window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Rasha ta gargaɗi Ecowas kan tura sojoji Nijar

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar and Rabiatu Kabir Runka

  1. Bankwana

    Masu bibiyarmu a wannan shafi, da haka muka kawo ƙarshen rahotannin na kai-tsaye.

    Rabiatu Kabir Runka ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Majalisar Ɗinkin Duniya ta kammala kwashe sama da gangar mai miliyan ɗaya daga Yemen

    ...

    Asalin hoton, COEN DE JONG/UNDP

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ta kammala aikin kwashe sama da gangar mai miliyan ɗaya daga wani lalataccen jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun Yemen.

    Ana fargabar jirgin wanda ake amfani da shi a matsayin wani rumbu tun shekarun 1980, zai iya darewa.

    Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce sauya wa man waje ya kare haɗarin da, da zai iya kasancewa gagarumin bala'i ga muhalli da kuma dan'Adam.

    Rabon da a kula da gyaran jirgin ruwan, tun lokacin da yaƙi ya ɓarke a Yemen, shekara takwas da ta wuce, Yanzu kuma za a mayar da hankali ne wajen wanke tankunan ajiyar man kafin kuma a janye jirgin daga inda yake.

  3. Sojojin Najeriya sun ceto tsohon shugaban kwalejin ilimi da ɗansa a Zamfara

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Army/Twitter

    Rundunr sojin Najeriya ta ce kubutar da tsohon shugaban kwalejin ilimi ta tarayya da ke Gusau Dakta Hassan Abubakar Augie tare da ɗansa daga hannun masu garkuwa da mutane.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinsa na Tuwita, sun dakarunsu na rundunar Hadarin Daji da ke Mada ne suka kubutar da Dakta Augie tare da ɗansa a lokacin wani sintiri da suka gudanar da a kan hanyar Shemori zuwa Yandoto.

    Sanarwar ta ce dakarun sun fatattaki 'ayn bindigar masu yawa, inda suka yi musayar wutar da su.

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Army/Twitter

    Sojojin sun ce 'yan bindigar sun gudu zuwa cikin daji bayan da suka ji wuta daga ɓagaren sojojin, tare da barin mutanen biyu da suka sacen..

    Binciken farko ya nuna cewa an sace mutanen biyu ne a daren ranar Alhamis a gidan Dakta Augie, inda aka tafi daji da su inda suka ci gaba da tsare su, har zuwa lokacin da sojojin suka isa wajen.

    Sojoji

    Asalin hoton, Nig.Army/Twitter

    Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato babura biyu na 'yan bingidar a lokacin gumurzun.

    Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da rikice-rikicen 'yan bindiga da ke sace mutane domin neman kudin fansa

  4. Remi Tinubu ta gana da wata ƴar Chibok da aka ceto

    Remi Tinubu

    Asalin hoton, Presidency

    Uwar gidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta gana da ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok 276 da ƴan Boko Haram suka sace sama da shekaru tara da suka gabata.

    An sace ƴan matan ne a ranar 14 ga watan Afrilu na 2014, lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

    Uwar gidan shugaba Tinubu ta tarbi Rebecca Kabu tare da uwar gidan matamakin shugaban Najeriyar Nana Shettima.

    Misis Remi ta yi wa yarinyar alƙawarin kula da ita da kuma mayar da ita makaranta a duk lokacin da take buƙata.

    Ta kuma ce gwamnati ba ta manta da sauran ɗaliban da ke tsare a hannun Boko Haram ba.

    Uwar gidan shugaban Najeriyar ta kuma miƙa godiyarta ga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da kuma hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya, da sauran dukkan waɗanda suka tallafa wajen kuɓutar da Rebecca.

    Sanata Oluremi ta ce "Idan aka ilmantar da yara masu tasowa, za su taimaka wajen ɗorewar abubuwan ci gaba."

  5. Peter Schmeichel ya bai wa Onana shawara

  6. Rasha ta gargaɗi Ecowas kan tura sojoji Nijar

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Rasha Vladimir Putin

    Ƙasar Rasha ta gargaɗi ƙungiyar Ecowas game da ɗaukar matakin soji da ta ce za ta yi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

    Tana mai cewa matakin ka iya haifar da rikicin da zai daɗe ba a ga ƙarshensa ba.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar ranar Juma'a ta gargaɗi ƙasashen yammacin Afirka da kada su aika sojoji zuwa Nijar.

    Sanarwar ta ce ''Mun yi imanin cewa matakin soji ba zai warware matsalar Nijar ba, a maimakon haka lamarin zai haifar da mummunan rikici, wanda ba a san ranar ƙarewarsa ba, tare da sake dagula lamura a yankin Sahel''.

    Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas na shirin wata ganawa a ranar Asabar domin tsara yadda za a shirya dakarun sojin.

    A ranar Juma'a ne ƙungiyar Ecowas ta amince da kafa 'rundunar ko-ta-kwana' a shirye-shiryen ɗaukar matakin soji kan sojojin na Nijar.

    Tuni dai shugaban ƙasar Ivory Coas, Alassane Ouattara, ya ce ƙasarsa za ta tura sojoji kimanin 1,000 waɗanda za su bi sahun sauran dakarun ko-ta-kwana da za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don tura wa Nijar.

    Ƙasashen Amurka da Faransa da kuma Tarayyar Turai tuni suka goyi bayan matakin da ƙungiyar Ecowas ta ɗauka, domin mayar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan karagar mulki.

    d

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Magoya bayan sojojin na Nijar riƙe da tutar ƙasar Rasha sun gudanar da zanga-zanga

    A ranar Juma'a magoya bayan sojojin na Nijar riƙe da tutar ƙasar Rasha sun gudanar da zanga-zanga a harabar ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai.

    Inda suka riƙa kiran ƙasashen yamma su fice daga ƙasar tare da kira ga Rasha ta kawo musu ɗauki.

    Rasha dai ba ta fito ƙarara ta goyi bayan juyin mulkin na Nijar ba.

    Ƙasashen Faransa da Amurka na da sansanonin soji a Nijar, domin yaƙar masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

  7. Wasu batutuwan da suka shafi Premier League ta bana

  8. An amince motoci marasa matuƙa su fara ɗaukar fasinja

    d

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a jihar California ta Amurka ta amince da faɗaɗa ayyukan tasi marasa matuƙa zuwa birnin San Francisco, tare da ba su damar ɗaukar fasinjoji.

    A yanzu an bai wa kamfanoni Waymo da Cruise da ke ƙera irin waɗannan motoci damar fara ɗaukar fasinjoji da motocin a birnin.

    An fara amfani da direbobi marasa matuƙa a birnin San Francisco a shakarar 2014, tare da samar da mutumin da zai zauna ciki domin kula da lafiyar direbobin.

    Masu sukar tsarin sun ce motocin suna da hatsari, sannna sukan janyo cunkoso ga manya da ƙananan tituna.

    Masu goyon bayan shirin sun ce motocin za su taimaka wa masu lalura ta musamman tare da kawar da bambance-bambancen da ake nuna wa fasinjoji.

  9. An gudanar da zanga-zanga a Katsina kan taɓarɓarewar tsaro

    hoto

    Asalin hoton, Ma'azzam Amadu

    Bayanan hoto, Al'ummomin wasu garuruwa a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin daɗinsu kan taɓarɓarewar matsalar tsaro a yankunansu.
    hotuna

    Asalin hoton, Ma'azzam Amadu

    Bayanan hoto, Mutanen yankunan ɗauke da kwalaye sun yi ta rera waƙoƙin kira ga gwamnati ta kawo masu ɗauki.

    hoto

    Asalin hoton, Ma'azzam Amadu

    Bayanan hoto, Mutanen yankin sun koka kan kan taɓarɓarewar tsaro, musamman yadda 'yan bindiga ke ci gaba da sace mutane, domin neman kuɗin fansa. Waniu mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun addabe su ba dare ba dare inda suke sace mutane da dukiyoyinsu.
    hoto

    Asalin hoton, Ma'azzam Amadu

    Bayanan hoto, Mata na daga cikin mutanen da suka halarci zanga-zangar ta lumana. Jihar Katsina na daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan 'yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.
  10. ECOWAS za ta ɗora wa Rasha laifi idan Wagner ta shiga Nijar

    b

    Kungiyar tattalin arzikin Afirka ta Yamma Ecowas ta ce za ta ɗora wa Rasha laifi matuƙar kungiyar sojojin hayar Rasha ta Wagner ta shiga jamhuriyar Nijar.

    Ecowas ta bayyana shigar wagner jamhuriyar Nijr a matsayin keta hakkin bil-adama.

    babban kwamishinan hukumar mai lura da zaman lafiya, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ne ya bayyana haka lokacin wata tattaunawa da gidan Talbijin na Channels ranar Juma'a.

    Ya ci gaba da cewa ''A yanzu Wagner na ƙasar Mali , kuma gwamnatin Mali ta ce wanna yarjejeniya ce ta ƙulla da ƙasar Rasha.''

    “Dan haka za mu yi musu hukunci da kalamansu, waɗanda ke nuna ayyukansu na keta hakkin bil-adama, ayyukan ƙungiyar Wagner ka iya wargaza yankinmu, matuƙar sojojin wagner suka shiga Nijar, to za mu ɗora alhakin kan ƙasar Rasha.”

    • Manyan hafsoshin sojin Ecowas za su gana don tsara shirin tunkarar Nijar
    • Ecowas ta umarci dakarunta su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar
  11. Manyan hafsoshin sojin Ecowas za su gana don tsara shirin tunkarar Nijar

  12. EU ta tallafa wa INEC da kayan aiki don inganta harkokin zaɓe a Najeriya

    f

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta samu kyautar wasu kayan aiki daga ƙungiyarTarayyar Turai ta EU, da za su taimaka wajen inganta harkokin zaɓen ƙasar.

    Shugabanb hukumar zaɓen ƙasar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, lokacin karɓar kayayyakin a Abuja bban birnin ƙasar.

    Farfesa Yakubu ya ce sabbin kayan aikin za su taimaki hukumar zaɓen ƙasar wajen inganta harkokin zaɓenta.

    Yav ƙara da cewa akwai wasu ƙarin kayayakin masu yawa da ƙungiyar EU za ta bai wa hukumar tasa.

    ''Waɗannan kayayyaki za su taimaka wa hukumar zaɓen wajen inganta harkokinta a ɓangarori da dama'', in ji shugaban hukumar.

    Kungiyar ta EU dai na daga cikin kungiyoyin da ke sanya idanu a zaɓuklan Najeriya, inda a lokuta da dama, ƙungiyar ke cewa ana tafka kura-kurai a tsarin zaɓukan ƙasar.

  13. Tarayyar Afrika ta bayyana damuwa kan halin da Bazoum ke ciki

    Bazoum

    Asalin hoton, AFP

    Tarayyar Afrika ta bayyana damuwa kan halin da hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum ke ciki.

    Ta ce ba za ta lamunci irin halin da sojojin da suka yi juyin mulki suka sanya Shugaba Bazoum ba.

    Shugaban ƙungiyar, Moussa Faki Mahama ya buƙaci jagororin sojin da suka ƙwace mulki su daina ɓata alaƙa tsakanin Nijar da ƙungiyar Ecowas da kuma sauran ƙasashe Afrika.

    Ya yi kiran a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ƙasar, tare da neman haɗin kan ƙasashen duniya waje kare mutumcin shugaban.

    Tuni dai Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana damuwa kan lafiyar Bazoum da iyalinsa, waɗanda suka shafe mako biyu a hannun sojojin da suka yi juyin mulkin.

    Shugabannin ƙungiyar Ecowas sun riga sun amince da ɗaukar ƙwararan matakai kan sojojin, waɗanda suka yi gargaɗin cewa za su kare kansu daga duk wani mataki da ƙungiyar za ta ɗauka.

    • Tura sojojin Ecowas zai kawo ƙarshen juyin mulkin Nijar?
    • Shiga tsakanin da zai iya hana Ecowas auka wa Nijar da yaƙi

    Latsa hoton da ke ƙasa don sauraren rahoton Ibrahim Isa

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama don sauraren rahoton Ibrahim Isa
  14. Naira miliyan biyu Akpabio ya tura mana 'kuɗin more hutu' - Kawu Sumaila

    Kawu Sumaila

    A Najeriya, wata kungiyar farar hula mai fafutukar kare hakkokin al'umma da sa ido kan harkokin tattalin arziki wato SERAP, ta yi barazanar kai karar shugaban majalisar dattawan kasar, dangane da kuɗin alawus ɗin naira miliyan biyu da ya yi suɓul da bakan sanar da cewa an bai wa ƴan majalisar, don su 'more hutun su' yayin hutun da suka tafi.

    Wannan al'amari, mai cike da ce-ce-ku-ce dai, ya sa hatta wasu 'yan majalisar dattawan ba su ji dadinsa ba.

    Ga rahoton AbdusSalam Ibrahim Ahmed

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton
  15. 'Yan wasan Afirka shida da za su haska a gasar Premier ta bana

  16. Najeriya na bin Nijar bashin sama da naira biliyan huɗu na wutar lantarki

    NERC

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoton da hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta fitar ya ce yanzu haka ƙasar tana bin jamhuriyar Nijar kuɗin lantarki har naira biliyan 4.22.

    Madatsar ruwa ta Kainji da ke jihar Neja ce take samar wa jamhuriyar Nijar lantarkin.

