Tuwon Sallah: Ina zamani ya kai shi?

Asalin hoton, KHADIJA DANFULOTI
- Marubuci, Mukhtari Adamu Bawa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Broadcast Journalist
Saɓanin shekarun baya, lokacin da matan gida kan shafe tsawon wunin jajibere da daren sallah, suna haƙilon shirya tuwon sallah, a zamanin yau, kuna iya cin girkin sallah, ba tare da hayaƙi ko ƙauri sun bulbule ku ba.
Kwance cikin falon gida, babu kwaramniya da yarfe gumi a ɗakin girki, kuna iya buɗe kwano kawai, ku ci tuwon sallah mai daɗin gaske cikin annushuwa.
"Da sallah, akwai manyan mutane da manyan mata, saboda ba sa son wahala, za su zo, su ce a yi musu abincin sallah. Kuma idan an yi musu, za mu ɗauka mu kai musu har gida", in ji Anas Yakubu Musa, wani mai gidan abinci a Kano.
Ya ce abokan hulɗa kan zo tun sallah saura mako biyu, su ce a yi musu girkin shinkafa nau'i uku ko huɗu da dahuwar kaza nau'i biyu. Idan sun gama, sai su zuba a mazubai su kai wa mutum har gida.
Ba kawai daɗi da ƙamshin tuwon sallah ne ke da jan hankali ba a yanzu, yadda za a tsara zubin abincin a kwano ma abin la'akari ne

Asalin hoton, SHAWARMA HOUSE

Asalin hoton, SHAWARMA HOUSE
Mai gidan abinci na Shawarma House, Anas Yakubu Musa ya ce: "Sai ka ga shinkafa ita kaɗai kala uku a filet, ga salak a gefe, ga kuma kaza.
Abin gwanin ban sha'awa da burgewa".
Mai gidan abincin ya ce masu buƙatar abincin sallah sun fi zuwa neman shinkafa a wurinsa. "Sai ɗan kayan snacks; irinsu samosa da tsire da sauransu. Akwai kuma kaɗan da za ka ga suna zaɓar a yi musu tuwo.
Za ka ji suna cewa al'ada ce. Tuwon sallah!

Asalin hoton, SHAWARMA HOUSE
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan ƙayatarwa game da Sallar Idi tsawon zamani a ƙasar Hausa, shi ne tuwon sallah.
Abincin biki ne na musamman don ranar Idi, a birni da ƙauye. Gidan talaka, da na mai kuɗi, har ma da masu mulki.
Alama ce ta al’ada da ke sanya annuri da annushuwa, gami da farin ciki a fuskoki.
Mai yiwuwa ma, yana cikin dalilan da suka sa, Sallar Idi ta zama bikin al'umma na shekara-shekara mafi burgewa, wanda Hausawa ke matuƙar ji da shi.
Wata masaniya, Dr. Hadiza Salihu Koko ta ce asalin tuwon sallah, ba ya rasa nasaba da murna. An kammala azumin Ramadan lafiya.
"Ranar sallah, da ma ana so a kyautata, a inganta abinci, a lilwanta iyalai" in ji malamar, wadda ke koyarwa a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari a jihar Sakkwato.
Bayan shafe tsawon wata, ana ƙauracewa abin ci a wuni, yanzu lokaci ne na yin ban kwana da Ramadan mai alfarma. Ana kuma yin hakan ne, ta hanyar kyautatawa da yalwata alheri, da ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ‘yan’uwa da dangi, maƙwabta, kai har ma da baƙi.
Wannan kuwa, sai abincin fita-kunya!

Asalin hoton, KHADIJA DANFULOTI
Ƙaramar sallah tana buɗe ƙofar marmarin abincin da aka daɗe ba a ci ba, in ji wata matashiyar matar aure a birnin Abuja.
"Tun lokacin da aka fara azumi na ce ba zan ci tuwo ba. An fi cin abincin maƙulashe da tanɗe-tanɗe".

