window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin wannan shafi na BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo karshensa.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu dawo don ci gaba da kawo muku sabbin labarin.

    Amma kafin nan, muke cewa mu kwana lafiya

  2. 'Elon Musk zai gano ɗaruruwan dalolin da aka yi almundanarsu a Amurka'

    Elon Musk

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Elon Musk - wanda ke sanya idanu kan kashe kuɗaɗen gwamnati, zai taimaka wajen gano ɗaruruwan biliyoyin da aka yi almundahansu da asararsu.

    Mista Trump dai bai bayar da wata hujja kan iƙirarin nasa na kashe kuɗaɗen ba, ya faɗa kafar yada labari ta Fox News cewa a lokacin yaƙin neman zaɓensa ya alƙawarta rage kashe kuɗaɗen gwamnati, don haka mutane na so ya cika alƙawarin.

    Shugaba Trump ya ce tuni biloniyan ya gama da hukumar USAID mai tallafa ƙasashe, kuma yanzu sai mayar da hankali a fannin ilimi da na soji.

    Mista Trump ya dage cewa babu wata riba da Elon Musk zai samu a wannan aiki, amma yana buƙatar gudanar da shi.

  3. Libya ta gano gawarwaki 28 da aka binne a wani katon kabari a ƙasar

    katon kabari

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin ƙasar Libya sun ce sun gano aƙalla gawarwaki 28 a wani ƙaton kabarin bai ɗaya a kusa da birnin Kufra da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    Rahotonni sun ce an kuɓutar da wasu ƴancirani 78 daga wata cibiyar da aka tilasta tsare su, yayin da dama suka bayar da rahoton cewa waɗanda suka yi safarasu sun muzguna musu.

    Jami'an ƙasar sun ce ana tsare da mutum uku kan lamarin - ɗan Libya guda da wasu biyu ƴan ƙasashen waje biyu.

    A makon da ya gabata ma, an gano gawarwakin wasu mutum 19 a wata gona da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Tun bayan hamɓarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a 2011, ƙasar Libya ta zama wata cibiyar da ƴancirani ke ya da zango, a bulaguron da suke yi mai cike da hatsarin tsallaka teku zuwa Turai.

  4. Babban ministan jihar Manipur a Indiya ya yi murabus

    Biren Singh

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban ministan jihar Manipur da ke arewacin Indiya, Biren Singh ya ajiye muƙaminsa gabanin kaɗa ƙuri'ar rashin gamsuwa da gwamnatinsa da majalisar dokokin jihar ke shirin yi.

    Mista Singh na fuskantar suka saboda rashin magance rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a jihar a 2023, tsakanin ƙabilar Meitei mai rinjaye da ta Kuki-Zo.

    Fiye da mutum 250 aka kashe tun bayan fara rikicin, yayin da kusan 60,000 suka rasa muhallansu.

    Wakilan ƙalibar Kuki-Zo sun ce ba su da wani fata daga babban ministan kan magance rikicin.

    Rikicin ya samo asali ne sakamakon umarnin wata kotu na faɗaɗa damarmakin tattalin arziki da ƙarin kaso mai tsoka na ayyukan gwamnati da ilimin da 'yan ƙabilar Kukis ke samu daga 'yan ƙabilar Meiteis.

  5. An tsaurara tsaro a Ecuador yayin da ake gudanar da babban zaɓen ƙasar

    jami''an tsaro

    Asalin hoton, Getty Images

    An tsaurara tsaro a Ecuador inda al'ummar ƙasar ke zaɓen sabon shugaban ƙasa da 'yan majalisar dokoki.

    An girke tarin jami'an tsaro riƙe da makamai a rumfunan zaɓe, yayin da aka yi gargaɗin samun abin da aka bayyana da ''hari kan dimokraɗiyya''.

    Shugaɓan ƙasar mai ci Daniel Noboa mai matsakaicin ra'ayi na fafatawa da Luisa Gonzales mai ra'ayin riƙau.

    Mista Noboa - wanda ya jagorancin ƙasar na tsawon wata 15 - ya fuskanci ricike-rikien masu safarar miyagun ƙwayoyi.

