Ra'ayi Riga: Kan sake nazarin ƙudirin dokar haraji 06/12/2024

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Ra'ayi Riga: Kan sake nazarin ƙudirin dokar haraji 06/12/2024

Shirin Ra'ayi Riga na wannan mako ya tattauna batun ƙudirin dokar haraji da ya janyo taƙaddama a Najeriya.

A ranar Laraba ne Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da jingine aiki kan ƙudirin dokokin haraji na ƙasar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya gabatar mata.

Majalisar ta kuma sanar da kafa wani kwamati da zai yi aikin dubawa da kuma gyara sassan dokar da ke jawo taƙaddama, musamman daga yankin arewacin ƙasar.

Bayan haka ne kuma Shugaba Tinubu ya umarci ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta yi aiki tare da majalisar dokokin domin samun masalaha kan wasu ɓangarori na dokar da ake taƙaddama a kai.

Tattaunawa kan ƙudurin ta janyo zazzafar muhawara a faɗin Najeriya, yayin da wasu ɓangarorin ƙasar suka yi zargin cewa an cusa wasu abubuwa da za su cutar da wasu sassa.

Me ya janyo taƙaddama game da wannan ƙudiri?

Ina makomar zargin da ake yi na kassara wani ɓangare na ƙasar?

Wace hanya za a bi domin warware dambarwar da ta biyo bayan gabatar da ƙudirin?

Wasu daga cikin batutuwan da shirin ya tattauna a kansu kenan.