'Yadda cunkoson mutum 500 a aji ya hana ni karatu a Najeriya'
Wannan labari yana cikin jerin labaran da BBC Hausa za ta gabatar bayan neman jin ra'ayoyin ƴan Najeriya a manyan fannonin da suka fi shafi 'yan kasar.
Wannan shiri ne na musamman da BBC ta tsara dangane da shirin manyan zaɓukan da ƙasar za ta gudanar daga watan Fabrairun 2023.
Fannonin da za a yi duba a kai din su ne na tsaro da ilimi da tattalin arziki da lafiya da kuma cin hanci.
Daruruwan mutane ne suka aiko da labaransu, kuma za mu wallafa 25 ne kawai, ɗaya a kowace rana daga 10 ga Oktoban 2022.

Asalin hoton, Naziru Usman Abubkar
Cunkoson dalibai kusan sama da mutum 500 ya hana wani matashi dan Najeriya mai suna Naziru Usman Abubakar, ci gaba da karatunsa, tun a ranar farko da ya fara zuwa makaranta, inda daga baya ya yanke shawarar tafiya Turai.
Wannan dai shi ne halin da makarantu da dama ke ciki a Najeriya, kama daga makarantun sakandire zuwa wasu makaratun gaba da sakandire, inda za a ga wasu daliban suna karbar darasi ta taga sakamakon yawan dalibai a cikin aji.
Naziru ya ce bayan kammala karatunsa na sakandire a shekarar 2011, sai ya samu gurbin karatu a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, inda ya samu gurbin karatu a fannin, harshen Hausa da ilimin addinin Musulunci.
To sai dai tun a ranar farko da ya fara halartar makarantar, ya yanke shawarar hakura da karatun sakamakon irin yanayin da ya samu kansa a ciki lokacin daukar darasinsa na farko a makarantar.
Ya kara da cewa ajin wanda bai kamata a ce akwai mutum sama da 200 ba amma waɗanda suka halarci ajin a wannan ranar sun haura mutum 500.
Matsalolin da cunkoson aji ke janyowa

Asalin hoton, Oreinted daily
Hakika a aji irin wannan, dole a samu matsaloli masu dimbin yawa, kamar yadda Naziru ya shaida mana "matsalolin sun hada da zafi da rashin wadatacciyar iska da hamami da rashin jiyo abin da malami ke faɗa sakamakon rashin na'urar amsa kuwwa.
Wasu matsalolin da ke addabar harkar koyo da koyarwa a Najeriya
Baya ga wadannan matsaloli, akwai wasu matsaloli da dama da ke ci wa bangaren ilimi tuwo a kwarya a Najeriya kamar yadda binciken BBC Hausa ya gano.
Sun hada da rashin kyawun yanayin azuzuwan karatu, inda a wasu lokutan ruwan sama da ke sauka da damuna ke hana dalibai karatu a azuzuwan.
Ga batun karancin kayan aikin koyo da koyarwa, da rashin sabunta manhajar karatu a kan lokaci, inda za a samu malami yana koyar da abu guda tun fiye da shakara goma ba tare da samun sauyi ko karin wani abu ba.
Ga kuma uwa uba batun yajin aikin malamai, da ma’aikatan manyan makarantun kasar.
Alal misali a yanzu haka kungiyar malaman jami’o’i ta kasar na cikin wata na takwas da fara yajin aiki a kasar, sakamakon gaza biya mata wasu bukatunta daga bangaren gwamnatin tarayya.
Wadannan dalilai na daga cikin dalilan da ke tilasta wa wasu iyaye masu ido da kwalli tura ‘ya’yansu zuwa kasashen Turai da ma wasu kasashen na Afirka, domin samun damar kammala karatunsu ba tare da fuskantar matsala ba.
Cunkoson dalibai na kusan sama da mutum 500, da sauran matsalolin da Naziru ya lissafa sun tilasta masa hakura da karutun.
Saboda a cewarsa "Idan mutum karatu yake son yi, ya samu ilimi ba kwali kadai ba, to tabbas ba zai iya karatu a cikin wancan yanayin ba."
Wannan dalilin ne ya sa Naziru ya hakura da karatun kacokan, inda ya ce ya shiga zuwa wasu jihohin kasar domin neman abin da zai rufa wa kansa asiri, irin su Bauchi da Adamawa inda ya fara sana’ar bugu da rini.
Me ya kai shi Turai, karatu ko sana'a?

