Yadda za ku shiga gasar BBC ta ƙwararren ɗanjarida ta Komla Dumor, 2024

Komla Dumor

BBC na neman sabon tauraron aikin jarida a Afirka wanda zai lashe lambar yabo ta Komla Dumor, wanda aka buɗe a karo na tara.

Ana gayyatar ƴan jarida daga sassa daban-daban na Afirka domin shiga neman lashe lambar yabon, wanda ke da nufin ganowa da kuma bunƙasa sabbin haziƙai daga nahiyar.

Wanda ya lashe kyautar zai shafe watanni uku a babban ofishin BBC da ke Landan, inda zai samu ƙwarewa da gogewa.

Za a rufe karɓar shiga gasar a ranar 15 ga watan Maris 2024 da ƙarfe 23:59 GMT.

An samar da lambar yabon ne domin karrama Komla Dumor, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye na BBC ɗan asalin ƙasar Ghana, wanda ya rasu yana da shekara 41, shekaru goma da suka gabata.

Matar Dumor, Kwansema Dumor, ta ce tana alfahari da irin tasirin da mijinta ya yi a kafar yaɗa labaru ta BBC, ta kuma ce ƴan'uwanta sun yi godiya ga BBC da ta tuna da shi ta hanyar kyautar.

BBC na ƙarfafa gwiwar ƴan jarida a faɗin Afirka da su shiga gasar, wadda ke neman bunƙasa da kuma karrama fitattun ƴan jarida da ke rayuwa tare da aiki a nahiyar.

Baya ga samun horo, ɗan jaridar da ya yi nasarar lashe kyautar zai samu damar tafiya wata ƙasa a Afirka don bayar da rahoto kan wani labari, wanda za a yaɗa a BBC ga masu bibiyar ta a faɗin duniya.

Shahararren ɗan jarida mai fafutuka, da kuzari, na da jajircewa wurin bayar da sahihan rahotonni kan labaran Afirka baki ɗaya, Dumor ya yi matuƙar tasiri a Afirka da sauran ƙasashen duniya.

BBC ta ƙuduri aniyar ci gaba da tunawa da shi ta hanyar bai wa ƴan jarida daga Afirka damar bayar da labarai daga Afirka don isa ga masu sauraro da ke faɗin duniya.

Mai gabatar da labarai Paa Kwesi Asare da asalin ƙasar Ghana shi ne ya lashe gasar a bara - wanda ya fito daga ƙasa ɗaya da marigayi Komla Dumor.

A lokacin da aka aike da shi ya je ƙasar Kenya ne domin bayar da rahoto kan yadda ake yunƙurin mayar da motocin tasi na "boda boda" na ƙasar masu amfani da wutar lantarki, maimakon man fetur ko man Gas.

Liliane Landor, babbar jami’ar kula da Sashen ƙasa da ƙasa ta BBC ta ce: “Mun yi farin ciki da irin hazaƙa da aka samu, sakamakon kyautar da aka ƙaddamar da sunan Komla.

"Ta hanyar ayyukan da ya gudanar muna so mu ci gaba da haɓaka aikin jarida a Afirka."

Dumor ya kasance mai gabatar da shirin Focus on Africa, shirin labarai na gidan talabijin na BBC na farko da ake yaɗa shi a kullum cikin harshen Ingilishi ga masu sauraro a Afirka. An watsa shi a tashar Labaran Duniya na BBC, wanda a shekarar da ta gabata ya haɗe da tashar yaɗa labarai ta BBC don samar da labaran talabijin na tsawon sa'o'i 24.

Ya kuma kasance ɗaya daga cikin jagororin masu gabatar da shirye-shirye na shirin safe na Turai a BBC.

Ya fara aiki a BBC ne a shekara ta 2007 bayan ya shafe shekaru goma yana aikin jarida a ƙasarsa Ghana inda ya lashe kyautar gwarzon ɗan jarida na Ghana.

A tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009 ya gabatar da shirin 'Network Africa' a sashen ƙasa da ƙasa na BBC, kafin ya shiga shirin 'The World Today'.

A shekarar 2009 Dumor ya zama mai gabatar da labaran kasuwanci na Afirka na farko a shirin Labaran Duniya na BBC, Mai suna 'Africa Business Report'. Ya karaɗe nahiyar Afirka, inda ya gana da manyan ƴan kasuwar nahiyar, ya kuma bayar da rahotanni kan sabbin hanyoyin kasuwanci a Afrika.

A shekarar 2013 mujallar New African ta sanya Dumor a cikin jerin ƴan Afirka 100 wanda suka fi tasiri a nahiyar.

Waɗanda suka lashe kyautar a baya

2023: Paa Kwesi Asare daga Ghana

2022: Dingindaba Jonah Buyoya daga Zambia

2020: Victoria Rubadiri daga Kenya

2019: Solomon Serwanjja daga Uganda

2018: Waihiga Mwaura daga Kenya

2017: Amina Yuguda daga Nigeria

2016: Didi Akinyelure daga Nigeria

2015: Nancy Kacungira daga Uganda