Cigaban mai haka rijiya aka samu a shekaru biyun Tinubu - Buba Galadima

Buba Galadima

Asalin hoton, OTHERS

Jigo a jam'iyyar hamayya ta NNPP, a Najeriya, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa ba wani abin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kawo wa kasar illa cigaban mai haka rijiya.

Dansiyasar yana mayar da martani ga jawabin da shugaban kasar ya yi a ranar Alhamis, 29 ga watan Mayu, 2025, ranar da gwamnatinsa ta cika shekara biyu a kan mulki.

A jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya ce, gwamnatinsa ta samu nasarori da dama musamman a tattalin arziƙin ƙasa da inganta tsaro da rage cin-hanci da rashawa da kuma fitar da ɗumbin al'ummar ƙasar daga talauci, tare da rage dimbin bashin da ake bin Najeriya.

A tattaunawar da Buba Galadiman ya yi da BBC, inda yake martani ga kalaman shugaban, na cewa gwamnatinsa ta samar da cigaba ta fannoni da dama.

''Mu ba mu ga komai ba – mun ga cibaya domin abin da naira goma za ta saya ma a da yau naira dubu ma ba za ta iya saya maka ba,'' in ji jigon na NNPP.

Ya ce, idan aka yi waiwaye a baya darajar naira a kan dala za a ga cibayan a zahiri, kasancewar a yanzu dala daya tana daidai da naira 1650.

Ya kara da cewa : ''Idan gwamnati ta ce tattalin arzikin kasar ya habaka, dala ta zama naira 1650, shin naira 1650 me za ta iya saya maka? Wannan ita ce magana.''

Dangane da farashin kayan abinci da gwamnatin ke cewa ya sauko, wanda take alfahari da hakan a matsayin cigaban da zai saukaka wa talaka rayuwa, dansiyasar ya ce wannan ma ba abu ne da za a yi murna da shi ba.

Ya ce: ''Ka san kowa da nashi ilimin, na yarda da maganar gwamnati cewa farashin abinci – shinkafa, alkama, masara ya yui kasa. Amma kai ka san abin da zai biyo baya"Aya al-Skafi zaune tana kallon kyamara idonta cike da ƙwalla, sanye da baƙaƙen tufafi da hijabi. " loading="lazy" width="3613" height="2032" style="aspect-ratio:3613 / 2032" class="bbc-139onq"/>