Yadda ƙasashen yamma ke hukunta dakarun Hisbah na Iran

Asalin hoton, Reuters
Ƙasashen yamma na tsananta dokoki kan hukumomin ƙasar Iran, daidai lokacin da zanga-zanga ke ci gaba da yaɗuwa a faɗin ƙasar.
Ciki har da dakarun tabbatar da ɗa'a na ƙasar waɗanda ake matuƙar tsoron su, waɗanda suka yi ƙaurin suna bayan da wata matashiya mai suna Mahsa Amini ta rasu a lokacin da take tsare a hannunsu.
Su wane ne dakarun Hisbah na Iran?
Dakarun Hisbah na Iran waɗanda a baya ake kiran su 'Gasht-e Ershad', wani ɓangare ne na dakarun ƴansandan ƙasar waɗanda aka ɗora masu alhakin tabbatar da dokar kiyaye al'adun al'ummar Iran, ciki har da yadda al'umma ke sanya tufafi.
Babu cikakken bayani kan yawan dakarun da ke aiki a ɓangaren, to amma gwamnati ta mallaka masu makamai, sannan suna da wuraren tsare mutane, da kuma wuraren da ake kira cibiyoyin sake ilimantar da al'umma.
Dakarun tabbatar da ɗa'a na da ikon tsare mace idan suka ga ba ta sanya hijabi, ko rufe gashinta yadda ya kamata ba.
A cibiyoyin sake ilimantar da al'umma ana bai wa waɗanda aka tsare darussa kan amfanin hijabi, sannan kafin a saki mutum sai ya sanya hannu kan takardar cewa zai yi biyayya ga dokokin sanya kaya na ƙasar.
Yawancin matan ƙasar kan yi yunƙurin turje wa kamen na ƴan hizba, dalilin haka ne ya sa a wasu lokutan ake amfani da ƙarfi wurin kama su.

Kamen da aka yi wa Mahsa Amini a ranar 13 ga watan Satumba a birnin Tehran (ta mutu bayan kwana uku) saboda rashin sanya hijabi yadda ya kamata, shi ne na baya-baya makamancinsa.
Wasu rahotanni sun ce ƴan hizban sun doke ta da katako a kai, sannan suka buga mata kai a jikin motarsu.
Sai dai hukumomi sun ɗora alhakin mutuwarta a kan rashin lafiyar da take ɗauke da ita tun fil'azal, wani abu da iyalanta suka musa.
Wane tasiri takunkuman ƙasashen yamma za su yi?
Da alama takunkuman da ƙasashen yamma ke sawa za su fi tasiri ne a kan al'ummar Iran da ke da niyyar shiga aikin hizban.
Wasu suna shiga aikin ne ba domin sun aminta da dacewar aikin ba, sai dai domin albashin da za su samu. Wasu ma ana tilasta masu ne a matsayin shirin yi wa ƙasa hidima na wajibi.
Ƙaƙaba takunkumi zai iya yin illa ga yawan masu shiga aikin.
Sai dai ƙoƙarin ƙasashen yamma na ƙaƙaba wa hukumomi kamar na hizba da gidanjen yari takunkumai, ana ganin da wuya ya sauya yadda ƙasar ke tafiyar da lamurranta.
Wasu na ganin gara a ɗauki matakai na siyasa da za su tursasa wa Iran ɗin su daina tsarewa ko kisan al'ummar ƙasar.
Wasu kuma na ganin sanya takunkumai kan ɗaiɗaikun mutane ba zai yi amfani ba, kasancewar da dama daga cikin waɗanda abin kan shafa ba su da wasu kadarori a ƙasashen Turai da za a iya ƙwacewa.
Su wane ne ke aikin murƙushe zanga-zangar?
A tsawon mako biyar da suka gabata, dubban iraniyawa sun hau kan tituna a sama da birane 100 na ƙasar domin nuna adawarsu da gwamnati.
Bidiyoyin da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jami'an tsaro suka rinƙa amfani da alburusai a kan masu zanga-zanga, da cin zarafin su ta hanyar bugu ko kuma lalata.

Asalin hoton, Rex Features
Wata ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Iran da ke da ofishinta a birnin Oslo ta ce aƙalla mutum 234 ne aka kashe sanadiyyar zanga-zangar, ciki har da yara 29.
Sai dai ana da yaƙinin cewar ainihin yawan waɗanda aka kashen ya zarce haka.
Hukumar kare haƙƙin bil'adama ta Iranm ta yi ƙiyasin cewa mutum 13,309 aka tsare, mafi yawan su kuma samari ne da kuma ƙananan yara.
Hukumomin tsaro daban-daban na gwamnatin ƙasar ne bidiyoyin da aka wallafa suka nuno su suna ƙoƙarin murƙushe masu zanga-zanga, cikin su akwai ɓangarori daban-daban na rundunar ƴan sandan ƙasar, kamar dakaru na musamman da ake wa laƙabi da 'Naja', da 'Nopo', da kuma na dakarun juyin-juya-hali na ƙasar, da kuma jami'an tsaro na farin kaya.
Su wane ne aka sanya wa takunkumi?
Ofishin kula da harkokin waje da na kasashe renon Ingila, na Birtaniya ya ce an ƙaƙaba takunkumi a kan shugaban hukumar hisba ta Iran Mohammad Rostami Cheshmeh Gachi, da shugaban hukumar reshen Tehran, Haj Ahmad Mirzaei a sanadiyyar mutuwar Mahsa Amini.
An kuma ƙaƙaba wasu takunkuman a kan wasu mayan jami'an tsaron ƙasar bisa zargin su da taka haƙƙin bil'adama.
Ita kuwa tarayyar turai ta ce ta ƙaƙaba takunkumai a kan wasu mutane 11 baya ga dakarun hisba na ƙasar ta Iran.
Ita ma Canada ta sanya takunkumai a kan wasu hukumomin ƙasar ta Iran.
Bankin Amurka kuma ya sanya takunkumi a kan jagororin hukumomin tsaron ƙasar guda bakwai, ciki har da hukumar hisba ta ƙasar, da ma'aikatar tattara bayanan sirri da na tsaro, da dakarun ƙasa na ƙasar da sauran su.
A nata martanin, Iran ta sanar da sanya takunkumai a kan hukumomin Birtaniya da dama, waɗanda ta zarga da ingiza masu zanga-zanga da kuma goyon bayan ta'addanci.
Takunkuman da Iran ɗin ta sanya sun haɗa da haramcin bayar da izinin shiga ƙasar, da ƙwace wasu kadarori da ke ƙasar.
Waɗanda Iran ɗin ta sanya wa takukuman sun haɗa da cibiyar sadarwa ta Birtaniya, da sashin BBC na Persia, da kafar talabijin ta Iran International TV, da ƙaramin ministan tsaro na Birtaniya Tom Tugendhat.