Abin da ba ku sani ba kan fashewar batutun mai na Lagos

A ranar Lahadi da safe 15 ga watan Maris din 2020 ne aka samu fashewar bututun man fetur a unguwar Abule-Ado da ke birnin Legas a kudancin Najeriya.
A yayin da aka yi amanna cewa wani abu ne ya fashe har ya yi sanadin da gine-ginen da ke kusa suka rushe tamkar hotunan yadda bam ke tarwatsa gini a kasar Syria, tambayar da kowa ke yi ita ce, "Me ya jawo hakan");