Gane Mini Hanya: Tare da shigaban AMMASCO

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Tare da shigaban AMMASCO

A duk lokacin da aka yi batun masu hannu da shuni a arewacin Najeriya, jihar Kano kan kasance ta farko kasancewar mafi yawancin masu ƙumbar susa kan fito daga Kano, Amma alƙaluma daga hukumomi daban-daban na nuna yadda jihar ke sahun gaba wajen yawan masu fama da talauci.

To sai dai wasu masu hannun da shuni irinsu, Alhaji Mustapha Ado Muhammad, shugaban AMMASCO International Limited, na jihar na cewa suna son sauya irin waɗannan alƙaluma ta hanyar inganta rayuwar matasa da marasa galihu da ke jihar ta Kano.

A hirarsa da BBC Hausa, Alhai Mustapha Ado ya yi bayani masu yawa, amma ya fara ne da bayani dangane da abin da ake nufi da AMMASCO.