An gano yadda ake hada baki da 'yan Najeriya ana hirar jima'i don cin kuɗin Turawa
Daga Nduka Orjinmo BBC News, Abuja

Asalin hoton, IEROMIN
Abokin hulɗar, mutum ne ɗan shekara 50 mazaunin Amurka, kuma sunan zankaɗeɗiyar matashiyar farar fatar da yake hira da ita ta intanet Gingerhoney, mai tallar tufafin ƙwalisa ce wadda hoton da ke shafinta na sada zumunta ya nuna ta yi kwanciyar ruf-da-ciki a kan gado. Abokin hulɗar ya ɗauka cewa Gingerhoney na zaune ne a kusa, bai san cewa ita, wani gardi ne da ke can nesa a Najeriya ba.
Maza a faɗin duniya, kamar wannan, na biyan ɗaruruwan daloli a shafukan batsa don yin hira da abin da suke ɗauka 'yan mata ne zankaɗa-zankaɗa, amma a haƙiƙanin gaskiya suna iya zama kowanne irin ƙato gama-gari, kamar yadda BBC ta gano.
A tsawon watanni da aka kwashe ana tattara shaidu an bankaɗo cewa wannan lamari da ya karaɗe shafukan jabu, yana kamawa daga Netherlands zuwa Amurka da ƙasar Suriname zuwa Najeriya kuma akwai yiwuwar suna karya tsauraran dokoki na harkar batsa a dijital.
Wani ɗalibin jami'a a Najeriya, Abiodun (ba sunansa na gaskiya ba ne) na ɗaya daga cikin masu shafin sada zumunta da yawa waɗanda ke kula da shafukan bogi a dandalin soyayya na intanet mallakar kamfanin Meteor Interactive BV na ƙasar Netherlands.
Abiodun yana caccanza hotuna a tsakanin gomman shafukan jabu da yake kula da su, amma kowanne lokaci yana ƙaryar gabatar da kansa a matsayin wata zankaɗeɗiyar matashiya farar fata.
A ɗaya daga cikinsu shi ne na Gingerhoney, wata mai tallar tufafin kwalisa 'yar shekara 21 sanye da rigar shiga wanka ruwan hoda, ta tsuke kugunta mai ɗaurin kalangu.
Tana jin kanta da cewa, in dai zaƙin ɗanɗano ake nema to idan mutum ya wuce ta, sai dai fa ya nemi zuma, don haka ta ce a kira ta da sunan Citta - "kalar gashin kaina".
Gefe ɗaya a kwamfyutar Abiodun wata jaka ce mai ƙunshe da hotunan batsa iri daban-daban na Gingerhoney, ko da wani abokin hulɗar zai nemi ƙarin hotuna masu motsa sha'awa. Hotunan sun ƙunshi irin wanda ake wallafawa a fuskar shafin sada zumunta da ɗumbin wasu da aka samo daga hanyoyi iri daban-daban.
Ba Abiodun ne kawai yake da hanyar shiga shafin Gingerhoney ba - gomman sauran masu kula da hirarrakin na kula da shafinta na bogi ba dare ba rana, a lokacin aikinsu.
Masu kula da hirar soyayyar kamar Abiodun na amfani da wata manhajar ingantacciyar taswira domin dasa inda Gingerhoney take na ƙarya a da'irar kilomita 50 na wani abokin hulɗa, abin da ya sa ma ake haɗa su kenan. Abokin hulɗar ya biya kuɗi don yin wannan hira kuma duk da yake bai furta ba amma yana fatan wata rana za su gamu ido-da-ido.
Ko da yake, kyauta ne shiga irin wannan dandali, abokan hulɗa na biyan kuɗi lokaci-lokaci gwargwadon tsarin soyayyar da suka yi rijista, wanda ke kamawa daga $6 (N4,300) zuwa $300 (N215,000), don karɓa ko aika saƙonnin soyayya ga "mata".