Asalin hoton, Naziru Usman Abubkar
Naziru ya ce makasudin zuwansa Turai shi ne tasirin abokai wadanda ya hadu da su a wajen yawonsa na neman abin rufin asiri.
''Lokacin da na fito daga gida ba ni da niyyar zuwa Turai, to amma kaddara ta turo ni zuwa nan, na biyo ta Nijar ta Algeriya, inda na hadu da wani abokina dan Saliyo lokacin ya dawo daga kasar Moroko, yana kuma shirin tafiya Turai ta hanyar Libya’’, in ji shi.
Ya kara da cewa a lokacin da ya je Turai (Italiya) ya fara aiki ne domin neman kudi, to amma daga baya sai ya yi tunanin fadada karatunsa a Italiya, kasancewar dama duk inda yake zuwa yana tafiya ne da takardunsa na makaranta, ko da Allah zai sa ya samu damar fadada karatunsa.
Ya ce ''na nemi gurbin karatu a jami’o’i biyu a Italiya kuma duka sun ba ni gurbin karatu.
"Daga nan na zabi daya a cikinsu, wacce ita ce jami’ar birnin Turin a shekarar 2020 inda nake karanta fannin shari’a kuma yanzu haka ina ajin karshe'', in ji ɗalibin.
Yaya yanayin karatu yake a Italiya?
A cewar Dalibin yanayin karatu a Turai yana da matukar kyau, saboda akwai muhallin karatu mai kyau da wadatattun malamai.
"Kuma idan dalibi bai fahimci karatun da aka yi masa a aji ba, to yana da damar saka lokaci domin samun malamin, domin yi masa karin bayani shi kadai, a wani wuri na musamman don ya fahimci karatun yadda ya kamata.@
Kwatanta yanayin karatu a Italiya da Najeriya

Asalin hoton, Naziru Usman Abubkar
''Yanayin karatu tsakanin Italiya da Najeriya ba zai zama daya ba, domin kuwa a nan akwai wadatattun kayan aikin koyo da koyarwa misali ta bangeren sauraron abin da malami yake fada kowa yana ji saboda akwai amsa kuwa ta zayage ko ina''.
''Sannan kuma ta bangaren karatu iya abin da ake so ka koya shi kadai ake koyar da kai, sabanin a Najeriya inda za ka ga ana aro wasu kwasa-kwasai daga wasu bangarorin, a yi ta wahalar da dalibai'', in ji Naziru.
'Dole gwamnatin Najeriya ta zuba kudade don inganta harkokin ilimi'

Asalin hoton, Naziru Usman Abubkar
Naziru ya ce idan har ana so a yi wa fannin ilimi garanbawul to dole gwamnatin Najeriya ta sanya makudan kudade a bunasa fannin.
Manyan hukumomin duniya irin su Unicef sun daɗe suna kiga ga ƙasashen Afirka ciki har da Najeriya da su ƙara ƙaimi wajen ware kuɗaɗe masu yawa ga fannin ilimi a kasafin kudin ƙasar.
Sai dai ga alama gwamnatocin ba su shirya hakan ba. A misali, daga cikin naira tiriliyan 17.13. na kasafin kudin Najeriyar na shekarar 2022, naira biliyan 742.5 kawai aka ware wa fannin ilimi.
Hakan ya kama kashi 5.6 cikin 100 kenan na jumullar kasafin kudin, kuma shi ne mafi karanci tun shekearar 2011.
Sannan Naziru yana ganin "ya kamata gwamnati ta samar wa wadannan makarantun masana’antu, inda za a rika daukar daliban da aka yaye a don yin aiki a masana’antun ta yadda makarantun za su rike kansu ta hanyar samun kudin shiga.
"Duk wasu wurare masu mihummanci kamar wuraren tarihi da asibitoci, da sauransu gwamnatin ta miƙa wa makarantu su, domin su riƙa samar wa kansu kudaden shiga.
"Kamar yadda ake yi nan Italiya makaranta ita take samar wa kanta kudi, abin da yake shigowa ta hannun gwamnati ba wani abu ne mai yawa ba," in ji Naziru.
Ya ƙara da cewa "a nan sai ka ga makaranta tana da kamfanoni da wasu abubuwa da suke domin samar wa kansu kudi."