Aikin Hajji: Shin dakatar da shiga Saudiyya don yin Hajji alamar tashin ƙiyama ne?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Shekaru biyu kenan a jere mahukuntan Saudiyya na hana wa al'ummar Musulmi daga wasu kasashen duniya gudanar da ibadar aikin Hajji, saboda annobar cutar korona da ke ci gaba da yaɗuwa a sassan duniya da dama.
Ɗumbin maniyyata daga ƙasashen da dama sun fara biyan kuɗaɗensu da zummar sauke farali a bana, kafin daga bisani wata sanarwar hukumomin Saudiyya ta bayyana hana 'yan kasashen waje zuwa ƙasar don yin ibadar.
Aikin Hajji na ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci, amma Ibada ce ga waɗanda Allah Ya ba hali, kuma a kan yi ta ne duk shekara, inda miliyoyin Musulmin duniya ke taruwa a Makkah domin sauke farali.
Amma dakatar da aikin hajjin shekaru biyu a jere, ya sa mutane sun fara tafka muhawara, inda wasu ke cewa dama Annabi Muhammad (S A W) ya ce da al'ummar Musulmi ''ku je aikin Hajji tun kafin a hana ku zuwa''.
Shin da gaske Annabi ya fadi hakan ?

Asalin hoton, Sheikh Mansur Ibrahim Sokkoto
Sheikh Mansur Sokoto, wani fitaccen malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa akwai wani Hadisi da aka jingina shi da Abu Huraira, wanda ya rawaito Annabi Muhamad (S A W) na cewa ''ku je aikin hajji tun kafin a hana ku zuwa''.
A cewar malamin wannan hadisi na Baihaƙi da Ɗabarani, malamai sun sanya shi cikin hadisan da suka shahara amma kuma ba su da inganci kwata-kwata.
Ya ƙara da cewa "Ba shakka ya inganta cewa yana daga cikin alamomin tashin ƙimaya cewa za a hana aikin hajjin gaba daya. sai dai jerin fitintinu ne da za su taso da Annabi ya fada za su sanya a hana, wadanda a cikinsu har da rusa ka'aba, rusawar da ba za a sake gina ta ba da zai sa a daina aikin hajji.
Fitintu ne masu yawa da za su kai ga cewa an kashe dukkanin Musulmai, lokacin da zai kasance babu mutum daya da yake cewa La ilaha illallah.
"A gaskiya ba mu zo wannan lokacin ba tukunna, yanzu annoba ce ta janyo aka hana aikin Hajji, ba wani yaki ko wata fitina ba," in ji Sheikh Mansur Sokoto.
Malamin ya ce halatta a yanzun ba wai daina aikin Hajji aka yi ba, an taƙaita yawan wadanda ke yi ne kawai, don haka shi kuma Hadisin yana magana ne a kan hanawa gaba daya, halin da ba shi ake ciki ba a yanzu.
"Abu ne da ya sha faruwa a can baya, wasu shekarun ma gaba daya ba a yi aikin Hajjin ba, wasu shekarun kuma mutanen kasar ne kawai suka yi saboda fashi da makami da aka yi ta yi a Makka.
"Akwai kuma lokacin da ambaliya ce ta hana, akwai lokacin da yaki tsakanin Ibn Zubaid da sojojin Yazid Bin Mu'awiya ya hana a yi aikin Hajji.
"Sojojin Ibn Zubaid suna Makka ba sa iya tafiya Mina da Arfat, su kuma sojojin Yazid suna wajen Makka, suna iya hawan Arfa amma ba za su iya zuwa su yi ɗawafi ba," in ji Sheikh Mansur Sakoto.
Ya ƙara da cewa rage alhazai da aka yi ba alama ba ce ta tashin Al-ƙiyama, domin akwai yanayi na annoba da ake ciki, kuma tana tasiri a kasashe da dama na duniya, don haka buɗe kasashe ko kuma a tara mutane a waje ɗaya zai sake tsananta halin da ake ciki ne kawai, kuma dakatarwar ma ta ɗan lokaci ce ba din-din-din ba.

Alamu ne na tashin ƙiyama - ra'ayin wasu malaman

Akwai kuma wasu malaman addinin da ke alaƙanta hana wa Musulmai na wasu ƙasashe zuwa aikin hajji da Saudiyya ta yi saboda cutar korona alamu ne na tashin ƙiyama.
A tasa fahimtar, Sheikh Halliru Maraya wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya ya ce "ko shakka babu hana 'yan ƙasashen waje yin aikin Hajji a yanzu alamu ne ƙarara da ke nuna cewa duniyar nan ta zo ƙarshe."
Ya ce shi kansa Hadisin da Annabi (SAW) ya ce "ku je Hajji tun kafin a hana ku" da wasu malamai ke ganin ba shi da inganci Muhammad Nasiruddin al-Albani ne kawai ya ƙaryata shi, amma sauran malaman hadisi kamar Baihaƙi sun tabbatar da cewa an rawaito wannan hadisi daga wajen Sayyadina Ali.
''Dama a ƙa'ida ta ilimi ko da Hadisi Da'ifi ne, wato ba shi da inganci, to ana aiki da shi a kan abubuwan da suke na nafila da falala, da kuma abubuwan da ake tsoratar da mutane don su guji aikata su'' a cewar Sheikh Halliru Maraya.
Ya ƙara da cewa ''Dama duk abubuwan da aka bayyana a matsayin alamun tashin alkiyama ai sun bayyana, idan ba haka ba babu yadda za a ce har Turawan nan da a can ne cutar ta fi ƙamari a cikinsu sun bude harkoki ana ci gaba da yi, filayen ƙwallon ƙafa sun bude suna tara mutane ana wasa, amma a ce sai Saudiyya wacce ba ta cikin kasashen da cutar ta fi addaba ce za ta hana aikin Hajji''?
''Ba tun yanzu ba, tun fiye da shekara 1,400 hijiriyya, Al-Kur'ani mai tsarki ya yi ishara da cewa duniya fa ta kusa ƙarewa, me ya sa sai yanzu ne za a yi mamakin haka.");