Katsina: Ƴan bindiga kan babura da suka addabi Arewacin Najeriya

Illustration

'Yan bindiga masu amfani babura waɗanda ke zaune a dazukan da aka yi biris da su na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna na arewa maso yammacin Najeriya.

'Yan bindigar su ne na baya-bayan nan da suka shiga harkar garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa inda kuma suke matsa ƙaimi a hare-harensu.

Shekaru goma da suka wuce, an kashe sama da mutum 8,000 a jihohin Sokoto da Kebbi da Naija da Zamfara kamar yadda ƙungiyar nan da ke ƙoƙarin kare afkuwa da kuma sulhunta rikici ta International Crisis Group ta bayyana.

Sai dai hare-haren baya-bayan nan da aka kai a mahaifar shugaban Najeriya wato jihar Katsina inda aka kashe sama da mutum 100 tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni sun jawo zanga-zanga inda aka nemi shugaban ƙasar da ya yi murabus.

A member of a local vigilante group in Zamfara state

Asalin hoton, Getty Images

A hare-hare biyu daban-daban, 'yan bindigar sun afka wa wasu ƙauyuka da suka samu tallafi daga gwamnati kan batun cutar korona yayin dokar kullen da aka saka.

"Su kusan 200 ne kan babura, kowane mai babur na ɗauke da fasinja kuma dukansu ɗauke da bindiga ƙirar AK 47," in ji Bashir Ƙadisau, wani ganau wanda ya shaida wa BBC yadda lamarin ya faru.

Ya ce ya hau can saman bishiya bayan ya ga yawan baburan da suka tunkari garin na Ƙadisau, kuma ya ga masu harin na fasa shaguna da satar shanu da hatsi tare da harbe mutanen da suke guduwa.

Sauyin yanayi ya ƙara rura wutar rikicin

A group of Fulani pastoralist men exchange money after cattle transactions at Illiea Cattle Market, Sokoto State, Nigeria, on April 21, 2019

Asalin hoton, Getty Images

Presentational white space

Akasarin masu kai hare-haren makiyaya ne, kuma akan gansu kan manyan hanyoyin ƙasar suna kiwon dabbobinsu, sai dai yanzu ana samun arangama tsakaninsu da manoma kan batun gonaki a arewa maso yammacin Najeriya da kuma jihohin da ke tsakiyar ƙasar.

"Ci gaban arangamar da ake samu ya sa aka kafa ƙungiyoyin sa kai da ake kira 'yan ƙato-da-gora, daga duka ɓangarorin," kamar yadda wani mai nazari kan harkokin tsaro Kabiru Adamu ya shaida wa BBC.

'Garkuwa da mutane ya fi kawo kuɗi kan kiwon shanu'

Ana zargin 'yan bindiga da ke cikin al'ummar Fulani da aikata manyan laifuka.

"Makiyayan a halin yanzu na kallon garkuwa da mutane da sata a matsayin abin da ya fi kawo kuɗi kan batun kiwo.

"Saniya mafi girma za a saye ta ne kan 200,000 amma mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi kan iya kawo miliyoyi," in ji Dakta Adamu.

Herdsmen along with their cows wait for buyers at Kara Cattle Market in Lagos, Nigeria, on April 10, 2019. - Kara cattle market in Agege, Lagos is one of the largest of West Africa receiving thousands of cows weekly due to the massive consumption of meat in Lagos area.

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai Fulani makiyaya sun musanta wannan zargin.

Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyeti Allah, sun ce su ne hare-haren 'yan bindigar ya fi shafa kuma an yi garkuwa da ɗaruruwan mambobinsu.

"An sace shanunmu. 'Yan bindigar wasu gungun mutane ne ɗauke da nau'ukan mutane daban-daban. Mun yi asarar kusan kashi 30 cikin 100 na shanunmu ga rikici daban-daban a Najeriya," in ji sakataren ƙungiyar Baba Othman Ngelzarma a wata tattaunawa da BBC.

Ya bayyana cewa waɗanda suke kai hari a arewa maso yammacin Najeriya "makiyaya ne daga makwaftan Najeriya".

Map: Nigeria
Presentational white space

'Makiyayan na neman ɗaukar fansa'

Iyakokin ƙasar a wangale suke kuma 'yan bindigar sun mayar da dazukan tamkar wata matattara ko kuma sansaninsu.

'Yan sanda a arewa maso yammacin Najeriya sun ce wasu gungun 'yan tayar da ƙayar baya ne ke kai hare-haren tare da Fulani makiyaya.

"Fulani makiyaya sun gane cewa suna da makamai da za su kare kansu. Sai dai ba wai suna kare kawunansu bane, suna bi domin ɗaukar fansa kan waɗanda suka yi musu laifi a baya," in ji Isah Gambo, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan reshen Katsina, a wata tattaunawarsa da BBC.

Bayanan bidiyo, .

Garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa ya yi ƙamari a Najeriya inda waɗanda ake yin garkuwa da su ke biyan tsakanin naira 7,000 zuwa miliyan bakwai domin karɓar yancinsu.

A lokacin da lamarin ya yi ƙamari tsakanin 2017 zuwa 2018, ana samun ayyukan garkuwa da mutane kusan sau goma a rana kan hanyar Abuja zuwa Kaduna inda ƙungiyoyi sama da 20 ke aikin garkuwar kan hanyar, a cewar Abba Kyari, wani ɗan sanda mai jagorantar runduna ta musamman da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane a Najeriya.

Sulhu da 'yan bindiga

A shekarar da ta gabata, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kutsa cikin dazukan da 'yan bindigan suke zaune inda ya yi yarjejeniya da su aka cimma matsaya domin su bar kai hare-hare domin a yafe musu.

A picture taken on May 10, 2016 in Okokolo-Agatu in Benue State, north-central Nigeria shows a burnt house following attacks by Fulani herdsmen.

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai 'yan Najeriya da dama sun razana bayan da aka ga hotonsa tare da 'yan bindigar inda wani daga cikin 'yan bindigar ke riƙe da bindiga ƙirar AK 47.

Wani ɗan kasuwa a jihar wanda aka yi garkuwa da shi a Katsina kwanaki kaɗan kafin wannan sulhu ya soki gwamnan kan wannan yunƙuri.

"Ta ya gwamnatin jiha za ta yi sulhu da ɓarayi waɗanda ba su da ilimi, ba su da tausayi, ba su da imani, mutanen da suke abubuwa kamar dabbobi," in ji shi.

Malam Ahmed ya bayyana cewa ya yi faɗa da ɓarayin da suka yi garkuwa da shi inda ya kwana saman bishiya a cikin daji.

"Na ji zafi ƙwarai da na ji labarin gwamna ya yi sulhu da su," a hirarsa da BBC.

Ana yi wa Buhari zagon ƙasa

Gwamnan ya bayyana cewa an yi sulhun ne domin kawo ƙarshen "kashe-kashe da kuma asarar dukiyoyi", kuma tattaunawar ta kawo ci gaba.

Sai dai a watan da ya gabata, Masari ya shaida wa 'yan jarida cewa yarjejeniyar da aka yi da ɓarayin ta ruguje sakamakon yawaitar hare-hare.

"Waɗannan ɓarayin na zuwa garuruwa su harbi mutane su kashe mutane ba tare da wata hujja ba. Ta ya ɗan adam zai rinƙa rayuwa irin ta dabbobi");