Me ya sa ake samun yawan mace-macen aure a arewacin Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Mutuwar ɗaya ne daga cikin manyan matsalolin da ke ci wa yankin arewacin Najeriya tuwo a ƙwarya.
Matsalar ta zama gagaruma da ke shafar mutane da dama, kama daga matan da ake saki, zuwa iyayen matan da ma ƙananan yaran da iyayensu ke rabuwa, sakamakon halin da yaran kan faɗa a wasu lokuta, sakamakon rashin rayuwa da duka iyayensu
Matsalar na ci gaba da ɗaukar hankulan jama'ar yankin, lamarin da ya sa malamai da masana ke ta kiraye-kiraye magance matsalar.
A lokuta da dama malamai da kuma masana kan shirya tarukan lakcoci da rubuce-rubuce kan matsalar da zimmar nemo mafita.
To sai dai har yanzu da alama matsalar na neman gagarar kundila, domin kuwa a kowace rana ƙaruwa take yi.
Ina matsalar take?

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Jamilu Yusuf Zarewa malami a Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma marubucin littafin ''Matsalolin Aure a Ƙasar Hausa'' ya shaida wa BBC wasu daga cikin abubuwan da ke janyo matsalar sakin aure, musamman a arewacin Najeriya.
Ƙarya a neman aure
Malamin Jami'ar ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo matsalar saki, shi ne rashin gina auren a kan doron gaskiya.
Ya ce mafi yawan auren da ake yi a yanzu ana gina su ne bisa doron yaudara da ƙarya.
''A ɓangaren mata wasu sai su ce sai mai kuɗi, to a lokacin da mazan suka gane haka, sai a riƙa zuwar wa matan a sigar yaudara ta fannoni daban-daban''.
''Yanzu akwai inda ake aron mota, da hayar tufafi, kai ta kai har akwai wuraren da ake zuwa domin aro kayan lefe '', in ji shi.
Malamin Jami'ar ya kuma ce a ɓangaren maza kuma akwai masu cewa su dole sai farar mace mai kyau suke so.
''To wannan ya sa wasu matan ke yaudararsu ta wannan fannin. A yanzu yawancin matan da kake ganin a matsayin farare, mafi yawansu ba fararen ba ne, shafe-shafe ne'', in ji malamin jam'iar.
Ya ƙara da cewa galibi bayan auren idan ma'auratan suka gano gaskiyar, sai a riƙa samun matsaloli nan da can.
Buri

Asalin hoton, Reuters
Wani dalilin da ke haifar da mace-macen aure a arewacin Najeriya kamar yadda masanin ya yi bayani, shi ne ɗora buri mai yawa tsakanin ma'auratan.
''Daga ɓangaren matan akwai masu cewa su ba za su auri kowane irin namiji ba, sai mai kuɗi'', in ji shi.
Su ma mazan akwai masu wannan burin, da ke son yin auren jari, ba za su nemi daidai su ba.
Don haka da zarar sun yi aure suka fahimci ba za su iya cimma muradinsu ba, sai ka ga matsaloli sun taro, lamarin da zai kai ga sakin aure.
Sauka daga koyarwar Addini
A addinance akwai abubuwa guda huɗu da Annabi (S.A.W) ya yi bayanin abubuwan da ke sa a auri mace saboda su.
''Annabi ya ce ana auren mace don kyawunta, ko don dukiyarta ko don nasabarta ko don addininta, amma a ƙarshe wadda ya yi umarni a aura ita ce ma'abociyar addini''.
''Amma galibi yanzu masu neman auren ba sa kula da wannan umarni na Annabi, inda suke la'akari da wasu abubuwa marasa muhimmanci, a lokacin neman aurensu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Zama a gidan gado

