Yadda za a cika katafariyar Madatsar Ruwan Kogin Nilu

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Damian Zane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Hoton da aka dauka daga tauraron ɗan adam tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yuli ya nuna yadda sabuwar babbar madatsar ruwa da ke kogin Nilu ke ƙara tara ruwa.
Hakan ya fusata Masar da Sudan ganin cewa har yanzu ba a cimma matsaya ba kan yaushe za a cika madatsar ruwan.

Kafafen watsa labarai a ƙasar sun yi bincike bayan rahotanni sun nuna cewa da gan-gan ake cika dam ɗin.
Amma wannan na cusa ra'ayin ƙarya kan cewa cika madatsar ruwan kamar cika kwamin wanka ne - kuma tamkar Ethiopia za ta iya kunna famfo da kashewa a lokacin da take so, ma'ana dai kogin yana hannunta.
Za a iya hana hakan?
A'a. Wurin tara ruwan da ke bayan madatsar ruwan zai cika a lokacin damina, wanda hakan ke farawa a watan Yuni zuwa Satumba.
An bayyana cewa "babu abin da zai hana wurin tara ruwan cika, tun daga ƙasan madatsar ruwan", in ji Dakta Kevin Wheeler a wata hira da BBC, wani da ke bin diddiƙin aikin ginin madatsar ruwan ta Ethiopia wadda aka bayar da kwangilarta kan dala biliyan huɗu tun a 2012.

Kalli yadda madatsar ruwan take a wannan bidiyon
Alastair Leithead da tawagarsa sun je madatsar ruwan ta Blue Nile a 2018 - tun daga Habasha suka ratsa ta udan har zuwa Masar.

Tun da aka fara aikin a 2011, an fara ginin madatsar ruwan a kewayen Kogin Nilu.
Masu ginin sun ci gaba da tsara ginin a gefen kogin ba tare da wata matsala ba. A tsakiya, lokacin bazara, an karkatar da inda ruwan kogin ke wucewa ta hanyar saka kwalbati da butut domin bayar da damar gina ɗaya ɓangaren.
A yanzu an kammala ɓangaren ƙasa daga tsakiya, kuma kogin na tafiya ta hanyar da aka karkatar da ruwan.
A daidai lokacin da aka fara ganin tasirin ruwan damina a madatsar ruwan, yawan ruwan da zai iya wucewa ta hanyoyin da aka samar na kwalbati ya kusan raguwa kan yawan ruwan da zai riƙa shiga madatsar, wanda hakan na nufin ruwan zai ƙara taruwa ya ƙaru a tafkin da zai tsaya a bayan madatsar ruwan, in ji Dakta Wheeler.
Hukumomi a Ethiopia za su iya rufe hanyoyin ruwan domin ƙara yawan ruwan da ke taruwa amma hakan bai zama dole ba, in ji shi.
Mene ne mataki na gaba?
A shekarar farko, madatsar ruwan za ta riƙe kimanin murabba'in mita biliyan 4.9 na ruwa, wanda hakan zai bayar da damar gwajin sabbin injinan samar da wutar lantarki.
Adadin yawan ruwan da ke gudu a Kogin na Nilu ya kai murabba'in mita biliyan 49.
A lokacin bazara, kogin na raguwa kaɗan, domin bayar da dama ga bangon madatsar ruwan ya cika sai kuma a shekarar gaba a samu ƙarin murabba'in mita biliyan 13.5 da za a tara.

Zuwa lokacin, yawan ruwan zai iya kai wa ga kashi na biyu na injinan samar da wuta, wanda hakan ke nufin za a iya lura da yawan ruwan da ke gudana yadda ake so.
Ethiopia ta bayyana cewa zai ɗauke ta shekaru biyar zuwa bakwai kafin ta cika madatsar ruwan zuwa matakin da har zai iya ambaliya wato murabba'in mita biliyan 74. A wannan matakin, tafkin da za a haɗa zai iya kai tsawon kilomita 250.
Tsakanin kowace kaka ta yin ambaliyar ruwa, wurin tara ruwan zai ragu zuwa murabba'in mita biliyan 49.3
Me ya sa Masar ke jin haushi?
Masar, ƙasa ce da za a iya cewa ta dogara kan Kogin Nilu domin samun ruwa, ta damu matuƙa kan cewa tsawon shekarun da aka ɗauka domin tara ruwan, ba ta da garanti kan adadin da za ta samu.

Asalin hoton, Reuters
Zuwa lokacin da madatsar za ta gama cika, Ethiopia ba za ta ji shakkar yanke hukuncin ruwan da za ta rinƙa saki ba idan madatsar ta fara aiki, madatsar za ta zama mafi girma a Afrika da za ta rinƙa samar da wutar lantarki.
Wata matsala da Masar ke shakka ita ce ta ƙarancin ruwan sama da za a iya samu nan gaba da zai iya ɗaukar shekaru da dama ana fama.

