Abin da ya faru a kotu game da shari'ar Hamdiyya Sidi a jihar Sokoto

Hamdiyya Sidi Sharif

Asalin hoton, Facebook/Hamdiyya Sidi

Wata kotun Shari'ar Musulunci a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta ɗage sauraron ƙarar da hukumomi suka gurfanar da matashiyar nan Hamdiyya Sidi Sharif sakamakon bidiyon da fitar a farkon watan Nuwamba.

Ƙungiyoyi da masu fafutikar kare haƙƙi a Najeriya sun yi tir da matakin da gwamnatin jihar Sokoto ta ɗauka na kama matashiyar, kodayake fadar gwamnatin ta musanta cewa ita ta kama ta.

Majiyoyi sun shaida wa ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International cewa daga cikin tuhume-tuhumen da aka yi mata sun akwai yunƙurin tayar da hankali, da tunzira mata su auka wa gine-ginen gwamnati.

Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa tun a zaman farko aka bayar da belinta, kuma kwana biyu bayan haka ne wasu mutane suka yi garkuwa da ita tare da ji mata raunika.

Kotun ta Shari'ar Musulunci ta ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 4 ga watan Disamba.

Wani ɗan gwagwarmaya kuma shugaban ƙungiyar Rundunar Adalci reshen jihar Sokoto da ke bibiyar shari'ar, Bashar Altine Guyawa, ya shaida wa BBC cewa wani maigari ne gurfanar da ita a kotu bisa wasu kalamai da ta yi.

A cewarsa: "Na ɗaya, ta nemi 'yangudun hijira su ɓalla gidajen gwamnati su shiga saboda ba su da wurin kwana. Na biyu, ta ce tana da ƙungiyar da za ta bayar da tallafi amma kuma ƙarya ne ba ta da wata ƙungiya. Tuhuma ta uku kuma, ta shafi kalaman da ta yi na kwatanta 'ya'ya da matar gwamna."

Amnesty International ta siffanta tuhume-tuhumen a matsayin "na gangan", sannan ta nemi gwamnatin jihar ta Sokoto ta janye tuhumar da take yi wa Hamdiyya.

"Tun bayan da bidiyonta ya karaɗe shafukan sada zumunta take shan kira a waya da ke yi mata barazana," in ji Amnesty cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X.

"Dole ne gwamnatin jihar Sokoto da rundunar 'yansandan Najeriya su jingine tuhume-tuhumen da suke yi wa Hamdiyya kuma su ƙyale ta ta dinga bayyana ra'ayinta."

Dr Mairo Mandara na ɗaya daga cikin masu gwagwarmayar kare 'yancin mata a Najeriya, kuma ta faɗa wa BBC cewa suna bibiyar halin da matashiyar ke ciki.

Kazalika, shahararren lauya ɗan Najeriya mazaunin Birtaniya, Audu Bulama Bukarti, ya yi tir da kama Hamdiyya, har ma ya yi tayin taimaka mata wajen kare kanta a kotun.

"Bayan bidiyon nata ya karaɗe shafukan zumunta, a ranar 13 ga watan Nuwamba wasu mutane suka ɗauke ta da ƙarfin tsiya suka saka ta a babur mai ƙafa uku bayan ta tafi karɓo wayarta daga wurin caji. Suka yi mata duka kuma suka jefo ta daga ciki bayan sun ji mata ciwo," a cewar Amnesty.

Hamdiyya sabuwar tauraruwa ce a masana'antar Kannywood ta finafinan Hausa, wadda ta fara fitowa a fim da kuma bidiyon waƙoƙi.

Matashiyar ta sha bayyana cewa "ni ba 'yarsiyasa ba ce kuma babu wanda ya turo ni don na yi masa kamfe".

Me Hamdiyya ta ce a bidiyon kuma me ya sa ta yi shi?

Hamdiyya 'yar asalin ƙaramar hukumar Wurno ce da ke gabashin jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya.

A farkon watan Nuwamba ne ta fitar da wani bidiyo a shafukanta na sada zumunta, inda take kokawa game da yadda 'yanbindiga ke shiga ƙauyensu suna sacewa tare da kashe mutane.

"Yallaɓai gwamnanmu na Sokoto Ahmad Aliyu, mu an manta da mu ne ko kuwa labari bai ishewa kunnenka ne");