangaren makamashin ke fuskanta.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin majalisar tattalin arzikin Najeriya kan wutar lantarki da na yaƙi da polio a fadar shugaban ƙasar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
“Lallai ba za a iya inganta tattalin arzikin ƙasar nan ba sai mun magance matsalar makashi, sannan mu tabbatar dukkan ƴan Najeriya suna samun isasshen makamashin da suke fuskanta," in ji shi.
Da yake bayyana takaicinsa kan yadda kashi 40 zuwa 70 na ƴan ƙasar suke fama da ƙarancin wutar lantarki, Shettima ya ce ganin gwamnoni da sauran waɗanda suka cikin kwamitin ya sa ya samu natsuwar za a magnce matsalar.
Asalin hoton, EPA
Ma'aikatan lafiya a Gaza sun ce aƙalla Falasɗinawa 30 ne suka rasu yayin da 50 suka jikkata a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat ranar Alhamis da dare.
Harin ya faɗa kan wani ginin gidan aikewa da wasiƙu da ake amfani da shi a matsayin matsuguni.
Mazauna yankin sun ce harin ya rutsa da iyalan wani gida mai yawa a wurin.
Wakiliyar BBC ta ce rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan shugaban ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ya jagoranci kai hare-hare kan dakarunta da kuma fararen hula a ƙasarta.
Asalin hoton, UN News
Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya amince da tsawaita takunkuman da ya ƙaƙaba wa ƙungiyar Taliban ta Afghanistan.
Takunkuman sun ƙunshi riƙe kadarori, da hana tafiye-tafiye, da haramta sayar musu da makamai.
Duka mambobin kwamatin 15 ne suka amince da matakin, wanda aka ƙaƙaba wa jami'an gwamnatin tun bayan da suka karɓe mulkin Afghanistan a watan Agustan 2021.
Asalin hoton, EPA
Kafar yaɗa labarai ta BBC ta ce za ta ci gaba da bayar da rahotonnin da suka shafi Jamhuriyar Nijar duk da matakin da hukumomin ƙasar suka ɗauka na hana ɗaukar shirye-shiryensu.
A ranar Alhamis ne hukumomin Nijar suka sanar da dakatar da tasoshin rediyo na FM a faɗin ƙasar yaɗa labaran BBC har na tsawon wata uku.
Sai dai cikin wata sanarwa da BBC ta fitar ta ce duk da cewa matakin zai shafi ƙoƙarinta na kai wa ga ɗimbin masu sauraronta, hakan ba zai rage mata karfin gwiwa ba.
''Haƙika wannan mataki zai shafi ƙoƙarimu na kai wa ga masu sauraronmu da ke cike da bukatar samun labaranmu na gaskiya waɗanda ba su nuna ɓangaranci," a cewar sanarwar daga ofishin hulɗa da jama'a na BBC.
"Muna kan ƙudirinmu na gudanar da aikin jarida bisa ƙwarewa, kuma za mu ci gaba da yaɗa labaran da suka shafi ƙasar ba tare da fargaba ko daɗaɗa wa wani ba."
Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Nwakuche Ndidi, a matsayin shugaban riƙo na hukumar kula da gidajen yarin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da sakataren ma'aikatar hukumar tsaro ta sibil difens da hukumar kashe gobara da ta shige da fice, Ja'afaru Ahmed ya ce naɗin Ndidi zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Disamba.
Naɗin nasa na zuwa ne bayan ƙarewar wa'adin shugaban hukumar na yanzu, Haliru Nababa.
A ranar 18 ga watan Fabrairu ne dai tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Nababa a muƙamin.
An haifi Nwakuche Ndidi ranar 26 ga watan Nuwamban shekarar 1966 a garin Oguta na jihar Imo.
Kafin naɗinsa kan muƙamin shi ne mataimakin shugaban hukumar mai lura da horaswa.
Asalin hoton, UNHCR
Sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya a Syria ta buƙaci Hukumar Kula da 'Ƴangudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ci gaba da ayyukanta a ƙasar.
Jakadan hukumar a ƙasar Syria, Gonzalo Vargas Llosa - ta shaida wa manema labarai cewa buƙatar tallafi a ƙasar tana da ''yawan gaske'' kamar yaddafanin dillancin labarai na AFP ya ambato shi yana bayani.
Ya ce hukumar na da ''tattaunawa'' da sabuwar gwamnatin kuma ''akwai alamun za mu aiki tare da su''.
