Gane Mini Hanya : Shirin Hajjin bana 22/02/2025

Bayanan sautiLatsa hoton sama domin sauraro
Gane Mini Hanya : Shirin Hajjin bana 22/02/2025

Filin Gane Mini hanya na wannan makon ya tattauna ne a kan taƙaddamar da ake yi tsakanin hukumar aikin Hajji ta Najeriya da wani kamfani na Saudiyya, tare kuma da irin shirye-shiryen da hukumar ke yi game da aikin Hajjin da ke tafe.

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON, ta ce tana tattaunawa da kamfanin nan na Saudiyya da ya yi barazanar kai ta ƙara a kotun kasa-da-kasa kan zargin cewa hukumar ta saɓa ƙa'idojin yarjejeniyar da suka yi da shi.

A farkon wannan makon ne kamfanin mai suna Mashariq Al Dhahabiah ya miƙa wata wasiƙa a ofishin hukumar, aikin Hajjin ta Najeriya, da ke Makkah yana zarginta da saɓa yarjejeniyar da suka yi cewa shi ne kawai zai yi wa mahajjatan Najeriya hidima a hajjin bana.

To Amma a hirarsu da Haruna Shehu – Tangaza, shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya Farfesa, Abdullahi Saleh Usman Pakistan ya ce zargin ba gaskiya ba ne amma ya fara ne da bayani kan inda hukumar ta kai wajen shirye-shiryen aikin Hajjin na bana.