Babu alamar haske a nan gaba - Matan Afghanistan

- Marubuci, Turpekai Gharanai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Service
- Aiko rahoto daga London
Ga Nadia da Liza da kuma Zala, shekara ukun da taTaliban ta yi a mulkin Afghanistan sun zama masu muni kuma mafiya wahala a rayuwarsu.
A yanzu da suke shekarunsu na 30 a duniya, sun kasance cikin jerin matan da suka samu ilimi da aikin yi a kusan shekara 20 da tunɓuke Taliban da aka yi a 2001.
A tsawon waɗanan shekaru da yawa daga cikin mata sun samu manyan muƙamai a aikin gwmnati. To sai dai a ranar 15 ga watan Agustan 2021 lokacin da Taliban ta yi kukan kura cikin Kabul babban birnin ƙasar ta kuma ƙwace iko da ƙasar, sai ta fara ɓullo da wasu matakan taƙaita wa mata ayyukan yi.
A yanzu Taliban ta haramta wa mata da 'yan mata zuwa makarantun jami'an da na sakandire, kodayake ƙungiyar ta ce matakin na wucin-gadi ne. Haka kuma an haramta wa matan zuwa wuraren shaƙatawa da na motsa jiki.
Ba a haramta musu aiki ba, amma an hana su riƙe mafiya yawan muƙamai a wasu fannonin aikin gwamnati, in banda fannonin ilimi da lafiya.
An cire da yawansu daga muƙamansu a ma'aikatun ƙasar. Matan ba su samun dmarmaki na riƙe manyan muƙamai a aikin gwamnati.
Matan uku - da suka yi karatu mai zurfi -sun ba mu labarinsu, mun kuma canja sunayensu domin kare su.
'Suna na ya zame min barazana'

Nadia, mai shekara 35 - wadda a baya ta riƙe babban buƙami a fannin tattalin arzikin ƙasar - ta ce byan komawar Taliban mulki an hana ta ci gaba da aikinta.
“Ina da albashi na. Ina biya wa kaina duka buƙatun da suka taso min," in ji ta.
"Ina da abokai, kuma muna rayuwa tare. muna gudanr da al'amuranmu tare, mu abincin rana tare , haka ma na dare. Amma a yanzu sai dai na jira ɗan'uwana ko zai samo mana abin da za mu saka a bakin salati, ko kuwa a a. Wannan abu na damuna matuƙa'', in ji ta.
Takan samu 90,000 kuɗin ƙasar, kwatankwacin dala 1,277 a wata, inda take ɗaukar nauyin gidansu mai mutum 15.
A yanzu duka waɗannan mutane sun dogara da ɗan'uwanta da ke aiki da wani kamfani - wanda samunsa ya dogara da yawan aikin da kamfanin ya yi a wata - don ɗaukar nauyinsu.
Nadia kuwa a nata ɓangaren cewa ta yi a baya-bayan nan ta taɓa fitowa ƙarara ba tare da ɓoye fuskarta ko sunanta ba ta yi magana kan 'yancin mata, amma ta ce a yanzu ba za ta iya yin hakan ba, saboda fargaba kan tsaron lafiyarta da na danginta.
Ta ce ta sha rubuta takardun neman aiki. ''Damarmaki taƙaitattu ne ga mata kuma akan samu masu nema da yawa,'' in ji ta. Ta ce a wata takardar da ta rubuta an gaya mata cewa cancantarta ta ma zarta abin da ae buƙata a aikin.
Ta ƙara da cewa ''Ina cikin damuwa. A yanzu abin da kawai ake yi a kullum, shi ne girki. Ba ma na son yin magana da kowa''.
Ta ce idan damuwar ta yi mata yawa, wani lokaci sai ta tafi kan wani dutse don ta ɗan numfasa.
A yanzu Nadia ta ce tana ɓata lokacinta wajen ''tara burukan da ba za ta iya cimma su ba'.
'Ba zan iya bayyana taƙaici da nake ji ba'

