An kashe wata yarinya a cikin gida bayan farmakin Isra'ila

Women and girls mourn during the funeral of 16-year-old Palestinian Loujain Musleh in Kafr Dan, in the north of the occupied West Bank (4 September 2024)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An yi jana'izar Lujain Musleh a Kafr Dan ranar Laraba, kwana guda bayan harbe ta a lokacin samamen Isra'ila
  • Marubuci, Mallory Moench
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC

An gudanar da jana'izar wata matashiya Bafalasɗiniya mai shekara 16 da rahotonni suka ce sojojin Isra'ila sun kashe a arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye a rana ta bakwai ta manyan hare-hare da Isra'ila ke kai wa a yankin.

Mahaifin Lujain Musleh ya ce sojoji sun harbe ta, lokacin da ta leƙa waje ta tagar gidansu da ke garin Kafr Dan, da ke wajen birnin Jenin, bayan da sojojin suka yi wa gidan wani makwabcinsu ƙawanya a ranar Talata.

Rundunar sojin Isra'ilar ta ce masu ɗauke da makamai a yankin sun buɗe wa sojojin wuta, abin da ya sa suka ''mayar da martani kan wadda suke zargin bayan ta gansu''.

Ma'aikatar lafiyar Falasɗinu ta ce an kashe Falasɗinawa 30 tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da abin da ta kira aikin kakkaɓe ''yanta'addan da ke ɓoye'' a yankin.

Ƙungiyar Hamas da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta PIJ sun yi iƙirarin cewa mafi waɗanda aka kashen mambobinsu ne, amma ma'aikatar lafiyar yankin ta ce akwai ƙananna yara da dama cikin wadanda suka mutu.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojanta guda a lokacin hare-haren.

An samu ƙaruwar hare-hare a Gabar Yamma da Kogin Jordan tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta ƙaddamar, wanda shi ne ya haifar da yaƙin Gaza.

Ƙungiyar da ke fafutikar kare haƙƙin yaran Falasdinawa (DCIP), ta ce sojojin Isra'ila sun shiga garin Kafr Dan da misalin ƙarfe 11 na safe a ranar Talata, lamarin da ya haifar da arangama tsakaninsu da ƙungiyoyin Falasɗinawa masu ɗauke da makamai.

“Sojojin Isra'ila sun zagaye tare kange gidan wani Bafalsɗine da suke nema ruwa a jallo, inda suka riƙa harba harsasai da makam cikin gidan,'' in ji ƙungiyar.

“Da misalin ƙarfe 2:10 na rana, matashyar, Loujain mai shekara 16 - wadda ke cikin gidansu a lokacin da wani ƙwararren mai harbi na Isra'ila ya harbe ta a ka ta tagar gidansu''.

A lokacin jana'izar Loujain da aka gudanar ranar Laraba, mahaifinta Osama ya shaida wa manema labarai cewa ''ba ta je ko ƙofar gida ba balantana ta riƙe dutse bare kuma makami''.

"Abin da kawai ta yi shi ne leƙewa ta gata, inda sojan ya hangota sannan ya harbeta."

Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojinta sun yi wasu gidaje biyu ƙawanya a yankin na Kafr Dan, inda suka yi amanna cewa mayaƙa masu ɗauke da makamai na zama a ciki don haka ne suka yi ''kira ga fararen hular da ke ciki da su fice kafin fara musayar wutar da aka yi a wurin.''.

“A lokacin da sojojinmu suka zagaye gine-ginen, 'yan'addatan sun buɗe musu wuta a wurin, don haka ne suka mayar da martani ga wadda suke zargin, bayan ta ga sojojin a wani mataki na kawar da barazana'', in ji rundunar sojin Isra'ila.

“Rundunar sojin Isra'la na sane da rahoton kan matashiyar ƴar shekara 16 da aka kashe a lokacin musayar wutar, ana nazari kan faruwar lamarin

Hotunan jana'izar sun nuna yadda aka lulluɓe gawarta da tutar Hamas. Galibi waɗanda Isra'ila ta kashe ana lullube gawarsu ne da tutar Hamas, ko da kuwa waɗanda suka mutu ba su goyon bayan ƙungiyar.

Palestinians

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ministan tsaron Isra'ila ya fada wa rundunar sojin kasar su yi yaƙi da ƙarfinsu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Ƙungiyar DCIP, ta kuma bayar da misali kan wasu bayanai da ta samu inda ta ce sojojin Isra'ila sun kuma kashe wani yaro ɗan shekara 14 Mohammed Kanaan da aka harbe a ranar Talata a sansanin ƴan gudun hijira na Tulkarm. Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana nazari kan rahoton.

Lokacin da BBC ta yi tambaya kan rahotannin kisan fararen hula, rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojinta na aiki ne bisa kiyaye dokokin duniya.

