window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da muhimman batutuwa da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/05/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida, da Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Za mu sake dawowa domin kawo muku wasu sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, muke cewa mu kwana lafiya

  2. Kotun Amurka ta ɗaure wani mutum shekara 53 saboda kisan wani yaro Bafalasɗine

    Wata kotun Amurka ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin shekara 53 saboda kisan wani yaro Bafalasɗine ɗan asalin Amurka mai shekara shida tare da raunata mahaifiyarsa a watan Oktoban 2023.

    Joseph Czuba ya daba wa Wadee Alfayoumi da Hanan Shaheen wuƙa saboda ɓarkear yaƙin Gaza.

    Matar tare da ƴarta na zaman haya a gidan mutumin da ke kusa da Chicago.

    Masu shigar da ƙara sun ce Czuba ya aikata abin da ya aikata ɗin saboda ƙiyayya da musulmi.

    A watan Fabrairu ne aka same shi da laifi kisan kai da yunƙurin kisan kai da kuma laifukan ƙiyayya.

  3. LP ba za ta shiga kowace ƙawance ba a 2027 - Abure

    Julius Abure

    Asalin hoton, Julius Abure

    Jam'iyyar adawa ta LP a Najeriya ta nesanta kanta daga shiga kowace irin ƙawance dmin tunkarar zaɓen 2027.

    Kwamitin zartarwar jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ne ta tababtar da haka lokacin wani taro da ta gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar.

    A baya-bayan nan dai jam'iyyun hamayya a Najeriya na ta ƙoƙarin ƙulla wata haɗaka domin tunkarar jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

    To sai dai jam'iyyar ta LP ta ce ba za ta shiga kowace irin haɗaka.

    “Taronmu a jajjada cewa jam'iyyarmu ba ta ciki, kuma ba za ta shiga kowane irin haɗaka ba domin tunkarar zaɓen 2027, a maimakon haka jam'iyyar LP za ta mayar da hankali wajen sake gina kanta ta hanyar ɓullo da sabbin sadaru da ƙarfafa kanta domin samun nasara a zaɓen 2027'', in ji Abure.

  4. Ina son sasantawa da iyalan gidan sarautar Birtaniya - Yarima Harry

    Prince Harry

    Asalin hoton, itv News

    Yarima Harry na Birtaniya ya ce yana son sasantawa da sauran iyalan gidan sarautar ƙasar -- amma Sarki Charles ba ya son magana da shi saboda saɓanin da aka samu kan wanda zai ɗauki ɗawainiyar tsaron lafiyarsa.

    Prince Harry na zantawa da BBC bayan rashin nasara da ya yi a kotu kan adadin ƴansandan da aka tanadar masa domin ba shi kariya a lokacin da ya ziyarci Birtnaiya.

    Ya ce ya damu game da matakin, kuma bai ga ta yadda zai dawo da matarsa da ƴaƴansa zuwa ƙasarsa domin su zauna ba.

  5. Kamfanin Meta ya yi barazanar rufe shafin facebook a Najeriya

    Meta

    Asalin hoton, Getty Images

    Akwai yiwuwar masu amfani da shafukan fesbuk da na instagram a Najeriya za su ga ɗib bayan da kamfanin da ya mallaki shafukan, wato Meta ya koka kan ɗinmbin tara da gwamnati ta lafta masa wadda ya ce "ba abu ne mai yiwuwa ba".

    A bara ne hukumomin sanya ido uku na Najeriya suka lafta wa kamfanin tarar da ta kai fiye da dala miliyan 290, bisa zargin kamfanin da karya wasu dokoki.

    Sai ga shi kuma kamfanin na Meta ya yi rashin nasara a ƙarar da ya shigar a wata babbar kotu da ke Abuja, inda ya ƙalubalanci matakin.

    "Za a iya tursasa wa mai shigar da ƙara ya rufe ayyukan shafin fesbuk da instagram a Najeriya domin rage hatsarin da zai iya faɗawa ciki idan bai bi umarnin ba," kamar yadda kamfanin ya rubuta a takardun shigar da ƙara.