"Sun yaba da ayyukan da muke yi a ƙasar na tsawon shekaru, kuma suna buƙatar mu ci gaba da aiki.'
Asalin hoton, Getty Images
Dubun dubatar ƴan Syria sun yi dandazo a Damascas, babban birnin ƙasar da sauran birane domin bikin murnar hamɓarrar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad, ranar da suka kira ta ''farin ciki''.
An kunna waƙoƙin neman sauyin gwmanati a dandalin Umayyad da ke babban birnin ƙasar.
Taron na kama da wata gagarumar walima, inda iyalai suka riƙa ɗaga tutocin neman sauyi, yayain da mutane ke ci gaba da tururuwa lungu da saƙo na ƙasar.
A cikin wani bidiyo da ya fitar, shugaban ƴantawayen da suka hamɓarrar da gwamnatin ƙasar ya buƙaci al'umma su fita su nuna farin cikinsu cikin kwanciyar hankali da lumana.
Asalin hoton, BBC/Lina Sinjab
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya naɗa abokinsa mai matsakaicin ra'ayi, Francois Bayrou a matsayin sabon firaministan ƙasar.
A makon da ya gabata ne ya rusa tsohuwar gwamnatin da ya zaɓa bayan wata uku.
Ƙasar Faransa na cikin ta shiga ruɗanin siyasa tun bayan zaɓen da mista Macron ya kira a farkon watan nan, wanda ya samar da majalisar dokoki da babu jam'iyyar da ke da rinjaye.
Mista Bayrou - shugaban jam'iyyar, Democratic Movement - zai fuskanci kaubale a koƙarinsa na janyo hankalin jam'iyyun da suka samu rarraubuwar kawuna a majalisar dokokin ƙasar domin shiga gwamnatin ƙasar.
Abu na farko da zai fara cin karo da shi, shi ne batun aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar.
Sheikh Tijjani Umara Gwani Muhammad malami ne da aka haifa kuma ya rayu a birnin Maiduguri na jihar Borno a arewacin Najeriya.
An haife shi a shekarar 1956, kuma ya yi karatu a makarantar Islamiyya ta Sheikh Abul Fathi da ke Maiduguri, kafin mahaifinsa ya kai shi garin Kaulaha na ƙasar Senegal inda ya yi sakandare.
Ya yi karatun kwaleji da na jami'a a birnin Tripoli na Libya, inda ya samu shaidar digiri na farko da na biyu a can.
Malamin ya faɗa wa BBC cewa ya fi ƙwarewa a fannin tafsirin Ƙur'ani da kuma Hadisi.
Asalin hoton, Yahaya Bello/Facebook
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kuɗi naira miliyan 500.
A zaman da kotun ta yi a yau Juma'a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Emeka Nwite, kotun ta buƙaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa domin samun belin.
Alƙalin ya ce dole ne mutanen da za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja, babban birnin ƙasar.
Haka kuma kotun ta ce dole ne masu tsaya masan su gabatar wakotun takardun kadarorin nasu domin tantancewa.
A baya-bayan nan ne dai hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi a gaban kotu bisa zarge-zarge 19 da suka ƙunshi almundahanar kuɗaɗe da yawansu ya kai naira biliyan 80.
Lamarin da ya sa kotun ta tura shi gidan gyaran hali, a yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar.
Sai dai Yahaya Bello ya musanta aikata ba daidai ba.
Mai shari'a Nwite ya ce dole ne tsohon gwamnan ya ajiye wa fasfo ɗinsa n tafiye-tafiye.
Haka kuma ya bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da zai cika sharuɗan beli.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai babbar kotun Abuja ta tura tsohon gwamnan gidan yarin Kuje bayan fatali da buƙatar belinsa kan zarge-zargen karkartar da sama da naira biliyan 100 a lokacin da yake gwamnan jihar da ke tsakiyar Najeriya.
Ma'aikatan lafiya a Gaza sun ce aƙalla Falasɗinawa 30 ne suka mutu tare da raunata 50 a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai sansanin 'yangudun hijira na Nuseirat ranar Alhamis da daddare.
Harin ya faɗa kan wani ginin gidan aikewa da wasiƙu da ake amfani da shi a matsayin matsuguni.
Mazauna wurin sun ce harin ya rutsa da iyalan wani gida mai yawa a wurin.
Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan wani babban jami'in ƙungiyar Islamic Jihad.
