Yadda za a kawo ƙarshen rikicin Kudancin Kaduna

Bayanan sautiRahoton Ibrahim isa kan lalubo bakin zaren rikici a Kudancin Kaduna

Latsa alamar lasifikar domin sauraron rahoton Ibrahim Isa

A Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, bangarorin al`umma da ke kudancin jihar na ci gaba da ɗora wa juna alhakin rikicin da ya ƙi ya ƙi cinyewa a yankin, wanda kuma ke haddasa asarar rayuka da dukiyar jama`a.

A halin da ake ciki, gwamnati ta kafa dokar hana fita a wasu ƙananan hukumomi biyu da nufin magance matsalar.

Amma masana harkokin tsaro na ganin cewa aiwatar da shawarwarin da wasu kwamitocin bincike suka bayar a baya, ita ce sahihiyar hanyar dawwamar zaman lafiya a yankin.

Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce bambancin ra'ayi na daga cikin abin da ya haifar da rikicin kuma "ba a samu wata kafa ba ta magance wannan bambancin ra'ayin sai siyasa ta shiga cikin lamarin."

A ganinsa, rashin ɗaukar matakin hukunta masu hannu a ta da rikicin na ta'azzara lamarin.