Waiwaye: Janye dokar hana fita a Sokoto da komawar Shekarau NNPP
Labarai da dama sun faru a Najeriya a wannan makon da ya gabata, kama daga na siyasa zuwa na zamantakewar al'umma.
BBC ta rubuta wannan makala ne domin yin waiwaiye kan wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya.
Ibrahim Shekarau ya haɗe da Rabi'u Kwankwaso don yaƙar Gwamna Ganduje

A cikin makon da ya gabata ne tsohon gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ya fita daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar NNPP ne domin ceto Jiharsa daga mawuyacin halin da take ciki.
Tsohon gwamnan wanda kuma tsohon Minista ne, ya shaida wa BBC Hausa cewa "mun dade muna tattaunawa da dan uwana Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, muna nuna damuwarmu ga makomar Kano" shi ya sa suka hada gwiwa domin ganin sun fitar da Jihar daga matsalolin da take fama da su.
"Mun tattauna mun gaya wa kanmu cewa wajibi mu kawo sauyi a Kano...idan ba mu waiwayi al'ummarmu mun sama wa Kano mafita ba, Allah zai tuhume mu. Damuwarmu ita ce ci gaban al'ummar Kano da Najeriya," in ji Sanata Shekarau.
Janyewar Ministan Shari'a daga Takarar Gwamnan jihar Kebbi

Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya janye daga takarar gwamnan Kebbi a zaɓen 2023, kamar yadda mai magana da yawunsa ya tabbatar wa BBC.
Umar Gwandu ya kuma ce Malami na nan kan kujerara ta ministan shari'a saɓanin rahotannin da ke cewa ya yi murabus.
Malami wanda ya ayyana aniyarsa ta takarar gwamna a jihar Kebbi ƙarƙashin jam'iyyar APC, ya janye ne bayan shugaba Buhari ya umarci ministocinsa da ke son takara su yi murabus.
Cire dokar hana fita a Sokoto

Asalin hoton, Nj
Gwamnatin jihar Sakkwato ta sanar da cire dokar hana fita da ta saka a babban birnin jihar a makon jiya bayan wata tarzoma da ta biyo bayan kamen da jami'na tsaro suka yi wa wasu matasan da ake zargi da hannun a kisan wata daliba da ta yi batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
A cikin wata sanarwa, Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya cire dokar ya soma aiki nan take. Sai dai ya ce gwamnati ta haramta duk wani nau'i na maci ko tattaki har sai abin da hali ya yi.
Kalaman Obasanjo kan wanda zai gaji mulkin Najeriya

Asalin hoton, HK
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce Najeriya na bukatar shugabanni masu ɗan taɓin hankali da za su iya mai da kasar kan turba mai dorewa.
Obasanjo ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban Najeriya karkashin jam'iyyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen a Abeokuta, a gidansa da ke Ogun inda gidansa yake.
Ya nuna bacin ransa kan halin da Najeriya ke ciki ba wai kawai koma bayan ba ne gare shi, da kuma wadanda suka damu da Najeriya baki daya.
Tsohon shugaban ya jaddada cewa, Najeriya za ta iya kawo karshen matsalar tsaron da take fama da ita cikin shekara biyu in ta samu shugaban da ya dace wanda kuma yake fatan daukar matakan da suka dace.
Shirin gabatar da Magu gaban kotu

Asalin hoton, Bv
Ministan harkokin 'yan sanda, Mohammed Maigari Dingyadi, ya ce mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu zai gurfana gaban kotu ne kawai idan an kawo rahoton binciken da ake gudanarwa a kan shi da mai shari'a Justice Ayo Salami-led ke jagoranta.
Ya bayyana haka ne a jiya ya yin taron ministoci na mako-mako wanda tawagar 'yada labarai na shugabancin Najeriya a Abuja.
A watan Yulin 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wata tawaga da za ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Magu, biyo bayan koken da Antoni Janar na kasa ya shigar Abubakar Malami.