'Na yi sa'a ban mutu ba' in ji dan wasan Arsenal da aka caka wa wuka

Mari ya koma Monza   daga Arsenal a watan Agusta a matsayin aro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mari ya koma Monza  daga Arsenal a watan Agusta a matsayin aro

Dan wasan bayan Arsenal Pablo Mari ya ce ya yi "sa'a" da za a yi masa tiyata a bayan caka masa bukar da aka yi a wani katafaren kantin zamani a kusa da Milan.

Kafafen yada labarai na kasar sun ce an kashe wani matashi mai karbar kudi mai shekara 30, kuma wasu mutane na daban su biyar sun ji muggan raunuka, a harin da wani mutum ya kai a garin Assago.

Tuni 'yan sanda suka kama mutumin da ake zargi da harin mai shekara 46, wanda aka ce yana da tabin hankali.

"Na yi matukar sa'a a yau, saboda a gabana mutum ya mutu," in ji Mari da ke zaman aro a kungiyar Monza.

Jaridar Gazzetta ta wasanni ta rawaito cewa dan wasan bayan Sifaniyan Mari mai shekara 29 yana zagayawa ne da matarsa da kuma dansa lokacin da aka caka masa wukar a bayansa.

"Ba wani gwarzo ba ne ni. Ban yi wani abu ba na musamman,"kamar yadda wani mutum dan shekara 51 ya bayyana wa jaridar.

Wakilin Mari Arturo Canales ya ce raunin da aka ji masa ba wani mai tayar da hankali ba ne, kamar yadda ya shaida wa BBC a ranar Alhamis.

Ya ce dan wasan na cikin hayyacinsa kuma babu wata gaba mai muhimmanci a jikinsa da ta jikkata.

Za a yi wa Mari tiyata a ranar Juma'a saboda raunin da aka ji masa.