Hanyoyi uku na inganta lafiyar ƙwaƙwalwa a lokacin aikin Hajji
Hanyoyi uku na inganta lafiyar ƙwaƙwalwa a lokacin aikin Hajji
Zuwa aikin Hajji wata dama ce babba ga Musulmi, kuma ibada ce da ke buƙatar cikakkiyyar lafiyar ƙwaƙwalwa.
A kan samu wasu matsaloli da suke da alaƙa da lafiyar ƙwaƙwalwa a lokacin gudanar da ibadar.
Wannan ya sa BBC ta gana da ƙwararren likita, wanda ya zayyana wasu hanyoyi uku da mahajjata za su iya inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu.