Ƙarshen rahotonni
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na Laraba, 15 ga watan Mayu.
Ku duba ƙasa don karanta labaran da muka wallafa a yau ɗin, kafin mu kawo sababbi gobe da safe.
Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya.
window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 15 ga watan Mayun, 2024.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na Laraba, 15 ga watan Mayu.
Ku duba ƙasa don karanta labaran da muka wallafa a yau ɗin, kafin mu kawo sababbi gobe da safe.
Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya.
Asalin hoton, EPA
A wani lamari na rarrabuwar kawuna da ba kasafai ake samu ba a majalisar yaƙi ta ministocin Isra'ila, ministan tsaro ya soki rashin amincewa da shirin mulkin Gaza bayan Isra’ila ta kammala yaƙi da Hamas.
Yoav Gallant ya ce cigaba da kwan gaba kwan baya kan lamarin na iya haifar da barazana ga tsaron Isra'ila.
Ya dage kan cewa dole hukumomin Falasdinawan da ke samun goyon bayan kasashen duniya ne ya kamata su shugabanci yankin, ba mulkin sojan Isra'ila ba.
Kalaman na Mista Gallant sun yi daidai da na babban jami'in diflomasiyyar Amurka, Antony Blinken.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce tattaunawa kan yadda za a gudanar da mulkin Gaza nan gaba magana ce kawai muddin Hamas ta ci gaba da kasancewa a yankin.
Asalin hoton, NG Police
Mutanen da suka rasu a wutar da ake zargin wani mutum ya cinna wa masallaci a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ƙaru zuwa takwas.
Da safiyar yau Laraba rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta kama Shafi’u Abubakar mai shekara 38 da ake zargin ya kunna wa masallacin wuta lokacin da mutane fiye da 30 ke sallar Asuba a ciki.
Lamarin ya faru ne a garin Gadan na ƙaramar hukumar Gezawa.
Wani mazaunin ƙauyen mai suna Hamisu Abdullahi ya faɗa wa BBC cewa mutum takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu zuwa yammacin yau Laraba.
"Yanzu haka an kawo gawar mutum bakwai da muka yi wa jana'iza, ɗayan kuma sai gobe da safe za a binne shi," in ji shi yana mai cewa ɗaya daga cikinsu ɗan'uwansa ne.
Ya ƙara da cewa "waɗanda suka rage a asibitin za su kai kamar 22".
'Yan sanda sun ce mutumin ya yi amfani da bam ɗin da aka haɗa da man fetur, inda mutum 24 duka maza suka ji raunuka, 20 daga cikinsu manya da kuma yara huɗu.
Asalin hoton, Reuters
Shugabannin duniya na ci gaba da yin Allah-wadai da harin da aka kai kan firaministan Slovakia.
Shugaba Biden ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan abin tashin hankali.
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana cewa wannan hari ne kan dimokuradiyya, yayin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce bai kamata irin wadannan hare-hare su zama ruwan dare ba.
Shugaba Putin ya bayyana Mista Fico a matsayin mutum mai jajircewa kuma mai kaifin tunani.
"Ba a saba ganin iriin wannan lamarin a wannan bangaren duniya ba, an san cewa dai akan yi hatsaniya a tarukan siyasa, haka ma a wuraren zanga-zanga amma da wuya a ga tashin hankali irin wannan," a cewar wakilin BBC.
Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyoyin gasar Premier League ta Ingila za su kaɗa ƙuri'ar amincewa ko akasin haka kan cigaba da amfani da na'urar VAR mai taimaka wa alƙalin wasa a wata mai zuwa.
Kulob ɗin Wolves ya miƙa ƙudiri a hukumance zuwa ga hukumar Premier, abin da zai sa a kaɗa ƙuri'ar lokacin da mambobin gasar za su gana ranar 6 ga watan Yuni.
Ƙungiyar ta ce an ƙaddamar da VAR ɗin ne da "kyakkyawar manufa" amma kuma ta koma jawo abubuwan da ba a nufata ba da ke lalata alaƙar 'yan kallo da wasan ƙwallon ƙafar".
An fara amfani da VAR a 2019 domin taimaka wa tawagar alƙalan wasa da ke cikin fili yanke hukunci, amma kuma an samu matsaloli da wasu hukunce-hukuncen a wannan kakar.
"Matsalar da muke samu wajen ba da hukunci daidai bai dace da al'adar wasanni ba," in ji sanarwar da Wolves ta fitar.