    Meta ne kuma kamfanin da ya mallaki manhajar WhatsApp, to amma kamfanin bai ambaci WhatsApp ɗin ba a bayanin nasa.

    Babbar kotun ta bai wa kamfanin wa'din zuwa ƙarshen watan Yuni ya biya tarar.

    BBC ta tuntuɓi kamfanin Meta kan matakin da zai ɗauka amma bai bayar da amsa ba.

    Fesbuk ne shafin da al'umma suka fi amfani da shi a Najeriya, inda miliyoyin al'ummar ƙasar ke amfani da shi a kowace rana.

  6. An janye kariya kan wasu ƴan majalisar Senegal don a bincike su kan zargin cin hanci

    Faye

    Majalisar dokokin ƙasar Senegal ya ɗage kariyar majalisar kan wasu mambobinta biyu, da ake zargi da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnati da aka ware don yaƙi da annobar Corona.

    Moustapha Diop ya kasance ministan masana'antun ƙasar, yayin da Salimata Diop ke matsayin ministar mata a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Macky Sall.

    Tuni dai ƴan majalisar suka musanta zargin da ake yi musu.

    Aƙalla ministoci shida ƙarƙashin tsohuwar gwamnatin aka zarga da cin hanci da rashawa da ya kai dala biliyan ɗaya da rabi.

    Shugaban ƙasar Bassirou Diomaye Faye da aka zaɓa a shekarar 2024 ya alƙawarta magance matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar.

  7. Kotu ta yanke wa direba hukuncin kisa a Legas

    Bus

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata babbar kotu a Legas ta samu wani direban motar bas, Andrew Ominikoron da laifi, tare da yanke masa hukuncin kisa, kan kisan wata budurwa mai shekara 22, Bamise Ayanwola.

    A zaman kotun na sama da awa biyu da rabi, mai shari'a Serifat Sonaike ta ce kotun ta tabbatar, ba tare da wani shakku ba cewa mutumin shi ne ya aikata laifin.

    Daga nan sai mai shari'ar ta furta cewa "za a rataye ka har sai ka mutu a matsayin hukunci kan kisan da ka yi wa Oluwabamise Ayanwola."

    Duk da cewa babu wani da ya shaida yadda lamarin ya faru, kotun ta dogara ne da bayani kan abubuwan da suka faru, da bayanin likita da kuma bayanan da wadda aka kashe ta yi gabanin mutuwarta.

    Kisan da aka yi wa budurwar, Bamiseye a shekarar 2022 ya fusata al'umma tare da janyo tofin Allah tsine, lamarin da ya sanya shari'ar ta ɗauki hankalin al'umma.

    Kotu ta ce direban ya yi ƙaurin suna wajen ɗiban fasinja ba bisa ƙa'ida bayan lokacin tashi aiki, inda yakan kashe wutar cikin motar, ya kulle ƙofofi sannan ya aiwatar da aika-aika.

    Kotun ta ƙara da cewa direban ya fi yi wa mata masu ƙananan shekaru irin wannan ta'asa, inda yakan ɗauke su zuwa wajen da babu wanda zai cece su, inda yakan yi musu fyaɗe.

    Yakan sadu da su ba da amincewarsu ba, in ji kotu.

  8. Ƙaryar maƙiya Najeriya ta ƙare - Tinubu

    Shugaban Najeriya Najeriya, Bola Tinubu

    Asalin hoton, Katsina State Gov.

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa sojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar.

    Yayin da yake jawabi ga sojojin ƙasar ranar Juma'a a wata ziyara da ya kai jihar Katsina - ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ƴan fashin daji, shugaban ƙasar ya ce matsalar ƴanta'adda da masu garkuwa da mutane da ƴan fashin daji ta jima a ƙasar.

    "Ƴan Najeriya sun zuba muku ido, suna jiran ku kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da ƙwato kowane yanki na ƙasarmu, ku nuna wa maƙiyan Najeriya cewa ƙaryarsu ta ƙare'', in ji Shugaba Tinubu.

    ''Gwamnati na ɗaukar matakan samar muku isassun kayan aiki, da suka haɗ da sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin tattara bayanan sirri da dabarun yaƙi, ba wai don kare ƙasarmu kaɗai ba, sai don samun ƙarfin da za ku iya murƙushe duk wata barazana a ko'ina ta ɓulla''.

    Dakarun Najeriya na yaƙi da Boko Haram tun 2009, inda suka samu nasarar karya logon ƙungiyar ta hanyar kashe manyan kwamandojinta.

    To sai dai a baya-baya nan, ƙungiyar tsagin ISWAP na nuna alamun dawowa da ayyukansu a wasu sassan ƙasar, musamman arewa maso gabashi.

    Haka kuma akwai ƙaruwar ayyukan masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a wasu sassan shiyyar arewa maso yammaci, ciki har da Katsina da yake ziyarar, inda suke kashe mutane tare da ƙona ƙauyuka da garuruwa.

  9. Bola Tinubu ya isa Katsina

    Tinubu

    Asalin hoton, KTSG

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa jihar Katsina da ke arewacin ƙasar domin ziyarar aiki.

    Gwamnan Katsina Dikko Radda, da tsohon Gwamna Bello Masari na cikin manyan mutanen da suka tarɓe shi tun daga filin jirgi.

    Jim kaɗan bayan isarsa ne kuma ya yi wa rundunar sojin ƙasar jawabi.

    Shugaban na ziyarar aiki ne ta kwana biyu, inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi.

    Tinubu

    Asalin hoton, KTSG

    Tinubu

    Asalin hoton, KSTG

  10. 'Yansanda na bincike kan kashe tsohon shugaban ƙaramar hukuma a jihar Bauchi

    Wani mutum da wuka a hannu

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta ce ta kama mutum ɗaya bisa zargin kashe tsohon shugaban ƙaramar hukumar Jama'are Isa Wabi.

    A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Juma'a, waɗanda ake zargin abokan ɗansa ne kuma sun aikata kisan ne da tsakar daren yau a gidansa da ke Fadaman Mada.

    Nan take aka kai shi asbitin Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa bayan rahoto ya ishe 'yansandan cewa wasu matasa sun caccaka masa wuƙa a wuya.

    "Binciken farko-farko ya nuna wasu mutum biyu ne suka aikata kisan waɗanda abokan ɗan Wabi ne ɗan shekara 24 mai suna Abdulgafar Isa Mohammed," a cewar sanarwar.

    Ta ce dakaru sun tarar da ɗaya daga cikin mutanen a sume kuma aka kai shi asibiti, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

    'Yansanda sun ce sun kama Abdulgafar domin ci gaba da bincike.

  11. Duka kwalejojin ilimi a Najeriya za su fara ba da shaidar digiri

    Kwalejin ilimi ta Kano

    Asalin hoton, FCE Kano

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara aiwatar da sabon tsarin Dual Mandate Policy a dukkan kwalejojin ilimi na ƙasar wanda ke ƙunshe cikin sabuwar dokar kwalejojin ilimi ta 2023.

    A cewar wata sanarwa daga ma'aikatar ilimi, dokar ta bai wa dukkan kwalejojin damar bayar da shaidar karatu ta digiri da kuma NCE a lokaci guda a fannin koyarwa.

    Ministan Ilimi Tunji Alausa ya siffanta tsarin a matsayin "babba kuma na cigaba".

    "Wannan tsari na Dual Mandate Policy ba gyara ba ne kawai, gagarumin sauyi ne da ke bai wa kwalejojin damar bayar da shaidar NCE da kuma digiri," in ji ministan kamar yadda sanarwar ta ruwaito.

    "Tsarin zai ƙarfafa kwalejojin, ya ƙara yawan damar samun ilimi, kuma ya kyautata ingancin azuzuwan koyarwa a faɗin Najeriya."

  12. Hukumomin Jamus sun ayyana jam'iyyar AfD mai tsattsauran ra'ayi

    Jamus

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar tattara bayanan sirri a Jamus ta ayyana jam'iyyar AfD ta ƙasar a matsayin ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi.