    Mista Gonzales mai ra'aiyin riƙau ya gudanar da yaƙin neman zaɓensa kan inganta tattalin arziki, inda ya sha sukar yadda Mista Noboa ya tafiyar da fannin makamashin ƙasar.

    Idan ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko na zaɓen ba, za a je zagaye na biyu cikin watan Afrilu.

  6. China ta kare matakin amfani da magunguna masu sauƙin kuɗi

    magunguna

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da ingancin magunguna ta China ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi cewa magunguna masu sauƙin kudi da ake kai wa asibitocin ƙasar ba sa aiki kamar na ƙasashen yamma.

    A shekarun baya-bayan nan China ta fara sayo magunguna masu sauƙin kuɗi da yawan gaske, a wani yunƙuri na karya farashin magungunan da ake shigar da su ƙasar daga ƙetare.

    To ai da kafofin ya ɗa labaran ƙasar, sun ruwait likitocin ƙasar na cewa magungunan masu sauƙin kudi ba sa aiki kamar yadda na ƙetaren ke yi.

    To sai dai hukumar kula da ingancin magunguna ta ƙasar, ta ce likitocin sun yi kuskure a bayanin nasu, tana mai bayyana abin da likitocin suka ce da ''jita-jita''.

  7. IMF ya yaba wa sauye-sauyen tattalin arzikin Ethiopia

    Abiy Ahmed

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar Asusun bayar da lamuni na duniya IMF, ta yaba wa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Ethiopia ke aiwatarwa.

    Yayin da take jawabi a wata ziyara da ta kai Addis Ababa, Kristalina Georgieva ta kira sauye-sauyen masu tsauri, amma ta ce suna tafe da ''gagarumar nasara''.

    Ms Georgieva ta ce a shekarar da ta gabata tattalin arzikin Ethiopia ya bunƙasa da fiye da abin da aka yi hasashe.

    A watan da ya gabata ne kasar ta buɗe kasuwannin hannayen jarinta, bayan da watan Yulin shekarar da ta gabata zare hannunta daga harkokin kuɗin ƙasar, wanda ke darajarsa ke zubewa.

    Tsare-tsaren Firaministan ƙasar, Abiy Ahmed na farfaɗo da tattalin arzikin kasar ya gamu da cikas sakamkon annobar korona da kuma yaƙin basarar yankin Tigray.

  8. Dakarun Isra'ila sun kashe mata biyu Falasɗinawa a Gaɓar Yamma

    Ma'aikatar Lafiyar Falasɗinawa ta ce dakarun ISra'ila sun kashe wasu mata biyu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

    Rahotonni sun ce ɗaya daga cikin matan na ɗauke da cikin wata tara.

    Mazauna yankin sun ce da farko dakarun na Isra'ila sun dakatar da bai wa matar tare da cikin nata kulawar da ak ba su a asibitin.

    Ma'aikatar lafiyar ta ce an kashe mace ta biyun, bayan da sojojin Isra'ilar suka yi amfani da abin fashewa domin shiga gidanta.

    Sojojin na ISra'ila sun ce suna faɗaɗa ayyukansu a arewacin yankin a matsayin martani kan abin da suka kira ''kawo tarnaƙi ga ayyukansu'' kuma tana bincike game da lamarin.

  9. Saudiyya ta soki Netanyahu kan furucinsa na 'gina wa Falasdinawa' ƙasa a ƙasar

    Mohammed bin Salman

    Asalin hoton, Getty Images

    Saudiyya da sauran ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya sun yi Allah wadai da kalaman Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ya nuna cewa a iya gina wa Falasɗinawa ƙasarsu a Saudiyya.

    Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin wata hira a Amurka jim kaɗan bayan ganawarsa a Shugaba Donald Trump, wanda ya bayar da shawarar abin da ya kira ''share Gaza da sauya wa Falasɗinawa matsuguni.

    Shugaban ƙungiyar ƙasashen Larabawa, Ahmed Aboul Gheit, ya ce kalaman nasa tsantar kauce wa gaskiya ce.

