Hikataya: Labarin Wanda Ya Ƙi Ji 09/02/2025
A filinmu na Hikayata na wannan makon mun kawo muku labarain 'Wanda Ya Ƙi Ji' da Jamila Lawal Zango ta rubuta.
Jamila ta gina labarinta kan wata mata da ta biye wa son zuciya da makauniyar soyayyar da take yi wa saurayinta ta kuma aure shi duk kuwa da gwajin likitoci ya tabbatar musu cewa za su iya haifar yara masu ɗaukar da cutar amosanin jini wato sikila.
Daga ƙarshe matar da tsinci talatarta a labara bayan da ta haifi 'ya'ya masu dauke da lalurar cutar, inda mijin nata ya gaji da ɗawainiyarsu ƙarshe ya gudu ya bar ta da su.
Aisha Shariff Bappa ta BBC ce ta karanta labarin.