    A cewar wakilin BBC, jam'iyyar Alternative for ko AfD ta zo ta biyu a zaɓen ƴanmajalisar dokoki da aka gudanar a baya-bayan nan.

    Hukumar tattara bayanan sirrin ta ce AfD tana son tsame mutane daga harkokin zaɓe saboda asalinsu ko ƙabilarsu wanda hakan, a cewar hukumar, ya yi hannun riga da tanadin kundin tsarin mulkin Jamus.

    A martanin da ta mayar, AfD ta kira matakin da aka ɗauka kanta a matsayin babban koma-baya ga dimokuraɗiyya.

  13. Gwamnan Edo Okpebholo ya ƙara wa ƙananan ma'aikata albashi

    Gwamnan Edo

    Asalin hoton, Edo State Government

    Gwamnan jihar Edo a kudancin Najeriya ya ƙara yawan albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikata daga N70,000 zuwa N75,000.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya Nan ya ruwaito Gwamna Monday Okpebholo na bayyana hakan a birnin Benin yayin jawabinsa na jiya Alhamis a bikin Ranar Ma'ikata.

    "A yau ina mai farin cikin sanar da cewa gwamnatinmu ta amince da sabon albashi mafi ƙanƙanta na N75,000 ga dukkan ma'aikatan Edo," in ji shi.

    "Wannan wata hanya ce ta gode muku ma'aikatan Edo. Mun yi imanin hakan zai yi tasiri ƙwarai kuma mun dogara da jajircewarku wajen inganta jihar Edo."

    Har yanzu akwai jihohin Najeriya da ba su fara biyan mafi ƙanƙantar albashi na N70,000 ba, wanda gwamnatin tarayya ta ayyana a watan Yulin 2024.

  14. Saudiyya ta saka tarar riyal 20,000 ga masu yin aikin Hajji ba bisa ƙa'ida ba

    Aikin Hajji

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta tabbatar da cewa duk mutumin da aka kama yana taimaka wa mutane wajen yin aikin Hajji ba bisa ƙa'ida ba zai fuskanci tarar riyal 100,000.

    Tarar za ta shafi duk wanda da ke ɓoye maniyyatan da ba su da cikakkun takardu a gidajensu, ko nema musu biza, ko kuma yin jigilarsu.

    Lokutan da dokokin suka shafa su ne daga 1 ga watan Zulƙi'ida (wanda ya yi daidai da 29 ga watan Afrilu) har zuwa 14 ga watan Zulhijja (10 ga watan Yuni).

    Duk mutumin da aka kama yana ƙoƙarin gudanar da aikin Hajjin ba tare da takardun izini ba zai fuskanci tarar riyal 20,000.

    Sannan kuma za a mayar da shi ƙasarsa tare da hana shi shiga Saudiyya tsawon shekara 10.

    Irin wannan tarar za a yi wa duk wanda aka kama da kowace irin biza ta ziyara wadda ta gama aiki yana ƙoƙarin shiga ko ci gaba da zama a garin Makka ko Madina a cikin lokutan da aka bayyana.

  15. Isra'ila ta kai hari kusa da fadar shugaban Syria

    Isra'ila ta ce ta kai hari a kusa da fadar shugaban ƙasar Syria da ke birnin Damascus don nuna goyon baya ga mabiya addinin Druz marasa rinjaye a kasar.

    Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce harin saƙo ne ga gwamnatin Syria kan kasarsa ba za ta zuba ido a aike dakarun sojin mabiya Sunni zuwa yankin da Druze suke ba.

    Isra'ila ta kai harin ne a jiya Alhamis bayan arangamar da aka yi tsakanin mabiya addinin gargajiya na Drzue da ke kudancin birnin Damascs da dakarun gwamnati, inda gwamman mutane suka mutu.

    A bangare guda kuma, shugaban mabiya addinin mai suna Sheikh Hikmat al-Hijri ya zargi gwamnatin Ahmad al-Sharaa da yi musu kisan ƙare-dangi.