    Shugaban Isra'ila, Isaac Herzog ya faɗa wa BBC cewa an samu wata sabuwar mafitar.

  10. Kwankwaso ya gana da Aregbesola a Legas

    Kwankwaso da Aregbesola

    Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/X

    Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar NNPP Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida na ƙasar, Rauf Aregbesola a birnin Legos da ke kudancin ƙasar.

    Cikin wani saƙo da Kwankwason ya wallafa shafinsa na X, ya ce sun yi ganawar ne domin tattauna batutuwan da suka sfahi siyasa da makomar dimokraɗiyyar ƙasar.

    Ganawar 'yan siyasar biyu na zuwa a daidai lokacin da jam'iyyun hamayya ke ta kiraye-kiyare ga jam'iyyun hamayya su haɗa kai don tunkarar zaɓen 2027.

    A watan da ya gabatane ne jam'iyyar APC resehn jihar Osun ta sanar da korar Aregbesola - wanda tsohon gwamnan jihar ne - bisa zarginsa da laifin cin amanar jam'iyyar.

  11. An fara maido da lantark a Sri Lankan bayan ɗaukewar wutar a duka faɗin ƙasar

    Jami'ai a Sri Lankan sun ce sannu a hankali an fara maido da wutar lantarki a Colombo, babban birnin ƙasar da wasu biranen ƙasar, bayan ɗaukewar wutar da ta faru a fadin ƙasar.

    Hukumomi sun ce asibitoci da cibiyoyin tsaftace ruwan sha aka fi bai wa fifiko wajen maido da wutar.

    Hukumar samar da lantarki ta ƙasar, ta ce an samu ɗaukewar wutar ne sakamakon wata matsalar gaggawa da ta faru a wata ƙaramar tashar samar da wutar da ke birnin Colombo.

    Jami'ai sun ce zai ɗauki sa'o'i kafin kammala mayar da wutar a duka faɗin ƙasar.

  12. Ɗaruruwan Falasɗinawa na komawa arewacin Gaza bayan janyewar sojojin Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗaruruwan Falasɗinawa a kan motoci da amalanken jakuna na ci gaba da tuɗaɗa zuwa arewacin Gaza bayan da sojojin Isra'ila suka kammala ficewa daga yankin Netzarim.

    Falasɗinawan sun cika titin, wanda sojojin Isra'ila suka shimfiɗa a farkon yaƙin domin raba tsakanin arewaci da kudancin Zirin Gaza.

    Ficewar sojojin Isra'ila daga yankin, wani ɓangare ne na sharaɗin yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Gaza da aka cimma a watan da ya gabata.

    Tuni dai tawagar wakilan Isra'ila ta isa Qatar domin fara tattauna mataki na biyu na yarjejeniyar, da za ta kawo ƙarshen yaƙin baki-ɗaya da kuma sakin duka mutane da Hamas ke garkuwa da su.

  13. Za a gudanar da babban taron shirin maido da dimokradiyya a Nijar

    Wasu sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin mulkin sojin Nijar sun sanar da gudanar da babban taron kan shirin dawo da mulkin dimokraɗiyya, kusan shekara biyu bayan hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum.

    Taron na kwanaki huɗu da za a yi a cikin Fabrairun da muke ciki zai bayar da shawarwari ga shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahamane Tiani, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato.

    Hukumar da za ta shirya taron, za ta tattara tare da gabatar da rahotonta a watan Maris.

    Jamhuriyar Nijar na ɗaya daga cikin ƙasashen yankin Sahel da sojoji suka ƙwace mulki.

    Kuma ƙasar tare da Mali da Burkina Faso, sun yanke alaƙa da Faransa da Ecowas.

  14. Trump ya zanta da Putin kan yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

    Trump/Putin

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump na Amurka ya faɗa kafofin yaɗa labaran ƙasar cewa ya zanta da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin ta waya kan ƙoƙarin yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

    Mista Trump ya nuna cewa ya sha zantawa da Shugaba Putin ta wayar a baya-bayan nan.

    To sai dai gwamnatin Rasha ba ta tabbatar ko ƙaryata rahotonnin ba.

    Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Shugaba Trump zai gana da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky nan gaba cikin makonnan.

    Toshon ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya bayyana shakkunsa kan ko Amurka za ta iya kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar tattaunawa da Rasha cikin kwana 100 da Mista Trump ya sako na dakatar da yaƙin.

  15. Sojojin Isra'ila sun kammala ficewa daga yankin Netzarim a Gaza

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun Isra'ila sun kammala janyewa daga yankin Netzarim da ke Gaza, a wani ɓangare na cika sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta domin sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su.

    Sojojin Isra'ilar ne suka ne suka shimfiɗa - wanda ya raba tsakanin arewaci da kudancin Gaza - a farko-farkon yaƙin.

    Yanzu haka masu shiga tsakani a yarjejeniyar tsagaita wutar sun nufi Qatar domin ci gabata da tattauna mataki na biyu na yarjejeniyar.

    Isra'la ta ce har yanzu akwai wasu matsaloli da suka shafi matakin farko da ya kamata a tattauna, kafin a fara tattauna mataki na biyun - wanda zai kawo ƙarshen yaƙin na dindindin.

    A nata ɓangare Hamas ta zargi Isra'ila da jan ƙafa, inda ta ce tattaunawa na cikin hatsarin rugujewa.

  16. Tsohon shugaban ƙasar Namibiya, Sam Nujoma ya rasu

    Tsohon shugaban Namibia

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Namibiya na farko bayan samun 'yancin kan ƙasar, Sam Nujoma, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

    Cikin wata sanarwa da shugaban ƙasar na yanzu, Nangolo Mbumba ya fitar ya ce tsohon shugaban ƙasar mais shekara 95 ya rasu ne a wan asibiti da ke Windhoek babban birnin ƙasar.

    Nujoma ya jagoranci dogon gwagwarmayar ƙwatar 'yancin ƙasar daga Afirka ta Kudu da ta yi wa ƙasa mulkin mallaka.

    A shekarar 1990 Namibiya ta samu 'yancin kai, inda ya zama shugaban ƙasar na farko, inda kuma ya jagorancin ƙasar har zuwa 2005.

    Shugaban ƙasar na yanzu, Nangolo Mbumba ya yaba wa marigayin bisa jajircewar da ya nuna wajen ƙwatowa ƙasar ƴancinta.

    "Ya kasance uban ƙasarmu, wanda ya sadaukar da ilahirin rayuwarsa don hidimta wa al'ummarsa'', a cewar Shugaba Mbumba.

  17. Ina da hujjojina amma INEC da kotu suka yi watsi da su - Hudu Ari

    Hudu Ari

    Tsohon kwamishinan zaɓen jihar Adawama, Hudu Ari - da aka sauke a baya-bayan nan bisa zargin aikata laifukan zaɓe, ya bayyana damuwarsa kan rashin ba shi dama kan zargin da ake yi masa kafin ɗaukar cire shi daga matsayinsa.

    Yayin da yake magana da manema labarai a Bauchi, Ari ya yi iƙirarin cewa ya rubuta wasiƙu da dama ga hukumar zaɓen ƙasar, domin bayyana mata ainihin abin da ya sani kan zargin da ake yi masa, amma sai hukumar ta yi watsi da wasiƙun nasa.

    Ya ƙara da cewa kotun - da ta saurari ƙarar zaɓe tsakanin tsohuwar 'yar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam'iyyar APC, Sanata Aishatu Binani da kuma gwamnan jihar Ahmadu Fintiri - ta ƙi amincewa da shaidarsa.

    A 2023 ne lokacin da ake dakon sakamakon ƙarshe a zaɓen gwamnan jihar Adamawa, kwamishinan zaɓen jihar, Hudu Ari - wanda a doka ba shi ne da alhakin faɗin sakamakon zaɓe ba - ya bayyana 'yar takarar APC, Aishatu Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen.

    Wani lamari da ya tayar da yamutsi da tashin hankali a jihar.

