Me ya sa Pakistan ke korar ƴan Afghanistan daga ƙasarta?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, અઝીઝુલ્લાહ ખાન
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, બીબીસી સંવાદદાતા
"Nan da nan fargaba ta ƙaru. Ba wai ina fargaba kan makomata ba, sai dai ina cikin damuwa kan karatuna saboda idan na koma Afghanistan, ba zan iya ci gaba da karatu ba."
Sadia (wadda aka canza wa suna), da ke zaman mafaka a Pakistan tun bayan dawowar Taliban kan mulki a Afghanistan, a yanzu tana cikin damuwa.
Tuni gwamnatin Pakistan ta sanar da cewa za ta mayar da ƴan Afghanistan waɗanda ke zama a Pakistan zuwa ƙasarsu ta asali.
Tun bayan haka ne, ƴan Afghanistan da dama, ciki har da Sadia, ke rayuwa cikin fargaba. Ta ce "Ba ma iya barci kuma muna cikin firgici.
"Bizar iyalaina za ta daina aiki. Ban san ko za a kara mana wa'adin biza ba kuma ina cikin tsoron me zai faru bayan 1 ga watan Nuwamba, " in ji Sadia
A yanzu, ƴan Afghanistan da ke rayuwa a Pakistan na cikin rashin tabbas kuma ba su san yaya gwamnati za ta yi da su ba bayan 1 ga watan Nuwamba.
Gwamnatin Pakistan ta bai wa ƴan ƙasashen waje da ke zama ba bisa ka'ida ba a ƙasar cewa su fice daga ranar 31 ga watan Oktoba. Ta kuma yi gargaɗin cewa za ta kaddamar da samame a faɗin ƙasar domin korar su daga ƙasar, daga ranar 1 ga watan Nuwamba.
Me ya sa Pakistan ta yanke shawarar mayar da ƴan Afghanistan gida?

A cewar ministan harkokin cikin gidan ƙasar ta Pakistan, Sarfraz Bugti, akwai kusan ƴan Afghanistan miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai a ƙasar da ke zama ba bisa ka'ida ba kuma ba su da takardu.
A cewar Hukumar Kula da ƴan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, yawan ƴan Afghanistan da aka yi wa rajista a hukumomi daban-daban a Pakistan sun kai miliyan uku da dubu ɗari ɗaya.
An ruwaito cewa akwai hannun ƴan Afghanistan a tayar da rikici, da safarar kuɗin dala da kuma sauran laifuka da ake aikatawa a ƙasar.
Duk da cewa gwamnatin Pakistan ba ta gabatar da wata hujja ba kan wannan zargi, amma an ɗauki matakin mayar da ƴan Afghanistan ɗin zuwa gida ne a zama na kwamitoci daban-daban da aka yi a matakin tsakiya da kuma na jiha.
Ɗaya daga cikin matakan shi ne, mayar da ƴan Afghanistan da ke zama ba bisa ka'ida ba a Pakistan zuwa ƙasarsu daga ranar 31 ga watan Oktoba.
Halayyar gwamnatin Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images
Mai magana da yawun gwamnatin Taliban a Afghanistan, Zabiullah Mujahid, ya bayyana a shafin X cewa ba za su amince da matakin Pakistan na korar ƴan gudun hijirar Afghanistan daga ƙasar ba.
Ya ce wannan halayyar ta Pakistan ba daidai ba ne, musamman ma zargin ƴan Afghanistan da aikata laifuka a ƙasar.
Ya ce a bi zaɓin ƴan Afghanistan kafin mayar da su gida.
Suhail Shaheen, jami'in ofishin gwamnatin Afghanistan a ƙasar Qatar, ya faɗa wa BBC cewa gwamnatin Afghanistan za ta marabci ƴan ƙasar da aka mayar gida.
Ya ce, "Jami'an da suka damu sun kafa kwamiti dangane da wannan mataki, don ganin an taimaka wa ƴan Afghanistan ɗin da aka iza ƙeyarsu zuwa gida da kuma kula da su."
“Ina cikin damuwa kan makomar karatuna da na iyalina”

Asalin hoton, Getty Images
A can birnin Peshwar, akwai wani titi da ya dangana zuwa wani gida inda iyalai ƴan Afghanistan da dama ke rayuwa a ciki.
Akwai wasu iyalai shida ƴan gida ɗaya da suka zo Pakistan kan biza ta shekara ɗaya.
Sadia (wadda aka canza wa suna), ita ce babbar ɗiya da ke karatu a wata kwaleji. Ta faɗa wa BBC cewa babban dalilin da ya sa take zama a Afghanistan shi ne domin ta samu damar yin karatu.
"Na yi aure a Afghanistan sai dai ba na cikin farin ciki a can, don haka sai na dawo gidan iyayena," in ji ta. "Bayan dawowar Taliban kan mulki a Afghanistan, an tilasta mana zama a gidajenmu.
Ba ma samun damar fita daga gidajenmu ko da don zuwa sayen kayan buƙatu na yau da kullum. Idan muna son guje wa kame, muna fita da mahaifinmu ko yayanmu." "An rufe makarantarmu. An kuma haramta ilimin ƴaƴa mata.
An gudanar da zanga-zangar adawa da matakin a Kabul, babban birnin ƙasar, amma hakan bai kawo wani sauyi ba. An ki barin ƴaƴa mata su samu ilimi," in ji Sadia.
Ta ce "Yanayin da muke ciki na ƙara munana a kowace rana. Ba mu san me za mu yi ba,".
"Mun yi iya ƙoƙari wajen ganin al'amura sun daidaita a Afghanistan da kuma ganin cewa ba mu bar ƙasar ba, amma hakan ya ci tura," a cewar Sadia.
Iyalanta sun fara isa birnin Islamabad. "Babu wanda ya san mu a nan. Mun shiga matsala da farko, amma sannu a hankali al'amura suka fara daidaita."
"Daga nan na shiga makaranta. Lokacin da ɗan’uwana kuma ya fara shirin yin sana'a, kwatsam sai gwamnatin Pakistan ta sanar da cewa za ta kori ƴan ƙasashen waje da ke zama ba bisa ka'ida ba a ƙasar daga ranar 1 ga watan Nuwamba."
Ta ce "A yanzu mun kasance cikin ruɗanin me zai faru nan gaba. Wani abu kuma shi ne zan rasa karatuna."
"Yanzu mutane a gida na cikin damuwa a kan abin da za su yi. Ba za mu iya zuwa wata ƙasa ba. Akwai haɗarin komawa Afghanistan kuma gwamnatin Pakistan ba za ta bar mu, mu ci gaba da zama a ƙasar ba," in ji ta.
"Daga gida sai wurin aiki"

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan ƙasashen waje da ke zama ba bisa ka'ida ba a Pakistan na cikin zaman rashin tabbas a yanzu kan abin da za su yi nan gaba.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne kan dukkan yan ƙasashen waje, sai dai ta fito ƙarara cewa wannan mataki ya ta'allaka ne kan ƴan Afghanistan da ke zama ba bisa ka'ida ba a Pakistan.
Sai dai, tun kafin Taliban ta karɓi mulki a Afghanistan, akwai ƴan gudun hijirar ƙasar da dama a Pakistan waɗanda ba su da takardun da suka kamata na yin tafiya ko zama a Pakistan.
A yanzu, ƴan Afghanistan da ba su da takardu na cikin mawuyacin hali a Pakistan.
Sajjad Ali (wadda aka canza wa suna) na cikin irin wannan yanayi.
A 2017, lokacin da Hukumar Kula da Ƴan Gudun Hijira ta MDD ta kaddamar da shirin tallafa wa ƴan gudun hijirar da suka koma gida bisa raɗin kansu, hakan ya sa sun ci gaba da komawa.
Sajjad ya ce ya koma Afghanistan ne bisa tunanin cewa yanzu za a samu zaman lafiya a ƙasar kuma gwamnatin Ashraf Ghani na samar da ababen more rayuwa ga ƴan Afghanistan da suke komawa gida.
Ya ce an lalata takardunsa na zama a Pakistan. Abun da ke nufin cewa rajistarsa ta zama a ƙasar ta daina aiki. "Tun da farko, ban tafi da ƴaƴana ba.
Suna Pakistan. Da isa ta Afghanistan, na lura cewa babu wani aikin yi kuma sharuɗan da aka saka sun yi tsauri," in ji shi. "Na gano cewa hakan babban kuskure ne. Yanzu ya zan yi na koma Pakistan?
Wannan ita ce matsala." Sajjad ya ce ya koma Pakistan cikin wahala, inda ya sake yin rajista karo na biyu da MDD a can.
Bayan haka sun ba shi wata lamba bayan ɗaukar bayanansa. "Yanzu ina da lambar amma babu kati, don haka ƴaƴana na da katin zama a nan." A yanzu Sajjad na cikin fargabar abin da zai faru da shi. Suna tafiya ne daga gida zuwa aiki sai kuma gida kaɗai a yanzu.
Me zai faru da mawakan Afghanistan?

Asalin hoton, Getty Images
A lokacin da ƙungiyar Taliban ta kafa gwamnatinta a Afghanistan shekaru biyu da suka gabata, ɗimbin mutanen da suka bar Afghanistan sun yi adawa da aƙida ko kuma waɗanda suka yi aiki da gwamnatin da ta gabata da kuma baki, da kuma waɗanda ke da alaka da waka.
Yawancinsu sun isa Pakistan. A cewar waɗannan mawaka, akwai mawakan Afghanistan 800 da ke zaune a ciki da kewayen birnin Peshawar kaɗai, waɗanda yawancinsu ba su da takardun zama a Pakistan.
Sohail (an canza sunan) mawaƙin Afganistan ne wanda ke rera waƙa a cikin harsunan Farisa da Pashto. Ɗan uwansa ma shahararren mawaki ne.
Ya isa Pakistan ne bayan da gwamnatin Taliban ta hau karagar mulki a Afghanistan shekaru biyu da suka wuce. Tafiyar sa daga Kabul zuwa Islamabad ba ta wuce ta kasada ba.
A wannan lokacin ne 'yan Taliban suka shiga fadar gwamnati da ke birnin Kabul kuma an shiga fargaba a kowane ɓangare.
Mutane suna ta gudu. Mutanen yankin kuma sun yi ta tarbar jiragen ruwan 'yan ƙasashen waje da ke isowa.
Sohail ya isa Islamabad da kyar tare da yan’uwa. A halin yanzu, suna da izinin zama daga wata hukuma ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke aikin tallafa wa 'yan gudun hijira, amma har yanzu ba a ba su dukkan takardu ko katunan ba tukuna.
Ya shaida wa BBC cewa akwai yanayi na rashin yarda. Ya ce, "Mu a matsayinmu na mawaka muna jin cewa ba mu da wuri a Afghanistan a halin da ake ciki, saboda mu mutane ne da ke da alaƙa da kiɗa kuma idan Taliban ba ta yarda da kiɗa a Afghanistan ba, me zai sa mu je can? Me za mu yi a can");