Gane Mini Hanya: Tare da Dr Hakeem Baba Ahmad 26/04/2025
A cikin 'yan makwannin da suka gabata ne ɗaya daga cikin hadiman shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sauka daga kujerarsa a dai dai lokacin da ake samun ƙorafi daga wasu 'yan arewacin ƙasar, cewa gwamnatin tarayyar ƙasar ta mayar da su saniyar ware.
Dokta Hakeem Baba Ahmed, wanda ke riƙe da muƙamakin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa kafin ya yi murabus a farkon wannan watan, ya daɗe ana damawa da shi a harkokin mulkin a Najeriya.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Dokta Hakeem Baba Ahmed ya bayyana dalilansa na ajiye muƙamin nasa a fadar shugaban ƙasa.