Yadda ƴan Afrika ta kudu suka ƙure adaka a babban taron siyasar ƙasar

Asalin hoton, Esa Alexander / Reuters
- Marubuci, Danai Nesta Kupemba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Ƴan siyasa da mawaƙa, da mashahuran mutane sun ƙure adaka yayin da suka halarci ɗaya daga cikin manyan al'amuran siyasa a Afirka ta Kudu - Jawabin halin da ƙasar ta ke ciki (Sona), wanda ya sa lamarin ya kusan riƙiɗewa zuwa bikin kayan kwalliya daga na siyasa.
Sona wani zaman haɗin gwiwa ne na majalisun dokokin ƙasar biyu a birnin Cape Town domin fara gudanar da ayyukan gwamnati na wannan shekara, inda shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana halin da ƙasar ke ciki tare da bayyana hanyoyin da za a bi domin samun ci gaba.
A cikin jawabin nasa, shugaba Ramaphosa ya yi magana game da juriyar al'ummar ƙasar, inda ya samu yabo a lokacin da ya bayyana cewa, "Ba za a ci zarafin Afirka ta Kudu ba."
Yayin da batun mulki ke kan gaba a taron, Sona ta zama tamkar bikin kayan ado a cikin shekarun da suka gabata, inda ƴan majalisa ke amfani da bikin wajen tallafa wa masu sarrafa tufafi a cikin gida da baje kolin basirar mutanen Afirka ta Kudu.
Tufafin sun kasance abubuwa masu jan hankali a kafafen sada zumunta a kodayaushe, kuma haka ma lamarin ya kasance a wannan shekarar.

Asalin hoton, Nic Bothma / Reuters
Mawaƙiya Inako Mateza, wadda ita ce imbongi ta bana (mawaƙiyar yabo ta gargajiya), ta taka muhimmiyar rawa a ɗaya daga cikin al'adun Sona masu mahimmanci.
Ta hanyar waƙa da rawa, ta ba da labarin tarihin rayuwar Shugaba Cyril Ramaphosa.
Ta ƙammala ta hanyar kiran shugaban da sanannen laƙabinsa wato "Cupcake."

Asalin hoton, Nic Bothma / Reuters
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na Afirka ta Kudu, Pemmy Majodina ta sanya kayan gargajiya da ƴan kunne masu ban sha'awa.
Kayayyakin nata na ƙabilar Xhosa wanda ya ƙware a sana'ar ɗinki, Zoleka Vicky Magwaca, daga Cibiyar fasaha ta Mthatha a Gabashin Cape ce ta sarrafa.
"Na himmatu wajen tallafa wa masu sarrafa tufafi na cikin gida," Majodina ta shaida wa Eye Witness News a wurin bikin.
Ruwa ya kasance wani muhimmin ɓangare na jawabin Ramaphosa, domin ya ce za a zuba jari a wasu ayyukan samar da ruwa don magance ƙarancin da ke addabar ƙasar baki ɗaya.

Asalin hoton, Nic Bothma / Reuters

Asalin hoton, Nic Bothma / Reuters
Sanye da tufafi mai launin zinare, wannan fitaccen mawaƙin Kwaito ne, Gezani Kobane, wanda aka fi sani da Papa Penny. Ɗan jam'iyyar tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma ne, uMkhonto we Sizwe (MK).
Yayin da MK ke tabbatar da kasancewarsa a siyasar Afirka ta Kudu a matsayin babbar jam'iyyar adawa, jiga-jigai kamar Kobane na jan hankali ga matsayinsu na siyasa da salon tufafinsu na musamman.
Sai dai Zuma bai halarci taron ba, yayin da yake fuskantar shari'a da ake yi masa na cin hanci da rashawa da suka jiɓanci wani cinikin makamai. Ya dai musanta aikata wani laifi.

Asalin hoton, Nic Bothma / Reuters

Asalin hoton, Nic Bothma / Reuters
A wajen majalisar, akwai wurin da baƙi da ministoci ke tsayawa domin ɗaukar hotuna.
An gudanar da bikin Sona na bana ne a babban ɗakin taro na birnin Cape Town yayin da ake ci gaba da sake gina zauren majalisar bayan wata gobara da ta tashi a ginin a shekarar 2022.

Asalin hoton, Dwayne Senior / Getty Images
Ministan wasanni Gayton Mckenzie ya ƙurev adaka inda ya sanya baƙaƙen tufafi da kuma tabarau.

Asalin hoton, Rodger Bosch / AFP
, Mwelo Nonkonyana, wanda yanzu ke zama a Majalisar Dattawan shugabannin gargajiya na Afirka ta Kudu a yankin Eastern Cape ya tabbatar da cewa an baje kolin kayan gargajiyarsa.

Asalin hoton, Nic Bothma / Reuters
Jam'iyyar Julius Malema, Economic Freedom Fighters (EFF) ta isa filin bikin sanye da jajayen tufafi.
Jam'iyyar ta kawo cikas ga taron Sona a baya, amma a bana sun zo cikin kwanciyar hankali.
Malema ya bayyana rashin gamsuwarsa da jawabin shugaba Ramaphosa kuma ya shaidawa kafar yaɗa labarai ta cikin gida NCA cewa "maganganu ne na fatar baki kawai".

Asalin hoton, Phando Jikelo / Shutterstock
Lindiwe Ntshalintshali, mataimakiyar ministar ma'aikatar gidajen yari ta yi ado ga yayin da ta sanya wata riga mai launin zinare a yayin da take sauraron jawabin.