    To sai dai Ari ya dage cewa yana da ƙwararan hujjojin da suka sanya shi ɗaukar matakin, amma ba a gayyace shi kotun domin gabatar da su ba.

    Ya ce korar da aka yi masa ba ta ɓata masa rai ba, kamar rashin ba shi damar kare kansa bisan zargin da ake yi masa.

    ''Aikin gwamnati wani abu ne mai cike da tsari, da dokoki da ƙa'idoji, bisa doka ya kamata a saurareni. Kuma ko Ubangiji ma ai ba zai hukunta ka ba har sai ya turo maka ɗan aike, manzanni da littattafai, kuma ka saɓa'', kamar yadda ya bayyana.

    Tsohon kwamishinan ya ce bai taɓa yin nadamar abin da ya aikata ba, saboda duk abin da yi a bisa doron gaskiya yake.

  18. Saudiyya ta buɗe rajistar aikin hajji ga mazauna ƙasar

    aikin hajji

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanar da buɗe rajistar aikin Hajji na wannan shakerar ga 'yan ƙasar da waɗanda ke zaune a ƙasar.

    Ana gudanar da rajistar ne ta hanyar wata manhaja da ake kira #Nusuk, inda mutum zai shigar da bayanan lafiya da adireshinsa da ma sauran bayanai.

    Cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za a bayar da fifiko ga waɗanda ba su taɓa gudanar da aikin hajjin ba.

    Bisa tsari dai sai mazauna ƙasar sun nemi izinin hukumomin ƙasar, ta hanyar yin rajisata, sannan sun cika sharuɗa kafin a ba su damar gudanar da aikin hajjin.

  19. Ƴan Thailand biyar da Hamas ta sako sun isa ƙasarsu

    'Yan Thailand da aka yi garkuwa da su a Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴan Thailand ɗin nan biyar da ke aikin gona a lokacin da Hamas ta yi garkuwa da su sun isa gida, kwanaki 10 bayan Hamas ta sake su.

    Ƴan uwa da abokan arziki na ta murna da koke-koke a lokacin da suka sauka a filin jirgin sama na Bangkok.

    Mutanen biyar dai na cikin ƙoshin lafiya, kuma tun da aka sake su suna asibiti a Isra'ila domin duba lafiyarsu, inda a yanzu kai tsaye za su tafi wurin iyalansu.

    A ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ne Hamas ta kama mutanen a lokacin wani hari da ta ƙaddamar cikin Israila inda suka kashe mutum 1,200 tare da garkuwa da 251.

    Ministan harkokin wajen Thailand ya gode wa dukkan waɗanda suka taka rawa domin ganin an sako mutanen, inda ya ce a baya sun fidda ran za su sake ganin mutanen.

  20. Sojojin Isra'ila sun janye daga shingen Netzarim da ke Gaza

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun sojin Isra'ila sun janye daga shingen Netzarim da ke Gaza, wani babban titin soji da ta raba Zirin Gaza biyu, ɓangaren arewaci da kudanci.

    Janyewar sojojin na daga cikin sharuɗan tsagaita wuta da ake aiki da ita a yanzu haka, inda a jiya Asabar Hamas ta saki Isra'ilawa uku, Isra'ila kuma ta saki fursunonin Falasɗinawa 183 daga gidajen yarinta.

    A wani labarin kuma yanzu haka wakilan Isra'ila a tattaunawar tsagaita wutar na kan hanyarsu ta zuwa Qatar domin ci gaba da tattauna mataki na biyu na yarjejeniyar.

    Sai dai Firaministan Isra'ilar, Benjamin Netanyahu ya nuna damuwarsa kan yadda Isra'ilawan nan uku da Hamas ta saka a jiya Asabar suka koma gida a ƙanjame cikin mummunan yanayi.

    Mista Netanyahu ya ƙara da cewa Isra'ila za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da sako sauran Isra'ilawan da ake tsare da su, da alƙawarin kawo ƙarshen ƙungiyar Hamas.

    A nata ɓangare Hamas ta zargi Isra'ila da jan ƙafa wajen barin kayan agaji su shiga Gaza, inda ta ce tattaunawar na cikn hatsarin rugujewa.