Abin da muka sani kan sabon harin Boko Haram ga sojojin Najeriya a Marte

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na nuna cewa mayaƙan Boko Haram sun kai wa sojoji hari a sansaninsu da ke Marte na jihar Borno, inda ake zargin sun kashe wasu sojoji da ba a iya ƙididdige adadinsu ba zuwa yanzu, sannan suka yi awon gaba da wasu.
Bayanan sun ƙara da cewa mayaƙan sun kai harin ne a kan sansani sojojin bataliya ta 153 da tsakar daren wayewar garin ranar Litinin.
Ƴan Boko Haram ɗin sun kai harin ne a kan babura riƙe da makamai, inda suka lallaba sansanin sojin da misalin ƙarfe 3 na dare, kamar yadda bayanai suka nuna.
Wasu daga cikin sojojin sansanin sun tsere zuwa babban sansanin soji na 24 birged da ke Dikwa da ke kusa da su, inda suka haɗu suka sake shiri, sannan suka koma suka sake ƙwace sansanin nasu tare da fatattakar ƴan Boko Haram ɗin.
Har yanzu dai rundunar sojan ƙasa ta Najeriya ba ta ce komai ba game da wannan sabon harin.
Ana dai fuskantar sababbin hare-hare a ƴan kwanakin a yankin arewa maso gabas da ake zargin ƴan Boko Haram da ISWAP da kitsawa.
Sabbin hare-haren na rura wutar fargabar cewa mayaƙan sun fara komawa bakin daga da ƙarfinsu, musamman ganin yadda suke amfani da sabon salon amfani da jirage marasa matuƙa da dasa nakiyoyi a manyan hanyoyi.
Hare-haren Boko Haram a Afrilu
A tattaunawarsa da BBC, Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, ya ce daga watan Maris zuwa yanzu mayaƙan Boko da ISWAP sun kai hare-hare sama da goma a jihohin Borno da Yobe.
Ya ce sai dai ba kamar yadda aka saba ba, yanzu mayaƙan sun fito da wasu hanyoyi kai hari da ake kira 'complex attack' "inda suke amfani da hanyoyi da dama irin su amfani da bindiga ta hannu da wadda ake kafewa a mota da jirage marasa matuƙa da kwantar ɓauna da kuma dasa bama-bamai a hanyoyi."
Daga cikin hare-haren guda, manyan waɗanda aka yi a watan Afrilun su ne:
- A ranar 12 ga Afrilun, an kai hari a garin Kumshe da ke ƙaramar hukumar Bama, wadda tsagin ISWAP muke tunanin ta kai a sansanin sojoji. Sojojin sun mayar da martani har suka kashe ɗaya daga cikin maharan, amma bayanan da muka samu sun nuna an kashe sojoji tsakanin ɗaya zuwa uku.
- A ranar 12 ga watan Afrilun, wata nakiya da aka binne ta fashe a titin Maiduguri zuwa Damboa, inda mutum takwas fararen hulha suka mutu.
- A ranar 18 ga Afrilu, akwai wani hari da aka kai wa sansanin soja da ke garin Gwazo a ƙauyen Ƴantake, inda aka kashe aƙalla sojoji biyu da wasu ƴan sa-kai, wasu kuma suka jikkata, sannan maharan suka kwashe makamai.
- A ranar 21 ga Afrilu, an kai hari a sansanin soji a garin Buni-yadi da ke ƙaramar hukumar Gujiba ta jihar Yobe, inda aka kashe aƙalla sojoji tsakanin huɗu zuwa takwas, sannan aka jikkata wasu.
- A ranar Asabar, 26 ga watan Afrilu mayaƙan sun kai wani hari a ƙauyen Kopre da ke ƙaramar hukumar Hong a jihar Adamawa, inda suka kashe maharba da fararen hula aƙalla guda 10 ta hanyar yi musu kwantar ɓauna.
- Sai kuma wannan sabon wanda mayaƙan suka kai wa sansanin sojin da ke Marte.
Ƙarfin mayaƙan na ƙaruwa?
A game da batun da wasu ke yi cewa an fara komawa gidan jiya a hare-haren Boko Haram da ISWAP, Dr Kabiru Adamu ya ce, "bayanai na nuna ana samun sabon yunƙuri daga ƴan ƙungiyar. Sai dai akwai bambanci tsakanin Boko Haram da ISWA, kuma yawancin waɗannan hare-haren da na lissafa ƴan ISWAOP ne suke yi."
Ya ce akwai wasu abubuwa guda huɗu da suka sa mayaƙan suke samun nasara a yunƙurinsu na sake samun ƙarfi:
- Abin da ke faruwa a yankin Sahel wato juyin mulki, musamman Nijar saboda girman iyakokinta da Najeriya. Ta daina tsaron bakin iyaka ta koma tsaron cikin gida.
- Raba hankalin sojojin Najeriya saboda ƙaruwar matsalolin tsaro. Alamu na nuna an kwashe wasu makamai da sojoji daga arewa maso gabas zuwa arewa maso yamma.
- Rashin sanya mutane (masana masu bincike) a ciki domin samun bayanan sirri sahihai.
- Rashin haɗin kai tsakanin jami'an tsaro. Saboda har yanzu ƙungiyoyin ba su da jiragen yaƙi manya wato 'fighter jet' sai dai ƙanana. Ke nan idan aka samu haɗin kai sosai, sojojin saman Najeriya za su yi musu illa sosai.
Sai dai ya ce duk da irin abin tashin hankali da ake gani musamman hare-hare a sansanin soji, alƙulama suna nuna cewa "an samu raguwar hare-hare, sannan walwalar jama'a a yankunan sun inganta. Sai dai ana fata da fargabar kada a koma gidan jiya."