"Rundunar IDF ba za ta taba kai wa fararen hula hari ba," a cewarta. "Diba da ci gaba da musayar wuta, ci gaba da zama a wurin yaƙi yana da nasa hatsari. IDF za ta ci gaba da daƙile duk wata barazana tare da kuma ƙoƙarin kauce wa duk wani abin da zai yi illa ga fararen hula."

IDF ta ce sojojinta sun kashe wasu mayaƙa a musayar wuta a Tulkarm ranar Talata, tare da gano wani bom da aka ɓoye a wani keken yara.

A ranar Litinin da yamma, ta sanar da cewa an kashe "ƴanta'adda" 14 a Jenin, tun soma sabon farmakin, sannan ta kama mutum 25 da take zargi.

"Dole a murƙushe duk wani ɗanta'adda, amma idan sun miƙa wuta, za a kama su. Babu wani zaɓi, za a yi amfani da ƙarfin tuwo," kamar yadda ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya faɗa wa dakarun IDF a ranar Laraba.

An Israeli armoured bulldozer digs up a road during a raid in Tulkarm, in the occupied West Bank (4 September 2024)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yadda wata babbar motar Isra'ila ke tonon hanyoyi a Tulkarm lokacin samame a ranar Laraba

Firaministan gwamnatin Falasdinawa Mohammed Mustafa ya ce hasarar da aka tafka sakamakon farmakin, musamman ma abubuwan more rayuwa, ta kasance mafi muni cikin shekaru 20.

Shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana damuwa kan Jenin.

An tarwatsa unguwannin Jenin, wanda da wahala mota ta iya bi, Isra'ila ta rusa shaguna a birnin.

Hukumomin yankin sun ce manyan motocin Isra'ila sun rusa kusan kashi 70 na hanyoyi, sun kuma lalata hanyoyin samun ruwa kusan kashi 80 na birnin da magudanar ruwa da kuma hanyoyin sadarwa da lantarki.

Sai dai IDF ta ce: "Yan'tadda a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan suna amfani da fararen hula a matsayin garkuwar yaƙi saboda wasu dalilai, wajen samar da abubuwan more rayuwa saboda ta'addanci da dasa abubuwan fashewa a ƙarƙashin hanyoyin da nufin kai wa IDF hari a lokacin da suke ƙoƙarin murƙushe barazana ga rayukan ƴan Isra'ila."

Ta ce za ta gaggauta yin aiki domin ba hukumomin yankin damar gyara abubuwan more rayuwa da aka lalata.

A Palestinian woman stands surrounded by rubble on a street in Jenin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jami'ai sun mazauna Jenin ba su samun isasshen abinci da ruwa da magani

Dakarun Isra'ila sun yi wa asibitin gwamnati ta Jenin ƙawanta tun da ta soma farmakin.

Daraktan asibitin Dr Wisam Baker ya shaida wa BBC a ranar Litinin cewa wanda ke iya shiga da fita, ciki har da likitocin asibitin kamarsa da ke zuwa gida, dole sai cikin motar daukar marar lafiya.

Sojoji na binciken motocin da kuma katin shaidar waɗanda ke ciki, in ji shi.

Direbobin suna tsoron karo marar lafiya zuwa asibitin ko kuma samun tsaikun shiga saboda bincike, in ji shi, yana mai cewa tsaikun zai iya zama barazana ga rayuwar mutum.

Ana tafiyar da harakokin asibitin ne da janareto, kuma a kullum ana kawo tankin ruwa 10, a cewar Dr Baker. Motocin ɗaukar marar lafiya kuma suna kawo abinci.

Da aka tambaye ta kan kasancewar dakaru a asibitin, IDF ta yi zargin cewa mayaƙa ne amfani da likitocin da kuma yin amfani da asibitocin waɗanda dokar ƙasa da ƙasa ta ba kariya.

"Asibitocin na ci gaba da aiki yadda suka saba. Ana gudanar da bincike kan waɗanda aka kawo asibitin, idan har hakan ba zai hana kula da su ba ko kuma jefa rayuwarsu cikin hatsari.

Kungiyar agaji ta Falasɗinawa, ta ce jami'anta na aiki tuƙuru domin samar da taimakon gaggawa ga mutanen da aka yi wa ƙawanya a sansanin Jenin, duk da ƙalubale daga dakarun Isra'ila da ke tarnaƙi ga ayyukansu.

A ranar Litinin, ta ce mazauna Jenin da dama na ɓukatar taimakon gaggaw na magani, da abinci, yayin da kuma aka raunata ma'aikatan sa-kai.

Taswirar da ke nuna  Jenin, Tubas, Nablus daTulkarm da Isra'ila ta mamaye