Asalin hoton, KHADIJAH ƊAN FULOTI

Asalin hoton, SHAWARMA HOUSE
To tsawon wata ɗayan nan, na cika da kwaɗayi da marmarin tuwo".
A cewar Ni'ima Ibrahim "Idan aka yi sallah, ban ci tuwo ba, sai in ga kamar ba (bikin) sallah ba".
Ta ce al'ada ce da ke tuno mata karimcin iyaye da kakanni. Tuwon Sallah kan bijiro mata da hoton zuci, na yadda magabata ke ganin darajar ciyarwa da rabon abinci. Ga kuma yadda ake taruwa a ci abinci kwano ɗaya.
Ga alama dai, duk da ɗumbin ƙalubale da sauye-sauyen rayuwa, zamani bai iya yin tafiyar ruwa da wannan al'ada ta Hausawa ba,
Wata dattijuwa a birnin Kano, Hajiya Hassana Rimin Ƙira ta ce, a tsawon shekara hamsin, ba ta taɓa fashin tuwon sallah ba.
"Saboda, abu ne mai muhimmanci," in ji ta. "A duk lokacin da aka ce ba zan yi ba, sai kawai na ji zuciyata ba daɗi."

Asalin hoton, Getty Images
Ga alama dai, ƙwarjinin wannan al'ada ta Hausawa, kan fara bayyana ne, tun ran jajiberen sallah. Manyan hidimomin da mata kan yi a ranar, su ne kitso da ƙunshi. Sai kuma shirya abincin sallah.
Murna da kekkewa da ɗokin sallah a wajen yara, ba sa misaltuwa.
Jajibere, rana ce mai faranta zuciya da sa kyakkyawan fata na zuwan wani babban abin alheri.
Musamman idan an yi gam-da-katar, tuni an karɓo ɗinkin sallah. An saya wa yara takalma da huluna ko ɗan kwali. Ga sabbin 'yan kunnaye da sarƙoƙi.
Kai! Cefanen tuwon sallah kawai, yakan sa yara su yi ta tsallen farin ciki. Su kasa zaune, su kasa tsaye a gida.

Asalin hoton, Getty Images
Tuwon Sallah a da
Wasu dai na da ra'ayin cewa, duk da ɗumbin tarihi da alhairan da ke tattare da ita, al'adar tuwon sallah tana daɗa ja baya a tsakanin Hausawa.
Hajiya Hassana Rimin Ƙira da ke cikin shekarunta na 70, ta bayyana damuwar cewa a yanzu, karimci ya yi rauni, don kuwa ko da halin yi, ba kowanne gida ake yin tuwon sallah ba.
Ta ƙara da cewa: “A cikin gida goma, bai fi a samu gida biyu da ke tuwon sallah ba a yanzu. Ko rowa ce, ko talauci ne, ko mene ne? Ban san ma’anar wannan abu ba".
Sai dai Anas Musa ya ce mai yiwuwa tsadar rayuwa ce ta shafi wannan al'ada ta tarihi. "Tuwon sallah a gida, ya fi tsada kuma ga shi babu biyan buƙata."
A shekarun baya, in ji Dr Hadiza Salihu Koko yawan karimci da son tallafa wa juna sun sa tuwon sallah ba ya gagarar hatta mai ƙaramin ƙarfi.
Masu hali kan fitar da zakkar kono wato fid-da-kai. "To, idan aka fitar, aka ba su, ita ce za su yi amfani da ita, su yi tuwon sallah. Su ci a gida ko da ba su rarraba ba"

A cewar Hajiya Hassana Rimin Ƙira “Iyaye ko yaya ake ciki, an san lokacin tuwon sallah ya yi a shekarun baya. Babu hali kamar yanzu amma akwai ƙoƙari".
Ta ce a lokacin suna amare, "Za a aika musu (wani abu da ake kira) ‘Kaiwar Sallah’.
Ko iyayen miji suna yin nasu, amma za ki yi naki tuwon sallah daban. Ki tara mutane da ‘yan’uwa da wanda duk i zo, a sa mai, ya ci.
Saɓanin yanzu, ba haka ake yi ba. Wannan zamanin daga ƙwauri, sai gwiwa. A gaskiya ma dai", in ji dattijuwar "Maƙwabci a yanzu, sai a ci tuwo a suɗe, bai san an yi ba".
Amma Ni'ima Ibrahim ta ce duk da rayuwar birni irinta Abuja, sukan tuna maƙwabtansu.
"Gaskiya, za ka ga ana yin tuwon sallah da yawa. Ana gayyatar mutane da yawa.
Ba wai kawai mu kaɗai muke yi mu cinye ba," in ji ta. "Ana ba maƙwabta sosai.
Za ka ga, sai a saka a irin ɗan basket haka. A saka miya da ɗan zoɓo, a kai".

