An saƙo ɗan jaridan da aka kama bisa kuskure a Kenya

Asalin hoton, Ruth Nesoba/BBC
Ƴan sandan Kenya sun saki wani gogaggen ɗan jarida bayan da suka kama shi a ofishin ƴan sanda inda suka tumurmusa shi cikin wata mota.
Macharia Gaitho, mai shekaru 65, ya ce wasu motoci biyu ne suka bi shi a kusa da gidansa da ke Nairobi babban birnin ƙasar a lokacin da ya ke tare da dansa mai shekaru 19, wanda ya tuka shi da shi zuwa wani ofishin ƴan sanda da ke kusa don kare lafiyarsa – inda aka jefa shi da karfi cikin mota aka yi gaba da shi.
Daga baya ƴan sanda sun ce lamarin kuskure ne, domin sun daɗe suna farautar wani mutum da suke zargi da katsalandan cikin binciken da ƴan sanda ke yi kan wanda ake zargi da kisan kai.
Wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jami’a sa sanye da kayan sarki suka tursasa dan jaridar cikin wata farar mota.
Hakan ya haifar da martani mai zafi daga ƴan ƙasar ta Kenya a shafukan intanet, inda ake ta zargin jami’an tsaro da sace mutanen da ake ganin suna da alaƙa da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a baya-bayan nan.