Asalin hoton, NAHCON
Asalin hoton, NAHCON
Asalin hoton, NAHCON
Asalin hoton, NAHCON
Asalin hoton, NLC
Ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun yi watsi da tayin da gwamnatin tarayya ta yi na naira 48,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙaranci ga ma'aikatan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC suka fitar, sun bayyana tayin na gwamnatin tarayya a matsayin abin ban takaici.
Sanarwar ta ce "Tayin da gwamnati ta yi na 48,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci tamkar cin fuska ne ga ma'aikatan Najeriya kuma ya yi ƙaranci idan aka kwatanta da buƙatun da ƙungiyoyin suka gabatar."
A kan haka ne ƙungiyoyin ƙwadagon suka yanke shawarar ficewa daga tattaunawar da ake yi kan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata, tare da yin kira ga gwamnati da ta sake tunani domin gabatar da tayin da ya fi dacewa domin samun matsay.
A bayan ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta gabatar da buƙatar tsayar da mafi ƙarancin albashi a kan naira 615,000.
NLC ta ce ta yi hakan ne la'akari da halin matsin rayuwa da tashin farashin kayan masarufi da al'ummar ƙasar ke fuskanta.
Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi ne tun bayan da shugaban ƙasar ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Wata kotu ta hana 'yan siyasa kuma masu sukar Shugaban Rwanda Paul Kagame yin takarar shugaban ƙasa.
Bernard Ntaganda mai shekara 55 ya nemi kotun ta ɗage haramcin don ya shiga zaɓen.
Dokokin Rwanda sun haramta wa mutanen da kotu ta ɗaure sama da wata shida riƙe muƙamin siyasa.
Babbar kotun ta ƙi amincewa da buƙatar Mista Ntaganda a yau Laraba, tana mai cewa ya gaza biyan kuɗaɗen shari'ar da aka taɓa yi masa a baya.
"Babbar kotun ta gano cewa Ntaganda bai yi biyayya ga dokokin da suka tanadi mutum ya nemi a janye ɗaurin da aka yi masa ba, sabod haka an yi watsi da ƙarar da ya ɗaukaka," a cewar hukuncin kotun kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin man Fetur ta OPEC ta ce yawan man da Najeriya ke tonowa a kowace rana ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.28 a kowace rana cikin watan Afrilu.
Cikin rahoton wata-wata da ƙungiyar ke fitarwa, da ta fitar ranar Talata ya nuna cewa ƙasar ta samu ƙarin kashi 4.04 cikin 100 na man fetur din da ta fitar a cikin watan Afrilu, daga ganga miliyan 1.23 zuwa miliyan 1.28
Wannan ne karo na farko da aka samu ƙari a man da ƙasar ke tonowa a cikin shekarar da muke ciki.
Da wannan ne Najeriya ta karɓi matsayinta na ƙasar da ta fi kowace ƙasar tono man fetur a Afirka, inda Aljeriya ke biye mata wadda ta fitar da ganga 907,000 a kowace rana cikin watan an Afrilu.
Najeriyar dai na samun kaso mafi tsoka na arzikinta daga man fetur, sai dai duk da wannan nasara da ƙasar ta samu, 'yan ƙasar na kokawa kan tsadar man fetur ɗin a acikin ƙasar.
Asalin hoton, AFP
Masu gabatar da ƙara a kotun duniya sun tabbatar da mutuwar mutanen da suka aikata laifukan yaƙi a kisan kiyashin Rwanda a 1994, waɗanda kuma ake neman su.
An zargi Ryandikayo, wani ɗan kasuwa wanda aka san shi da suna guda ɗaya kwal wanda kuma tsohon magajin gari ne da Charles Sikubwabo, da hannu a kitsa da hannu a kisan kiyashin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban 'yan ƙabilar Tutsi.
Ofishin mai gabatar da ƙarar ya ce dukkan mutanen da suka bar ƙasar sun mutu a shekarar 1998.
Hukumomi a Rwanda sun ce suna ƙoƙarin tabbatar da cewa kimanin mutanen da suka tsere sakamakon hannun a rikicin sun gurfana a gaban kuliya.
Asalin hoton, Nahcon
Rukunin farko na maniyyatan Najeriya ya tashi zuwa ƙasar Saudiyya domin fara ibadar aikin Hajjin bana.
Tawagar farkon ta tashi ne daga filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da ke birnin Kebbi na jihar Kebbi da ke arewacin ƙasar.
Gabanin fara jigilar maniyyatan sai da hukumar da gudanar da wani ƙwarya-ƙwaryar bikin ƙaddamar da jigilar maniyyatan.
Cikin waɗanda suka halarcin bikin ƙaddamarwar har da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima.