Asalin hoton, KHADIJA DANFULOTI
Hajiya Hassana ta ce ko a shekarun yarintarsu, ba tuwo kawai suka taso suka ga ana yi ba. "Masu funkaso za su yi, masu waina ma za su yi. A yi abinci sosai, a mimmiƙa wa maƙwabta”.
Ta ce akan yi wa tuwon sallah kirari da maganin mai kwaɗayi. "Du irin kwaɗayinka, sai ka ci, ka bar shi.”
Dattijuwar ta kuma ce a shekarun baya, har tuwon dawa, ana yi. "Kuma tuwon dawa, a lokacin yana da daraja. Za ka ga ana rububin sa, ana ci”.
Masu yin tuwo, suna nan da yawa har yanzu. "Kawai sai dai canjin abincin," in ji Dr Hadiza Koko.
"Wasu su yi waina, wasu funkaso, wasu sinasir da sauransu".
Zama da tsofaffi kuma ga alama ya sa matasan matan aure kamar Ni'ima Ibrahim, har yanzu ba su san wani abincin sallah ba, sai tuwo.
Ta ce tuwon shinkafa ta saba yi na gargajiya saboda tun ainihi, shi ta tashi ta gani wajen iyaye da kakanni. "Za ka gani, tun iyaye miyan kabewa ake yi. Miya ya ji kabewa sosai, ya ji tantaƙwashi, ya ji alayyahu".
Ƙamshi da ɗanɗanon girkin, in ji ta, sun fita daban.
Mai gidan Shawarma House ya ce a bana ya karɓi buƙatun yin tuwon shinkafa daga mutum biyar.
"Suna son a yi musu tuwon sallah, miyar taushe. Wasu kuma su ce shinkafa, wasu su ce tuwo da shinkafa, da kuma ɗan 'snacks' suke so, don su haɗa wa mutane".

Asalin hoton, SHAWARMA HOUSE
Duk da yake, Ni'ima Ibrahim tuwo kawai ta sani don ƙayata bikin sallah a gidanta, amma ta faɗa min cewa akwai mutanen da ta sani da ke girka abincin ƙasashen waje kamar shinkafar mutanen China (Chinese rice) da Biryani duk a matsayin tuwon sallah.
Sai dai tana ganin irin waɗannan nau'o'in abinci, ba sa taimakawa wajen tattalin al'adun gargajiyar Bahaushe.
Anas Musa ma ya ce wasu kan zo, su ce tsire suke so a wurinsa. "Da kabaab da kafta da kidney, wanda a gida za a ɗan ba mutane. Ba abinci ne (mai nauyi) ba".
A cewar Dr Hadiza Koko, abincin biki nau'i ɗaya yana iya sa gundura. Amma abincin da aka yi musaya da juna tsakanin maƙwabta, yana kore haka.
Tuwon sallah dai, maganin mai haɗama, in ji Hausawa!
"Za ka ga an yini, ana cin abinci, saboda ga shi nan kala-kala, an kawo daga wurare daban-daban sai wanda kaz zaɓa.
Wani yana iya kawo waina, wani ya kawo tuwo, wani ya kawo shinkahwa. Ga su nan dai gwargwado. Mutum zai wuni yana annushuwa".

Asalin hoton, SOKOTO GOVERNMENT
Gidajen abinci za su ƙwace wa mata ragama
Masu gidajen abinci irin Anas Yakubu Musa suna ƙara samun kasuwa a lokacin bukukuwan sallah.
Ya ce ƙwarewarsu da rashin bai wa abokan kulɗa kunya wajen shirya abincin fita-kunya kamar tuwon sallah cikin gwaninta sun sa mutane na ƙara neman ƙwararrun masu dafa abinci.
Ko ba komai, in ji shi, ba a ko'ina ake samun ɗanɗano da daɗi da iya tsara dafaffen abinci mai rai da lafiya a kwano, da ƙamshin burgewa ba.
"A kawo muku har gida, ba tare da kun san wata wahalar da aka yi ba, kawai ci kuka sani" in ji mai gidan abincin.
"Sai dai ku ci, ku ji daɗi, shi ma wanda aka ba, ya ci ya ji daɗi. Sai a yi ta tunanin ta yaya aka yi haka");