“Wani lokaci nakan ji kamar na kulle kaina a ɗaki na yi ta zabga ihu,” in ji Liza, mai shekara 36, tsohuwar malamar jami'a, da ke zaune a lardin arewacin ƙasar.
A watan Disamban 2022, ƙungiyar Taliban ta umarci duka jami'o'in ƙasar su dakatar da ɗalibai mata har zuwa lokacin da gwamnati za ta waiwayi batun. Sannan kuma aka faɗa wa mata daga malaman jamai'a cewa su zauna a gida.
Ba korar Liza daga aiki aa yi ba, to amma an zaftare albashinta daga dala 510 zuwa dala 70. Mijinta bakanike ne, wanda ke samun ƙananan kuɗi.
Tana alfahari kasancewarta ɗaya daga cikin malaman jami'a mata a jamai'ar garinsu, kuma tana jin ɗaɗin yadda hakan ke taimaka mata wajen ɗaukar ɗawainiyar iyalinta.
A yanzu takan karɓi rance kuɗi a wajen wata 'yar uwarta, ba tare da sanin lokacin da za ta biya ba.
Liza ta fara aiki a matsayin malamar jami'a shekara 11 da suka wuce. Tana da digiri na biyu, yayain da take koyarwa ta yi amannar cewa matsalolin da ta shiga a wancan lokacn sun haifar mata ɓarin ciki.
“Na sadakar da jaririn ga karatu da aikina, amma a ƙarshe na rasa duk komai da nake da burin samu,” in ji ta.
A yanzu tana da 'ya'ya uku, da kuma juna-biyu, amma ba ta da kudin da za ta je asibiti domin a duba lafiyar junan. Ta ce a wasu lokutan idan yaran nata suka ganta tana kuka , sai su riƙa tambayarta dalilin kukan, sai dai kawai ta rungume su ba tare da yi musu bayanin dalilin ba. ''Na sani ba zan iya bayanain irin taƙaici da bakin cikin da nake ji ba'', in ji ta.
“Ina cikin matuƙar damuwa, saboda tuninin aikina dakuma ɗawainiyar 'ya'yana. Ayanzu ba na iya ɗaukar ɗawainiyar 'ya'yanta kamar yadda ya kamata,'' in ji ta.
Liza tana ƙarama a okacin da Taliban suka fara karɓe mulkin Afghanistan “An samu ɓullar yunwa a ko'ina cikin ƙasar nan, mutane ba sa iya ciyar da iyalinsu,” in ji ta.
Iyayenta sun tafi da ita zuwa ƙasar Iran, inda suka zauna na tsawon shekara bakwai. “Bana son 'ya'yana su yi irin rayuwar da muka yi a wancan lokacin,” kamar yadda ta bayyana.
Idan abubuwa suka yi wa Liza zafi, ta ce takan bai wa fulawar gidanta ruwa domin samun sauƙi a ranta na ɗan lokaci.
“Ina fatan wata rana, wani ya taimakemu kamar yadda nake bai wa fulawar nan ruwa, muma ya ceto rayuwarmu” In ji Liza.
'Ina neman adalci'
Shekara uku da suka gabata, Zala, wadda a yanzu shekarunta 30, tana matsayin mai shigar da ƙara ta rundunar sojin ƙasar. Tana da digiri a fannin shari'a da kimiyyar siyasa, kuma tana karatun digirinta na biyu.
Aikn da take yi da ya ƙunshi binciken sojojin da ake zargi da aikata laifi, ''cike yake da ƙalubale da wahalhalu'' in ji ta.
Ta ce masu laifi sun sha yi mata barazana, amma ta ce tana farin ciki game da aikin nata, kasancewar tana da 'yanci kuma tana yaƙi ne don ''tabbatar da adalci''.
Zala ta kasance wadda duka 'yan'uwanta suka dogara da ita, inda take zaune a Kabul ''Albashi a ƙarshe da na karɓa shi ne kwanaki biyu kafin Taliban su ƙwace Kabul'', in ji ta.
Albashin ya kai dala 511 a wata guda. Bata da aure, amma takan yi amfani da albashin wajen ɗauar nauyin kanta da 'yan'uwanta shida. ''Sai dai yanzu babu ɗaya daga cikimu da ke da sana'a,'' tana mai cewa a yanzu duk abin da ta tara ya ƙare.

Asalin hoton, Getty Images
A baya Zala kan je wurin motsa jiki, a kowace safiya, amma yanzu an haramta mata hakan, kuma ba za ta iya ci gaba da karatu ba.
“Abin da nake yi kawai shi ne zama a ƙuryar ɗakina. Idan na gama duk abin da nake yi a gidan, sai dai na shiga shafukan sada zumunta ko na yi barci. Ba ni da wata fata a yanzu, babu wani ƙwarin gwiwwa,'' in ji ta.
“Duk da cewa a ƙarƙashin gwamnati da ta gabata mata sun fusknaci ƙalubale, amma aƙalla akwai dokokin da ke kare mana 'yancinmu, muna muna da damar yinmagana a ji mu,” in ji ta. “Muna da fukafukin da zamu tashi, amma yanzu gwamnatin Taliban ta yanke mana fukafukin.”
“A baya na kasance mai yaƙi da 'yancin mata a ƙasarmu,” in ji ta. “Amma a yanzu an kange mu, an hana mu komai. Ko tufar da za mu sanya sai an zaɓa mata kalar da ake so mu saka.”
“Ban taɓa ganin mummunan abu irin wanan ba. Halin da muke ciki da makomarmu na cikin duhu. Ba ma hango ko alamar haske a cikin fatanmu.”