  16. Masu garkuwa sun kashe limami a jihar Zamfara da 'ya'yansa uku - Amnesty

    'Yanbindiga

    Asalin hoton, Social Media

    Kisan gillar da wasu ƴanbindiga suka yi wa babban limamin Maru a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Alƙali Salihu Suleiman, da ƴaƴasa uku ya harzuƙa al'umma.

    Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayyana lamarin a matsayin "wani mummunan matsayi" da matsalar garkuwa da mutane ta kai a Najeriya.

    Cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar a Najeriya Isa Sanusi ya ce limamin mai shekara 79 da ƴaƴansa uku sun shiga hannun ƴanbindiga ne a lokacin azumin watan Ramadana a watan Maris kuma sun kashe su ne duk da karɓar kuɗin fansa naira miliyan 11 cikin miliyan 20 da suka buƙata.

    Amnesty ta bayyana cewa waɗanda lamarin ya shafa sun fuskanci "matsananciyar azaba" a hannun ƴanbindigan.

    "Baya ga dukan da aka dinga yi musu kullum, yanbindigan sun hana su abinci da ruwa na tsawon lokaci

    "Amnesty International na Allah wadai da wannan kisan gilla. Abu ne mai tayar da hankali yadda irin waɗannan laifuka ke ci gaba da faruwa ba tare da hukunta masu aikata su ba."

  17. Gwamnan Katsina ya ba da hutun aiki saboda ziyarar Tinubu

    Dikko Radda

    Asalin hoton, Katsina State Government

    Gwamnan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ya ayyana yau Juma'a a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin "tarɓar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu" da ke ziyara a jihar tasu.

    Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin jawabin da ya gabatar a taron Ranar Ma'aikata.

    "Ina mai farin cikin shaida muku cewa Shugaba Tinubu zai kawo ziyara Katsina gobe [Juma'a] domin buɗe ayyuka da dama da muka kammala cikin shekara biyu da suka wuce," in ji gwamnan.

    "Saboda haka, na ayyana goben a matsayin ranar hutu saboda ma'aikata su samu damar haɗuwa da mu wajen tarɓar shugaban ƙasa."

    A jiya Alhamis ne fadar shugaban Najeriya ta sanar cewa Tinubu na jam'iyyar APC zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar da ke arewa maso yamma kuma ta tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

  18. Amurka ta cire haraji kan kaya marasa tsada daga China

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta kawo ƙarshen cire haraji kan wasu kayayyaki da ba ma su tsada ba da ake shiga da su ƙasar daga China.

    A baya Amurkawa na iya sayan kayayyakin China da ba su haura dala 800 ba, idan za su yi oda ta intanet ba tare da wani haraji ba, amma yanzu za su biya kashi 120.

    Ana sa ran harajin zai fara aiki nan take, kuma wasu Amurkawa masu sayayya za su ji a jikinsu.

    Hakazalika su ma yawancin kamfanonin China da ke samar da kayan da shigar da su can.

  19. Ƙungiyoyin agaji a Gaza sun yi gargaɗin rufe sauran wuraren dafa abincin Falaɗinawa

    ...

    Ƙungiyoyin agaji a Gaza sun yi gargaɗin cewa nan da kwanaki masu zuwa, tilas za su rufe sauran gwamman wuraren dafa abincin da dubun-dubatar Falaɗinawa suka dogara da su.

    Watanni biyu kenan da Isra'ila ta toshe duk wata hanyar shigar da kayan agaji Gaza

    Ana kuma gargaɗin wannan zai janyo mummunar yunwa da ba a taɓa gani ba.

    Samy Mahdi na ƙungiyar agaji ta ANIRa ya bayyana damuwa kan hakan inda yace a baya su kan dafa shinkafa da nama da nau'in abinci mai gina jiki, amma yanzu babu nama bare kayan lambun da suka shigo da su Gaza.

    Manyan jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun koka kan abin da suka kira zalunci da azabtar da Falasdinawa.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Juma'a..

    Sannunmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, wanda zai kawo rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Aisha Babangida ne ke tare da ku a wannan safiya bisa kulawar Usman Minjibir.