Gane Mini Hanya: Kan Ranar Mata ta Duniya 08/03/2025

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Kan Ranar Mata ta Duniya 08/03/2025

Kowacce shekara, tsawon sama da ƙarni guda, ana keɓe ranar 8 ga watan Maris a matsayin Ranar Mata ta Duniya.

Gwamnatoci da ƙungiyoyi da yawa a faɗin duniya suna karrama wannan biki saboda gudunmawar 'ya'ya mata da kuma tabbatar da 'yancinsu.

Tun tale-tale dai, mata da 'yan mata ba su cika samun dama iri ɗaya da ta maza ba, kuma har yanzu mata na fuskantar wariya, kodayake al'ummomin na faɗi-tashin ganin an canza hakan.

Albarkacin wannan rana ta bikin mata, Aisha Shariff Bappa ta duba mana ƙoƙarin da wasu al'ummomi ke yi.