Asalin hoton, Getty Images
Wata matsalar da ke haddasa mutuwar aure a wannan zamani ita ce zama a gidan gandu, ko gidan gado.
''Galibi iyayenmu ba koyaushe suke kallon ɗawaniyar da miji ke yi wa matarsa a matsayin haƙƙin da ya rataya a wuyansa ba, wani lokacin za a riƙa kallon cewa ka ɗauko wata bare ka zo kana bauta mata'', in ji.
Ya ce daga nan sai dangin miji su riƙa ɓullo da wasu matsaloli tsakaninsu da matar, daga nan sai a riƙa samun matsalolin da za su iya kai wa ga saki.
''A wasu lokutan ma iyayen ne ke sakar wa ƴaƴansu aure, saboda biyayyar iyaye, koda kuwa su ma'auratan suna son junansu,''.
Don haka ne ya shawarci matasa su riƙa mallakar gidansu kafin su yi aure don kauce wa samun wannan matsalar.
Rashin sauke haƙƙi
Wata gagarumar matsalar da ke haddasa mace-macen aure a ƙasar Hausa ita ce rashin sauke haƙƙi, musamman daga ɓangaren miji.
Waasu mazan ba sa sauke nauyin da ke kansu a matsayinsu na jagorori a zaman aure, inda suke sakar wa matan wasu ɓangarori ko duka ɗawainiyar gida da kula da yara.
''Misali a yanzu idan miji ya ga matarsa na aikin gwamnati ko sana'a, sai ya ce zai sakar mata wani ɓangare na kula da gida, wanda kuma asali haƙƙinsa ne'', in ji shi.
Malamin Jami'ar ya ƙara da cewa mace na daraja mijinta sanadiyyar abin da yake kashewa na ɗaukar nauyinta tare da yaranta.
''Don haka duk lokacin da ya zama raba daidai kuke yi da matarka wajen kula da ɗawainiyar gida to raini zai shigo ciki, kuma ba za ka samu daraja yadda ya kamata ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Rashin haƙuri
Zaman aure abu ne da ake ginawa kan tafarkin haƙuri da juna, don haka idan aka kasa samun haƙuri da juna, to dole a samu cikas a zaman aure.
''Babu yadda za ka auri mace kuma ka sameta 100 bisa 100 a kowane fanni, dole ka samu nakasu a wasu fannonin, haka ita ma dole ta samu mijinta da gazawa a wasu fannonin''.
Malamin ya ce lokacin da ake neman aure, ko zuwa zance, kowa zai yi ƙoƙarin fito da mafi alkairin halinsa, to amma bayan aure sai sauran halayen su bayyana. Don haka ne ake buƙatar haƙuri da juriya tsakanin juna.
Rashin gamsuwar saduwa
Wannan shi ne kan gaba wajen abubuwan da ke haifar da sakin aure a cewar masanin zamantakewar auren.
''A mafi yawan lokuta auren da ke mutuwa har a gaban alƙali, shi kansa alƙalin bai sai abin da ya haifar da matsalar ba, saboda abin da ake kawo masa ƙara ba shi ba ne ainihin matsalar ba'', in ji shi.
Malamin ya ce gamsuwa wajen saduwar aure na daga cikin sirrin ɗorewar zaman aure.
''Galibi duk matsalar da mace ke ciki a rayuwar aure, indai tana samun gamsuwa wajen saduwa, to wannan na daga cikin abubuwan da ke toshe matsalolin zamantakewar aure.'', acewarsa.
Rashin adalci
Shi ma wannan ginshiƙi ne daga cikin abubuwan da ke janyo mace-macen aure a ƙasar Hausa, a cewar Dakta Jamilu.
''A ɓangaren maza, za ka samu wani na da mata biyu ko fiye, amma kuma sai sai ka ga rashin adalci ƙarara tsakanin matan nasa''.
Zargi
Shi ma zargi ɗaya babba ne ciki dalilan mutuwar aure musammana arewacin Najeriya.
Akwai ma'aurata da dama da ke zargin junansu da cin amana, wanda kuma ba haka ya kamata rayuwar aure ta ginu a kai ba.
''Akwai mijin da na sani duk mako sai ya bai wa matarsa Al'qur'ani ta rantsa cewa cikin makon ba ta ci amanarsa ba, haka ma akwai matar da duk fitar da mijinta ya yi, idan ya dawo sai ta shinshina shi wai ko ya ci amanarta''.
Rashin iyaye nagari
Iyaye nagari su ne waɗanda suka horar da ƴaƴansu kan hakaye nagari. Don haka idan mutum ya tashi yin aure na daga cikin abubuwan da zai yi la'akari da su.
''Su iyaye nagari an fi tasirantuwa da su, don haka ma'aurata kan kwakwaiyi wasu daga cikin ɗabi'unsu, waɗanda za su taimakesu a wajen zaman aure''.
''A duk lokacin da aka samu saɓani tsakanin ma'aurata, iyaye nagari za su goyi bayan gaskiya ne koda kuwa ba ɗansu ko ƴarsu ba ce mai gaskiyar''.
Tasirin ƙawaye da abokai
Abokai da ƙawaye na daga cikin abubuwan da ke haifar da mutuwar aure musamman a ƙasar Hausa.
''Duk yadda ka samu mace tagari, yana da kayu ka duba yanayin ƙawayen da take abota da su'', kamar yadda Dakta Jamilu ya yi bayani.
Littattafan Soyayya da Fina-finai
Dakta Jamilu ya ce kallon fina-finan Hausa da karanta littattafan soyayya na daga cikin dalilin mace-macen aure a wannan zamani.
''A baya kafin zuwan fina-finan Hausa ɗabi'un kashe miji da tsiwa duk ba a sansu ba tsakanin ma'aurata'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa kallon fina-finan sun taka muhimmiyar rawa wajen sauya ɗabi'un wasu ma'auratan maza da mata.
Mene ne mafita?
Daga ƙarshe Dakta Jamilu ya bayar da shawara ga masu yin aure su riƙa yin aurensu domin Allah, su cire kowane irin buri da ƙarya a neman aurensu, su yi aure domin bautar ubangiji ba domin wata manufa ba.
''Idan an yi aure domin kuɗi, watarana ana iya wayar gari babu kuɗin, haka ma kyau wata rana zai gushe''.
Sannan kuma ya ce idan an yi auren, to ma'aurata su rungumi haƙuri da juriya tsakaninsu.
'"A riƙa kawar da ido kan duk wani abu da aka gani na laifi bayan auren'', in ji shi.