Ga Karin bayani a rahoton Buhari Muhammad Fagge
Asalin hoton, Siminalayi Fubara/X
Kwamishinonin ilimi da gidaje na jihar Rivers, Farfesa Chinedu Mmon da Gift Worlu sun ajiye muƙamansu saboda abin da suka kira ''hatsarin da ke cikin ayyukansu''.
Mista Mmon da Mista Worlu - waɗanda masu biyayya ne ga tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike - su ne kwamishinoni na uku da na huɗu da suka ajiye muƙamansu bayan tsamin dangantaka tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara da tsohon gwamna Wike.
Cikin wata wasiƙa da ya aike wa gwamnan ta hanyar ofishin sakataren gwamnatin jihar, tsohon kwamishin ilimin ya ce ya ajiye muƙaminsa ne saboda wurin aikinsa ba shi da daɗi.
A baya-bayan nan dai dangantaka na ƙara yin tsami tsakanin ɓangaren ministan Abujan, da Gwamna Fubara.
A ranar Litinin ne gwamnan ya zargi tsahon gwamnan da bar wa jiharsa tilin bashi, bayan sauka daga mulki.
Asalin hoton, Reuters
An jikkata firaiministan Slovakia, Robert Fico sakamakon harbin bindiga kamar yadda rahotanni ke cewa.
Rahotanni dai sun ce an harbi mista Fico a ƙofar cibiyar baje al'adun gargajiyar ƙasar da ke garin Handlova, inda ake gudanar da wani taron gwamnatin.
'Yan jarida sun rawaito cewa an ji ƙarar harbe-harbe.
Tuni 'yan sanda suka tsare mutumin da ake zargi da harbin shugaban, inda shi kuma mista Fico yake samun kulawa a asibiti.
Handlova ta kasance mai nisan kilomita 180 daga arewa maso gabashin birnin Bratislava na ƙasar.
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 33.69 a cikin watan Afrilu, idan aka kwatanta da watan Maris da yake kashi 33.20.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba ta ce an samu ƙarin kashi 0.49 tsakanin watan Maris zuwa tana na Afrilu.
Kayan abinci ne kan gaba wajen tashin farashin daga nan sai man girki da kaji.
Hukumar ta ce idan aka ƙwatantan ƙarin a shekara, za a ga cewa an samu ƙarin kashi 11.47 a shekarar da muke ciki idan aka kwatanta da watan Afrilun 2023, wanda a lokacin yake kashi 22.22.
'Yan Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki, lamarin da ya jefa yan ƙasar da dama cikin mawuyacin hali da matsin tattalin arziki.
Asalin hoton, Shutterstock
Hukumar agajin gaggawa ta Ukraine ta ce tana kwashe mutum 8,000 daga yankin Khirkiv sakamakon harin dakarun Rasha a garuruwan kan iyaka da suka fara ranar Juma'a.
A tasharta ta kafar Telegram, hukumar ta ce mafi yawancin waɗanda aka kwashe mata ne da tsaffi da mutanen da ba sa iya tafiya da nakasassu da ƙananan yara.
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken yana kammala wata ziyara zuwa Kyiv, inda ya ce Amurka za ta samar da ƙarin dala biliyan biyu domin sayen makamai ga Ukraine.
Mista Blinken ya ƙara da cewa kuɗin za su samar da makamai a "yau" sannan a sanya jari a masana'antun ƙasar nan gaba.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya soke duk wasu tafiye-tafiye zuwa ƙasashen wajen a daidai lokacin da dakarunsa ke fafutukar shan kan dakarun Rasha.
A ranar Juma'a, Rasha ta ƙaddamar da sabon farmaki a kusa da Kharkiv, birni na biyu magi girma a Ukraine.
Yanzu dai Ukraine ta janye dakarunta daga ƙauyukan da ke kan iyakoki sakamakon matsin lamba da musayar wuta da sojojin ke fuskanta.
Wata kotu a Switzland ta yanke wa tsohon ministan cikin gida na Gambiya hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari saboda samunsa da laifukan cin zarafin bil-adama da aka gudanar lokacin da Yahya Jammeh ke kan mulki.
A shekarar 2016 ne Ousman Sonko ya gudu zuwa Switzerland, gabanin Mista Jammeh ya yi rashin nasara a zaɓen shugaban ƙasar.
Switzerland ta yi masa shari'a ne bisa dokar da ta ba ta damar gurfanar da mutanen da suka aikata laifuka ko ina a faɗin duniya.