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin sojin Myanmar ta rasa iko da ilahirin kan iyakar ƙasar da Bangladesh a karon farko tun bayan ƙwace ikon ƙasar kusan shekara huɗu da suka gabata.
'Yantawaye masu ɗauke da makamai daga ƙabilar Arakan sun kori sojoji daga wuri na ƙarshe da suka fi ƙarfi a jihar Rakhine.
Sun ƙwace sansanin sojin da ke garin Maungdaw da ke kan iyakar kasashen biyu.
Ɗaruruwan sojoji ne suka miƙa wuya, yayin da aka kashe da dama.
Shugaban mulkin sojin Myanmar, Janar Min Aung Hlaing ya shafe shekara guda yana fuskantar koma-bayan soji, yayin da faɗa ke ci gaba a ƙasar.
Ko a watan Afrilu ma mayaƙan na ƙabilar karen sun ƙwace iko da garin Myawaddy da ke kan iyakarta da Thailand.
Ana dab da fara Sallar Juma'a ta farko tun bayan da 'yantawaye suka ƙwace ikon Syria.
Jagororin 'yan tawayen sun yi kiran gudanar da gagarumar zanga-zangar murnar hamɓarar da gwamnatin Assad.
Kalli hotunan wasu mutane da suka taru a wajen masallacin Umayyad a birnin Damascus.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Maryam Waziri
Tsohon ɗan ƙwallon Najeriya, Tijjani Babangida ya ce matarsa, Maryam Waziri ta rasa idonta guda ɗaya kuma an yi mata tiyatar gyaran fuska a Netherlands.
A ranar 9 ga watan Mayu ne wani mummunan hatsarin mota ya rutsa da Babangida da iyalansa ciki har da ƙaninsa da matarsa da ɗansa mai shekara ɗaya da rabi, a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.
Cikin wata hira da ya yi da tsohuwar ƙungiyarsa ta Ajax Amsterdam a Netherland, Babangida ya ce damuwar da ya shiga ba za ta taɓa gushewa ba.
Maryam Waziri - wadda tauraruwa ce a masana'atar shirya fina-finai ta Kannywood - ta auri tsohon ɗan ƙwallon ne a watan Nuwamban 2021.
Ƙaninsa Ibrahim Babangida ya mutu nan take bayan hatsarin, yayin da ƙaramin ɗansa, mai suna Fadil ya rasu kwanaki bayan hatsarin, sannan mai aikin gidansu ta samu karaya a ƙafa.
Tsohon ɗan wasan na Najeriya ya ce shi ya ji raunuka a ƙafarsa a lokacin hatsarin, don haka ne ya ƙudiri aniyar taimaka wa matar tasa inda ya tafi Netherlands domin ta samu cikakkiyar kulawa.
Ya kuma ce sakamakon yanayin da matar tasa ta shiga ta manta komai na rayuwarta.
“Bayan shafe wata uku a nan Netherlands, na faɗa mata cewa hatsarin ya rutsa da ƙaramin ɗanmu. Daga nan sai ta fara tambayata wai ya sunansa. Ba ta iya tuna komai'', in ji shi.
Babangida ya kuma yaba da irin gudunmowar da abokansa na ƙwallon ƙafa suka ba shi a ƙasar ta Netherlands.
Ya ce sun taimake shi da duk abin d ayake buƙata, kuma sun fara gangamin tara masa kuɗi domin daukar ɗawainiyar jinyar matar tasa, wadda ya ce za ta kwashe shekara guda ana yi mata aiki a asibitin.
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya - da ake yi wa laƙabi da G7 - na shirin ganawa a yau domin tattauna halin da ake ciki a Syria.
Ƙungiyar - wadda ta ƙunshi ƙasashen Amurka da Birtaniya da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da kuma Japan - ta ce a shirye take domin nuna goyon bayanta ga kafa sabuwar gwamnati da za ta kunshi kowa da kowa ba tare da nuna ɓangaranci ba.
Cikin wa ta sanarwa da ta fitar ranar Alhamis da maraice, ƙungiyar ta ce dole ne gwamnatin Syria da za a kafa ta martaba 'yancin ɗan'adam, ciki har da mata.
Haka kuma ƙungiyar ta ce dole ne sabuwar gwamnati ta kare duka al'ummar ƙasar, ciki har da kungiyoyin addinai da ƙabilu marasa rinjaye.