Matakan da jam'iyyar NNPP za ta dauka domin shawo kan matsalar tsaro a Sokoto - Sanata Tambuwal

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Dan takarar gwamnan jihar Sokoto a jam'iyyar NNPP, Sanata Umaru Dahiru Tambuwal, ya ce rashin tsaro a jihar tasa na ci masa tuwo a kwarya.

Ya bayyana haka ne a tattaunawa da BBC Hausa.

"Kuma ban gamsu da irin matakan da ake dauka ba. Shi ya sa ni zan fi ba shi muhimmanci idan har Allah ya sa na samu nasara a zaben 2023,"in ji shi.

Sanata Tambuwal ya kara da cewa "zan bai wa matasa muhimmanci kasancewar su ne kashin bayan cigaban kowacce al'umma."