Dalilan ƙungiyoyin fararen hula na kiran Sanata Akpabio ya sauka

Asalin hoton, President of the Senate/Twitter
Wasu fittatun ƙungiyoyin kare fararen hula a Najeriya sun yi kira ga Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio ya sauka daga muƙaminsa.
Matakin ya zo ne kwanaki ƙalilan bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin wata ƙaramar kotu a kan Farfesa Peter Ogban, baturen zaɓen ɗan majalisar dattijai na Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a 2019, bayan ta same shi da laifin tafka maguɗi.
A ranar Laraba ne dai kotun ɗaukaka ƙarar a Calabar, ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara uku da ƙaramar kotu ta yi wa Farfesa Ogban, saboda ta same shi da laifin shirya sakamakon ƙarya wanda ya bai wa Sanata Akpabio na jam'iyyar APC nasara.
Wata sanarwa da ƙungiyoyin fararen hula 56 suka sanya wa hannu, ta ce hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar, ya haifar da matsananciyar damuwa kan halarcin Akpabio a shugabancin majalisar dattijai.
Sun kuma ce "abin damuwa ne matuƙa cewa zaɓen da ya kawo shi Majalisar Ɗattijai a yanzu kotu ta tabbatar cewa na maguɗi ne.
"A duk wani tsari na dimokraɗiyya, irin wannan lamari yana neman bin bahasi cikin gaggawa da kuma sanin ya kamata daga shugabanni".
Cikin ƙungiyoyin dai har da CISLAC mai rajin kyautata faɗakarwa kan ayyukan majalisa da yaƙi da cin hanci da rashawa.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa, Mallam Auwal Musa Rafsanjani ya yi iƙirarin cewa Akpabio bai ci zaɓensa na 2019 zuwa Majalisar Dattijai ba, don haka kotu ta tabbatar da maguɗin da aka yi.
Ya ce Sanata Akpabio ba shi da cancantar da ta ba shi damar ci gaba da zama a kan muƙaminsa na shugaban majalisar dattijai.
Ƙungiyoyin sun jaddada cewa duk da yake Sanata Akpabio ya musanta hannu a maguɗin, amma samun jami'in zaɓen da ya ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara da laifi, ya dusashe sahihancin zaɓen nasa.
Sun dage cewa jazaman ne Sanata Akpabio ya sauka daga kan kujerarsa na wucin gadi har zuwa lokacin da za a warware wannan batu gaba-ɗaya, don tabbatar da ƙwarin gwiwar al'umma da tabbatar da ikon doka da kuma martabar hukumomin kare dimokraɗiyyar Najeriya.