Yayin da abokan hulɗa matasa ke son gamuwa ƙiri-ƙiri da matan da suke jin suna kusa da inda suke, tsoffin abokan hulɗa sau da yawa sukan gamsu ma da hirarrakin batsa kawai, da hotuna da bidiyon motsa sha'awa, in ji Abiodun.
Manufar Abiodun da saura masu kula da hirar soyayya ita ce su riƙe irin waɗannan masu biyan kuɗi a dandalin tsawon lokaci har sai sun ciye musu kuɗi.
Ana umartar masu kula da hirarrakin cewa dole ne sai saƙo ya kai yawan a ƙalla harafi 150 kuma ya kasance wanda zai ja dogon zance don a daɗe ana hira.
"Aiki ne kamar na yi wa mai sayen haja hidima, abokin hulɗa kawai ya ji tamkar yana hira da wata hamshaƙiya," Abiodun ya fada wa BBC.
Kamfanin Meteor Interactive BV na amfani da wani kamfanin kwangila a ƙasar Suriname - mai suna Logical Moderation Solutions (LMS), wanda wani mutum ɗan ƙasar Suriname mai suna Orano Rose ya kafa, don ɗaukar ma'aikata da horar da su, da kuma raba aiki ga 'yan Najeriya masu kula da hirar soyayya.
BBC ta ga shaida a shafukan kamfanin LMS na dandalin WhatsApp da Telegram da Skype da ke bayyana cewa ya ɗauki ɗaruruwan masu kula da hirar soyaya tare da horar da su, akasari a biranen Najeria na Lagos da Abuja.
An tallata ayyukan masu kula da hirar soyayyar a dandalin Instagram da Twitter da Telegram, ga ɗumbin marasa aikin yi a Najeriya da matasa masu ilmi don riƙe wani "matsayin aiki a intanet" da "harkokin kasuwanci na dijital" da "matsayin mai kula da hira", ba tare da an ambaci wata harkar sheƙe aya da ma'aikaci zai tunkara ba.
Daya daga cikin manyan masu ɗaukar ma'aikata a kamfanin LMS, ita ce Adedamola Yusuf, mazaunin Jamus, tana riƙe da aikin tallace-tallace a shafukan sada zumunta, inda take rayuwar kece-raini da ƙasaita a hamshaƙan wuraren buɗe ido.
"Kana hira da fararen fata masu gundura. Aikin gaba ɗaya yana kan doka kuma muna da lasisi a kasashen Jamus da Najeriya," ta ce yayin zantawa ta kafar WhatsApp da mutanen da take yiwuwar ɗauka aiki a ranar farko ta tattaunawarsu.
Adedamola Yusuf ta ɗauki masu kula da hirar soyayya aiki a tsawon sama da shekara biyu kuma a wani lokacin ɗaukar ma'aikata cikin watan Nuwamban bara, ɗaruruwan mutane ne suka nemi aikin.
Ta ƙi yarda ta mai da martani lokacin da BBC ta nemi jin bahasinta.
"Mutane daga ƙasashen Yamma akasari suna son hira," in ji wani mai horar da sabbin ma'aikata. Sai sun ci jarrabawar Ingilishi mai tsauri don kada a yi saurin gane salon wannan damfara.
"Cewa ake yi: 'I am', ba 'am' ba," nan ana yi wa ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗauka aiki gyara ne lokacin wani taron horarwa da aka shirya a zauren kamfanin na Whatsapp, wanda ni ma na halarta.
Nicholas Akande, darakta a kamfanin LMS a Najeriya ya yi rijista ga mutane fiye da 100 a makon farko na watan Yuli don ɗaukar su aikin kula da hirar soyayya inda ya shaida musu cewa aikin da za su yi bai saɓa wa doka ba.
Bai amsa tambayoyin da muka yi masa ba lokacin da muka nemi jin bahasi daga gare shi.

Asalin hoton, Nicholas Akande/Instagram
Ana horar da masu kula da hirar soyayya kan al'adu da salon rubuce-rubuce da hirarrakin da ake yayi a garin da abokan harkarsu suke, ta yadda za a fi gaskata zancensu.
A ƙarshen taron horarwar wanda kan shafe daga tsawon kwanaki har zuwa mako ɗaya, ana ba su jerin adireshin shiga dandalin intanet daban-daban inda za su iya ganin bayanan mutane kamar adireshin gida da lambar wayar tarho da shekarun masu biyan rijista.
BBC ta ga bahasi daga maza a intanet, waɗanda suka ce sun kashe kama daga $300 (N215,000) har zuwa $700 (N504,000) a irin wannan dandali da fatan za a haɗa su da "matan" da suke hirarraki.
"Na aika wa mata kamar 20 sako amma ko da yaushe sai a yi ko oho da ni duk lokacin da na nuna sai mun gamu da juna ƙiri-da-ƙiri," in ji wani mutum wanda ya yi iƙirarin cewa ya kashe kimanin $65 (N47,000) a wani dandali mallakar kamfanin Meteor Interactive.
Wani mutum shi ma ya ce "ya biya kuɗi har $400 (N288,000) da tunanin cewa mata ne da gaske... rashin azancina ne da ba na karanta 'yan ƙananan abubuwan da za su tada musu balli", a cewarsa.
Wani mutum ya ce shi ma ya kashe sama da $300 (216,000) wajen sayen kati a kan ƙaryar cewa za a haɗa shi da mata ƙiri-da-ƙiri.