Da farko Ousmane Sonko ya yi fatan samun mafakar siyasa a Switzerland bayan da aka sauke shi daga muƙamin ministan cikin gida na Gambiya.
To amma sai wata ƙungiyar ta gabatar da hujjoji daga shaidu da dama da suka alaƙanta shi da aikata laifukan cin zarafin bil-adama.
Masu shigar da ƙara sun ce mista Sonko - wanda shi ne tsohon shugaban 'yan sandan ƙasar - ya goyi baya, tare da kasa hana jami'an tsaron ƙasar far wa masu adawa da tsohon shugaban ƙasar Yahya Jammeh.
Wani lauyan kare haƙƙin bil-adama da ke cikin shari'ar ya ce samun Sonko da laifi na tabbatar da cewa adalci ba ruwansa da iyaka.
Wannan ne karo na biyu da kotun ta Switzerland ke yanke wa wani mutum hukunci bisa dokar bai ɗaya kan laifukan cin zarafin bil-adama.
Hukunci na farko da kotun ta taɓa yankewa shi ne na watan Yunin 2023, lokacin da ta yanke wa tsohon shugaban 'yan tawayen Laberiya, Alieu Kosiah hukuncin ɗaurin shekara 20 kai laifukan cin zarafi dasuka haɗa da fyaɗe da kisan kai da cin tsokar mutane.
Wasu ƙasashen irin su Jamus da Amurka na gudanar da wasu shari'o'i kan tsoffin kusoshin gwamnatin Mista Jammeh.
Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Babba Bankin Ƙasar, Godwin Emefiele a gaban kotun kan zargin amincewa da kashe naira biliyan 18.96 wajen buga takardun kuɗi na naira miliyan 684.5.
An gurfanar da tsohon gwamnan ne a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume guda huɗu.
To sai dai mista Emefiele ya musanta duka zarge-zargen da aka tuhume shi a kansu.
Kan haka ne lauyansa ya nemi kotun ta bayar da belinsa, inda aka bayar da belinsa kan naira miliyan 300, da sharaɗin mutum biyu da suka tsaya masa.
Haka kuma kotun ta ce dole ne tsohon gwamnan babban bankin ya gabatar mata takardun biza da fasfonsa, kuma ba zai fice daga ƙasar ba, dole sai da izinin kotun.
Godwin Emefiele ya fuskanci jerin tuhume-tuhume tun bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya dakatar da shi a shekarar da ta gabata kan zargin saɓa ƙa'idan aiki.
Asalin hoton, Kano Police
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta cafke wani matashi da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta a lokacin da mutane fiye da 30 ke sallar Asuba a ciki.
Al'amarin dai ya faru ne a a ƙauyen Larabar Abasawa a ƙaramar hukumar Gezawa.
A wata sanarwar da rundunar ta fitar, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin mai suna Shafi'u Abubakar mai shekara 38 ya yi sanadiyyar ƙonewar mutane.
Tuni dai aka kwashe mutum 24 waɗanda suka ƙone zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu, kuma mutum ɗaya ya rasu.
SP Kiyawa ya ƙara da cewa binciken da aka gudanar dai ya nuna cewa an yi amfani da man fetir ne wajen cinna wutar.
Dangane kuma da dalilin faruwar al'amarin, SP Kiyawa ya ce "matashin ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon ƙin raba gado a tsakanin danganinsa, inda ya ce waɗanda suka zalunce shi ɗin suna cikin masallacin a lokacin da suke sallah. Kuma ya yi hakan ne domin ya aike da saƙo." In ji matashin.
Hukumomin Aljeriya sun ce sun gano wani mutum da ya ɓata fiye da shekara 25 a gidan makwabcinsa a lardin Djelfa da ke arewacin ƙasar
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce Bin Omran Omar ya ɓata a tsakanin shekarun 1996 da 1998, a lokacin yaƙin basasar ƙasar.
Kafar yaɗa labarai ta Echorouk ta ce an same shi a wani ramin ƙarƙashin ƙasa da aka rufe da ciyawa.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato kafofin yaɗa labaran ƙasar, na cewa wanda ya kama shin ya tsare shi a wurin da ba zai iya neman taimako ba.
AFP ya ce ɗan uwan wanda ya kama mutumin ne fallasa shi a shafukan sada zumunta a lokacin da suka samu saɓani a kan gado.
Tuni hukumomin ƙasar suka garzaya da mutumin mai kimanin shekara 40 zuwa asibiti domin duba lafiyarsa.
An dai kama mutumin da ake zargi da tsare mutumin mai kimanin shekara 61.