'Dole a tilasta wa iyaye shigar da 'ya'yansu nakasassu makaranta'
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wani Malamin jami'a makaho dake koyarwa a jami'ar Bayero dake Kano a Najeriya ya ce dole ne hukumomi su tilastawa iyaye da ke da yara masu nakasa su shigar da su makaranta. Farfesa Jibrin Isa mai lalurar gani ya ce zamani ya sauya kuma barin yara makafi da guragu da kurame suyi ta bara a kan titi ba alkhairi ba ne. Farfesa Jibrin wanda ya yi karatu mai zurfi a fannin masu bukata ta musamman ya fara karatu ne daga matakin Furamare har ya kai ga digiri na uku sannan ya zama Farfesa. Malamin jami'ar ya bukaci hukumomi su tallafa domin shigar da yara nakasassu dake gararamba a kan titi. "Dole ne gwamnati da kuma iyaye su fahimci muhimmancin karatu ga yara masu nakasa". Ya kara da cewa idan har iyaye suka baiwa 'ya'yansu kwarin gwiwa babu shakka za su samu ingantaccen karatu fiye da wanda yayi. Da ya ke bada labari kan karatunsa, Farfesa Jibrin ya ce boko ta kai shi har Jami'ar Birmingham da ke Burtaniya.