    Nijar tana ƙoƙarin kammala madatsar ruwanta kafin ƙarshen 2025 don magance dogaro kan Najeriya wajen samun lantarki.

    Rahoton ya ce Nijar tana daga cikin abokan cinikin lantarki na Najeriya da ba su biya maƙudan kuɗin wutar da suka sha ba.

    Hukumar kula da lantarkin ta Najeriya dai ta nemi a ɗauki matakin ganin waɗanda lamarin ya shafa sun biya kuɗaɗen lantarkin da suka sha.

  17. Ƴan Rohingya 23 sun mutu, wasu 30 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa

    Rohingya

    Asalin hoton, Getty Images

    An zaƙulo gawawwakin ƴan Rohingya 23 bayan wani hatsarin jirgin ruwa a jihar Rakhine ta Myanmar.

    Akwai kuma mutum 30 da ake ci gaba da nema, yayin da rahotanni ke cewa an ceto wasu takwas.

    Waɗanda suka kuɓuta sun ce suna kan hanyarsu ta zuwa Malaysia ne a lokacin da jirgin ruwansu ya nutse ɗauke da matafiya 50.

    Dubban ƴan Rohingya ne ke yin irin wannan tafiya mai hatsarin gaske don neman tsallakewa zuwa Malaysia ko Indonesia.

    Suna ƙoƙarin tserewa ne daga Myanmar da kuma sansanin ƴan gudun hijira da ya cunkushe a Bangladesh.

    Wani mai aikin ceto ya ce waɗanda suka mutu a cikin wannan mako sun haɗar da mata 23 da maza 10, kuma dukkansu musulman Rohingya ne.

    • Shin duniya ta manta da Musulman Rohingya ne?
    • An yanke wa Aung San Suu Kyi ƙarin ɗauri na shekara bakwai

  18. Isra'ila ta kwashe ƴan ƙasarta daga yankin da ake faɗa a Habasha

    Ethiopia

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta sanar da kashe ƴan ƙasarta fiye da 200 da kuma wasu yahudawan Habasha, daga biranen Amhara da Oromia masu fama da rikici zuwa babban birnin ƙasar Addis Ababa.

    Akwai dubban yahudawa da ke zama a yankin Amhara.

    Sanarwar da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fitar ta umarci a ajiye mutanen a wani wuri na musamman mai ingattaccen tsaro kafin kwashe su zuwa gida.

    Akwai rahoton samun kwanciyar hankali a birnin Amhara, inda aka yi fama da ƙazamin faɗa tsakanin dakarun soji da kungiyoyin mayaƙa.

    Sojoji sun ce sun yi nasarar kwantar da tarzoma a yankin, amma ana ci gaba da samun rahoton tashin hankali a ƙananan ƙauyuka.

  19. Dakarun Najeriya sun kashe ƴan Boko Haram a Borno

    Army

    Asalin hoton, Nigerian Army/Facebook

    Dakarun sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram biyu, a yankin ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno.

    Kakakin rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya ce dakarun sun yi wa ƴan Boko Haram ɗin kwanton-ɓauna ne a wata hanya da suka saba wucewa.

    Nwachukwu, ya ce an yi musayar wuta tsakanin mayaƙan da dakarun soji, inda daga baya sojojin suka yi nasarar fatattakar su da kuma kashe biyu a ciki.

    Haka kuma, kakakin rundunar sojin ya ce dakarun sun ƙwato makamai iri daban-daban, da ƙwaya da kuma kuɗi a hannun mayaƙan na Boko Haram.

    Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya jinjina wa dakarun bisa ƙoƙarin su wajen kawar da abin da ya kira ɓata-gari daga yankin arewa maso gabas da ma sauran sassan Najeriya.

  20. An kulle otel ɗin ƴan luwaɗi a Habasha

    Ethiopian

    Asalin hoton, Addis Ababa City istration

    Hukumomi a Habasha sun ce sun rufe otel-otel da mashaya da kuma gidajen rawa da ake zargin ana ayyukan luwaɗi.

    Hukumar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta Addis Ababa ta ce tana ɗaukar matakin ne a kan duk wani waje da masu neman jinsi guda suna ayyukan su.

    Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a facebook ta ce an gano wuraren ne bayan samun bayanai daga jama'ar gari a kan ɓata-garin da kuma maɓoyarsu.

    Ta kuma ce za ta ci gaba da kai samame irin wuraren da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu.

    Habasha ta haramta luwaɗi, amma a baya-bayan nan ana samun rahotannin ɓullar masu irin wannan ɗabi'a a ƙasar.